Page 45

589 31 0
                                    

*PAGE 45*

*This page is for you HAUWA SALEH ADAMU, you are indeed a sister from another mother, girl I love you to the moon and back... Stay blessed always sweery* 💜💜💜

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

Gudu kawai takeyi bata san inda zataje bah, duk wani corner data gani sai ta bi duk da batasan inda zai kaita bah.

Kusan mintuna 10 tayi tana gudu bata ko tsaya bah, ga yunwa yana matukar damunta a yayinda bakinta ya bushe saboda kishirwa. Ta gaji tilis ta zube karkashin wani bishiya tana maida numfashi, gabad'aya karfinta ya kare bata tunanin zata iya gudun kuma, addu'arta kawai Allah ya turo wanda zai taimaketa tunda ta lura ta shigo wata unguwa.. Tana nan zauneh karkashin bishiyar aka turo kofar wani gate, wani saurayi da bazai girme mata sosai bah ya fito da motah ya ajiye nan kusa da itah sanan ya koma ciki yana kokarin kulle gate d'in duk a idon Sahr .

Bayan 2 minutes wannan saurayin ya fito, ya karaso wurin motan yana kokarin sa key yayi unlocking motan ya lura da Sahr dake zauneh ta k'ura mishi idanu, da har ya bud'e motan zai shiga yayi tafiyarsa sai kuma ya fasa, ya mayar da kofar motan ya rufe sannan ya nufota.

Har ya karaso inda take bata sani bah, a nutse cikin kamala da sanyin murya yace

"Salamou Alaikoum, baiwar Allah me kikeyi anan neh tun d'azun kike zauneh ke kad'ai, lafiya kuwa?"

Shiru Sahr tayi bata ce komai bah, bata ma san yana yi bah, a karo na biyu ya sake cewa

"Baiwar Allah lafiya ina magana kinyi shiru?" Ya fad'a neh tare da bubbuga hannayenshi

'Firgigit' ta dawo daga duniyar tunanin ta takeyi, a razaneh ta kalleshi shi d'in ma ita yake kallo. Kafin tayi magana hawaye ya fara wanke mata fuska, a cikin muryan kuka tace

"Don Allah bawan Allah ka taimakeni, am thirsty I need water, ruwa please"

Gabad'aya Sahr ta bashi tausayi yadda yaga bakinta duk a bushe, kuma duk da bai santa bah she don't seem alright, she must have went through something terrible.

Cikin tausayawa wannan saurayin yace
"Sunana Sameer kuma wannan gidan mu neh, if you can trust me zaki iya bina ciki wurin umma, daga nan sai kisha ruwa kici abinci don na lura harda yunwa kikeji ba kishirwa kawai bah, ki yarda dani bazan cutar dake bah". Ya fad'a don ya lura tana d'ari d'ari dashi.

Da kyar Sahr ta iya d'ago idonta tana kare mishi kallo har yanzu tana hak'i, haka kawai ta gamsu Sameer bazai cutar da ita bah, a hankali tace

"Nah... Nah gode"

Sannan ta rik'e bishiyar domin ta mik'e, duk tanajin jikinta babu k'wari kuma jiri yana d'ibanta, bata gama mik'ewa bah ta tafi luuuu, ta fad'i kasa sumammiya.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'uun" kawai Sameer yake furtawa, hankalinshi yakai k'ololuwa wurin tashi, kardai ace wani mugun abu ya samu yarinyar nan. A rikice ya d'agata yayi wajen mota da ita, jikinshi har rawa yakeyi yayi unlocking motan sannan ya b'ude back seat ya sakata a ciki ya rufe, da 'yar gudunshi ya dawo gaba ya shiga yayi starting motan without any idea'n asibitin da zai kaita, da sauri yayi reversing motan sannan yabar wurin in a very high speed.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*KHULAYD, 03:45PM*

Da sauri Mami ta mik'e jiki na b'ari ta karasa wurin gadon cikin tsananin farin ciki, tsayawa kawai tayi tana kallonshi tama rasa me zata ce mishi sai tayi bursting into tears, out of happiness tace

"Son am I dreaming ko abunda na gani da gaske neh, don Allah Son kar kace mafarki nakeyi, don Allah", tana fad'an maganan tana kuka at same time tana murmushi.

