🌹The death🌹

211 19 0
                                    


🌸na Anty pink🌸

Koda suka isa gidan ita da idi mai shago suka tarar da Abba a tsakar gida ya rafka tagumi fuskarsa hawaye shar shar kamar karamin yaro. Rayyana ta karaso gun shi da sauri ta dafa shi domin shi ko lura ma baiyi da shigowarsu ba tace "abbana menene na ga ka zauna kayi tagumi. Abba ya shiga matso kwalla batareda ya damu da ya goge su ba yace" Rayyana ban San inda zan sa kainaba ummarki ta tafi ta barni. Rass gaban ta ya fadi hawaye suka fara tsere a idonta ta ce"Abba me kake nufi ban ganeba kafadamun inda ka dosa. Abba Dan Allah idan ma zolaya ta kakeyi Dan Allah ka dena Abba bana so. Abba bai ce komaiba saima nuni dayai mata da hannu alamar ta shiga dakin da ummarta take tagani domin bazai iya kuma furta wani Abu gameda mutuwarta matar saba da kuma uwar yarsa kwaya daya tilo. Rayyana ta daga kai taga yamata nuni da daki ai a guje taruga ta fada dakin idi mai shago ma yabi bayanta. Wani mummunan faduwa gabanta yayi takarasa inda ummarta a hankali kamar bata son taka kasa. Ta bude fuskarta ta na kallon kyakkyawar fuskarnan da bazata taba mantawa dashi ba tace"Allah ya jikan ki Umma ya rahama miki ya sa kin huta. Umma bazan miki kuka ba na miki alkawari bazan yi kuka ba zan dinga miki addu'a domin kisamu rahamar ubangiji. Umma kisani ina sonki kuma har karshen rayuwata bazan taba samun kamar kiba Allah ya jikan ki. Ta kawar da kanta gefe hawaye na mata zarya a idanu tasa hannu tai saurin goge hawayen. Idi mai shago yace" kiyi hakuri ki dau dangana ki danne zuciyarki kici gaba da yi mata addua kawai ni natafi. Har yakai bakin kofa ya juyo yace zan fadawa mutanen anguwa Ku kuma kuyi kokari kuyi mata wanka Allah ya jikan ta. yasa kai ya fice.

Bayan rasuwar ummar rayyana yarage daga abbanta sai ita. Abincin ma da zasu ci gagararsu yakeyi domin tuni masu taimaka musu suku dena kawowa sai in Abba ya fita yayi buge bugen shi idan ya samu ya kawo itama rayyana haka. Yau asabar rayyana na zaune a tsakar tayi nisa cikin tunani Abba ya shigo. Har so uku ya kira sunanta amma bata Masan da yashigo ba sai da yabuga kafarasa a kasa ya kira sunanta da karfi. A raxane ta amsa mai tace "na'am Abba yaushe ka shigo bari in dauko ma kujera Abba ya ce barshi kawai nan ma yayi ai. Tace toh takoma ta zauna. Abba yace rayyana wlhy naga ji duniyar nan duk tajuya mana baya gashi bamuda yan uwa anan kusa rayyana bansan ya zan sauke hakkina akanki a matsayina na mahaifinki ba.Rayyana ta ce Abba kar ka damu Allah na sane damu watarana sai labari. Abba inason kabarni inje birni ko aikatau ne inyi inyaso kudin da za'a dinga biyana a wata sai in aikomaka. Abba yace a'a rayyana bazai yu ace mace mai ilimi kamarki ba tace zatayi aikatau. Rayyana tace Abba bamuda wata zabi daya wuce wannan. Abba yace toh shikenan zan ma saude magana ba ita kekai masu aikatau birni ba? Rayyana ta girgixa ma Abba kai yace toh shikenan Bari in je in sameta yanxu.

Koda Abba ya sami saude da maganar sai caa mishi tayi ai kuwa akwai wasu mutane acan habuja dama tayi dasu akan zata sama musu yar aiki amma tunda ta samu ai sai batun tafia. Abba yace amma matsalar kwaya daya ce sauda tace matsalar mey kuma. Abba yace mata agsky bayada kudin motar da zai bai wa rayyana taje birni. Saude ta bushe da dariya tace ai wannan bana su bane su masu bukatar yar aikin su zasu bada kudin motar. Saude tace amma tayi karatu ko dan su mai ilimi suke so. Abba yace ai idan ta bangarennan ne basuda matsala amma a matakin sakandire ta tsaya saude tace ai wannan ma yayi indai tana jin turanci. Abba yai mata godia yatafi gida da xummar cewa gobe zasu tafi da rayyana birni.

🌹💐Ni da Rayyan🌹💐Место, где живут истории. Откройте их для себя