🌹The experience🌹

129 20 0
                                    

🌸 Na Anty pink🌸

Koda Abba ya fadawa rayyana akan yanda sukayi da saude batace mishi komai ba da toh kawai ta amsa mishi ta shiga ciki domin ta fara harhada kayanta amma a jikinta jita keyi kamar zata rabu da wani bare na jikinta.

Kashegari tunda sassafe saude tashiga doko musu sallama tana cewa wai ina rayyanan takene bazaki ba wai. Rayyana tafito da d'an akwatinta na karfe sanye da hijabi tsaf tsaf ba Wanda zai ganta yace daga kauye ta ke domin rayyana farace tas ga hancinta rad'au kamar an dasa shi kasan hancinta kuma dan karamin pink lips ne. Rayyana dai sai Wanda yagani ahakan ma ummarta tafita kyau domin ummarta yar Sudan ce kuma shuwa arab amma talakawannan neman abunda zasu sa abakin su ya kawo ta najeriya da ita da abokan tafiyarta dama can iyayenta sun rasu yan uwanta kuma suka ki daukar ta cewa wai zata zamar musu burden suma ya suka karasa balle a kawo musu wata . Abban rayyana mutum ne mai karfin hali domin duk yanda talauci takai shi bango bai yarda ya bar rayyana ba ilimi ba domin a boarding skull ya sata nan gaba da kauyensu kadan yanxu haka bata dade da gamawa ba. Duk wani aikin karfi mahaifin rayyana nayi domin yaga ya hada kudin makarantar rayyana itama ummarta na contributing wajen biya mata skull fees dan abunda tasamu ta tara acikin sana'ar da takeyi agida duk zata tattara ta bayar ayi amfani dasu abiya mata kudin mkrnta da kuma d'an siyayyar da za'a mata kafin tatafi haka sukai tayi har suka samu ta kammala.

Da kyar saude ta b'anb'are rayyana daga jikin Abba. Kuma Sosai tayi kuka da kyar da danne zuciya suka samu suka kai tasha inda suka shiga motar abuja. Tafiyar kusan awa bakwai sukayi kafin suka isa garin abuja. A wani tsararren gida naga an wangale musu gate su rayyana kam sai kallo akeyi ina ruwan d'an kauye ya shigo birni itako saude ko a jikinta dayake wurin zuwanta ne kai tsaye ciki suka wuce. "Ya salam" shine abunda rayyana ta furta a zuciyarta a lokacinda suka doso wani hadadd'an rikitaccen Palo yasha kayan kyale kyale har ya gaji kujeru har set uku aka jera a palon ga sanyin ac dake ta busowa ga kamshin room freshener ya kara k'awata palon. Wata matashiyar mata nagani zaune akan wata makekiyar kujera ga ma'aikata da keta kaiwa da komowa. Cikin azama suka isa inda matar nan take suka zube kasa suka shiga kwasar gaisuwa matar da fara'arta ta amsa musu tace sannunku matafiya ya hanya. Saude jikinta na b'ari ta shiga amsa mata. Haj mun suka lafiya kuma injin munsa meku lafiya. Lafiya kalau wannan itace mai aikin da kikace kin samo. Eh haj itace ko bata miki ba. Ai bazancan bata mun ba indai taiya aiki ai an wuce wurin. Saude kamar an bude fanfo tasoma zuba tana cewa ai haj wannan ta iya aiki kamar injim inta fara ba tsayawa sai kin ce ta dena kuma ga jin turanci kamar baturiya. Hajyr tayi murmushi tace wat is ur name. "RAYYANA" kai tsaye tabata amsa. Matar ta zaro ido tace wow I'm really impressed itakuwa saude sai washe hakora takeyi tana cewa kin gani nagayamiki ko. Haj ta dora da cewa how old are u. "18" nan ma kai tsaye ta bata amsa tace toh yanxu bari insa a nuna miki dakinki anjima zanzo inji dame dame kika iya kinji gyada mata kai kawai tayi. Precilia, precilia haj ce keta faman kiran wata yar aiki can sai gata taxo ta durkusa gabanta tace yes ma'am haj tace take her to her room tace OK ma. Rayyana ta dauki dan akwatinta na karfe tabi bayanta jiki ba kwari

Wacece haj
Menene asalin sunanta
Kubiyoni domin kuji Karin bayani
#vote
#share
#comment
Yawan votes dinku yawan updates
💋Anty pinky

🌹💐Ni da Rayyan🌹💐Where stories live. Discover now