With tears rolling down his cheek Khulayd ya mika hannunshi ya riko hannun Mami, don ya tabbatar mata da cewa ba mafarkin takeyi bah, yace

"Aunt you are not dreaming, da gaskene am moving, am feeling inside of me that I can seat up Aunt, Allah ne ya amshi addu'ata ya dawomin da kuzari nah don inje chan waje in nemo soyayyar rayuwata, kuma zuwa yanzu na gama yarda cewa *Sahr-Khulayd* are destined for each other, zuwa yanzun na tabbatar da cewa Allah neh ya had'a soyayyar mu kuma babu mai rabamu"
Kamar wasa mami taga Khulayd ya tashi ya zaunah yana kallonta, yana murmushi shima.

Da gudu Mami ta fita tana fad'in

"Lemme inform the doctor" bata tsaya taji me zai fad'a bah

On seeing that, Khulayd ya sauke kafafunshi ya mik'e kamar zai fad'i, ya fisge abun drip da aka d'aura mishi sannan yasa slippers dake ajiye kasan gadon, baiyi wani tunani bah ya fice don zuciyarshi ta gama yarda da maganganun Nailah da shawaranta.
Tafiya yakeyi da sauri sauri a cikin asibitin bai masan inda take shiga bah, burinshi kawai ya isa bakin gate ya hau ko adaidaita sahu neh yaje gida ya d'auko mota...
Ya d'auki tsawon mintuna kafin ya isa gate din yana kokarin fita.

⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜⚜

*SAHR-KHULAYD*

Sameer yayi droving cikin asibitin da wani uban gudu, he's not even seeing clearly, fatanshi Sahr ta samu immediate medical attention, saura kad'an ya k'ade Khulayd dake kokarin fita zuwa waje

"Baka gani neh malam, can't you drive carefully? Wannan asibiti neh not your father's house" Khulayd ya fad'a cikin fushi.

A fusace Sameer yayi packing motan a nan bakin gate d'in ba tare da ya damu da next car dake bayanshi yana ta faman horn bah, kuma ba tare da ya rufe marfin motan bah ya karasa gaban Khulayd wanda ya tsaya yana kallonshi a kufule, cikin b'acin rai Sameer yace

"Hey Mr whatever, ka iya bakinka, karka kuskura ka zagar min iyaye or else...."

Khulayd bai bar Sameer ya karasa zancenshi bah yace

"Or else what huh? Me zakayi min,who do you even think you are to talk to me this way, zan iya inyi maganinka kafin kyaftawan ido"

Sameer zayyi magana Khulayd ya tari numfashin shi

"Am not done talking to you yet, bari in gaya maka abunda baka sani bah, no one messes with me coz am *KHULAYD ABEED OMAIR* " ya fad'a da karfi

Karaf a kunnen Sahr dake kwance a mota lifeless, sunan Khulayd ya daki dodon kunnenta duk da a sume take, hakan ya tilasta mata farfad'owa.
Da sauri ta bud'e idonta tanaji kamar karya kunnenta ya jiyo mata, ta tattara dukkan karfin ta tashi ta banke kofar motan har tana tuntub'e

Kamar a mafarki taga Khulayd a tsaye yana ta faman fad'a da Sameer, da karfi tace

*Ya Khulayd*

Ko a mafarki Khulayd bazai taba manta voice d'innan bah

*Baby doll* ya fad'a shima da karfi yana waige waige.



#TEAMSAHRKHULAYD💯




Drop your comments via my inbox @ 08060522342, my Facebook page @ Seemby luff novels or follow me on instagram @ Seemby_luff

© *SEEMBY LUFF*😘

Sahr-Khulayd Where stories live. Discover now