chapter 45

1.1K 87 1
                                    

💗💗💗💗💗💗
Sark'ak'iyar soyayyah!
     ❤❤❤❤❤❤

_F.O.W_

_NA_

_Foulani cerdiya_
&
_khairat up_

          "45"

"kwanan maisha uku a asibiti daidai da sadakar uku na mutuwai rukky."

"ta yi kuka sossai da sossai ko da ta koma gida ma ta ga little ae sai ta kuma sa wani kukan me ban tausayi me yasa mutuwa? me ya sa? yah rukky me sa ban ganki ba? ki ka tafi ki ka barni da little why? mami ta dinga lallashin ta."

"tun da ta dawo little yake a hannun ta komai ita take masa a kankame yake kasancewa a jikinta"

"yan gidan su yah mas ma sun zo gaisuwa lokacin kuma saura sati daya bikin mas da saudatu."

"an yi bakwai an watse , maisha da kyar ta yarda ta koma gidan ta little kuma na hannun mami tana kula da shi a wajen ta."

"yah muhd tamkar wanda aka ce mahaifiyar sa ce ta mutu,ya dawo wani mara magana,miskilanci ya karu a kan na da, da zama shi kadai wani lokacin idan abun ya ciyo shi kawai ze dau hoton ta yayi ta kalla yana kuka. da magariba yaje ya ga little ya koma gida."

"an kai amaryar mas kyakyawa da ita washe gari ko maisha ta ga kabilanci da ruwan dangin yah mas a gidan wai an zo ganin amarya inda ta dinga mamaki dan ita ba wanda yake zuwa gunta ko ta je bata ganin walwalar su a tare da ita."

"yah mas ya ki kula amarya, saida maisha ta masa fada da nasiha tukuna ya dinga kula ta ya raba musu kwana biyu biyu."

"da safe bata fasa ba ta musu girki ta jera musu suka yi break tare duk da dai amaryar yar iyayi ce da gani gani sai da ta koka ganin kyawu da kyawun diri irin na maisha to me zata nuna mata? babu."

   _BAYAN KWANA ARBA'IN_

_GIDAN ABBA!_

"Baffa usthman ne da umma da sauran dangin abdul_ali aka tada meeting hatta yah mas yana gun yayin da maisha ta na rike da little a hannun ta kamar za a kwace mata shi."

"addu'a aka yi ma abba da rukky sannan aka yi doguwar nasiha a kan hakuri,musamman ma ga mijin da ya rasa matar sa"

"baffa usthman ya kalli mami da ke jikin kujera duk ta rame ya ce mamin yara wa ki ke ganin za a bawa rikon little?."

"mami ta ce zan rike ta alhaji ,Allah ya raya mana ita."

"farat maishan tayi ta ce baffa zan rike ta dan Allah."

"mami ta ce tayaya za a baki rikon jaririn dan wata daya da sati?"

"mami zan iya dan Allah ku bar mun shi dan soyayyar da ke tsakanina da yah rukky a bani."

"baffa ya ce to ki nemi izinin mijin ki in ya yarda."

"ta kalli yah mas,yaya zan amshi  little na rike a wurina."

"yaso su hada idanuwa ta hana,amma ya zai yi ta ki kallan sa balle ya hana,ba komai baffa tunda tana so a bamu mu rike,Allah ya raya ta."

"amin kowa ya amsa."

"yah muhd kawai da ido ya bisu ganin karfin da aka nuna masa a kan dan sa,shi kam ba a san ransa ze bada ba dan ba yadda ze yi ne yasa yay shiru,ae sai mutanen gurin suga rashin kunyar sa."

"to amma idan ze ga little sai yaje gidan yah mas? se ya dinga tuna wani abu?... yaya kenan?"

"an rufe taro da addu'a bayan an kasa abunda mariagayiya ta bari."

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now