🌹Babi na hudu🌹

120 29 0
                                    


🌸Na Anty pink🌸

Wacece haj?
Menene asalin sunanta?

Haj kamar yanda kowa ya sani asalin sunanta marwanatu. Mahaifinta hamshakin mai kudi ne a abuja mijinta alhj Ahmad suleiman Tafida multi billionaire ne kuma dan kasuwa. Yayanta guda biyu mace daya namiji daya.Ayman itace babba  kafin rayyan. Ayman zata kai kamanin shekara 33 Rayyan kuma zai shekara 29. Ayman tayi aure tun shekara biyar da suka wuce tanada yara guda biyu da mai sunan daddy wato Ahmad da kuma Aswad. Shi kuma Rayyan yana London acan yake aiki shi likitan kwakwalwane. Haj marwantu tana nuna ma yayan ta guda biyu tsananin so da kauna dama can rayyan akwai shagwaba da son jiki shiyasa kullum yagirma amma kamar bai girma ba ga miskilancin da ke cinshi idan dai har ya maka magana sau daya biyu toh baya sakeyin magana indai bada ummarshi ba ko Abba ko Ayman ita kanta datake yayarshi bai cika sake mata fuska ba har shakkun shi takeyi. Wannan kenan.

Bayan sallahn isha ummar rayyan tasa aka kira mata rayyana. Tasoma tambayarta tana cewa dame dame tasani a kicin. Tace ita dai tasan tukunya tasan frying pan sannan kuma ta iya abinci. Ummar rayyan tace batasan mixer ba batasan egg beater batasan ice cream scoop ba batasan blender ba batasan heater ba batasan gas cooker ba da dai sauransu. Duka tace tasani domin a makarnatar su ana koya musu amma bata iya amfani dasu ba. Ummar rayyan tace toh ai wannan duk mai sauki ne tunda tanada iliminta ai koyo bazai mata wuya ba. Tace mata ta tashi taje ta kwanta in Allah ya kaisu gobe duk za'a koya mata tace toh ta koma dakinta. Wani daki ne mai dauke da katifa yana da dan fadi ba laifi sai Dan madaidaicin closet da standing fan da kuma na sama sai toilet da ke gefen gado.

  Washegari Umma da kanta ta shiga kicin tareda rayyana ta shiga gwaggwada mata abubuwa cikin k'ank'anin lokaci kuwa duk ta d'auke duk abunda Umma ta koya mata dama rayyana akwai k'ok'ari ga hankali ga tunani ga ladabi da biyayya. Ummar rayyan ta matuk'ar ji dad'in xama da rayyana domin bata da kiwya ko kad'an ga son aiki sai halin su ya xo d'aya domin ummar rayyan itama akwai tsafta harna fitar hankali haka ma yaranta sun biyo halinta har sun kere ta wajen tsafta.

  Kwanci tashi rayyana har tayi wata d'aya a gidan aikinta kudin albashinta kuwa tuni ta aika ma Abba dubu ashirin cur. Tun jiya ummar rayyan ta tara duka ma'aikatan.gidan ta shaida musu da cewa d'an autanta d'an lele zai  iso gobe cewa a yau dan haka tarbota keso ayi masa na musamman dan haka kowa ya dukufa wajen aiki. Ta rarrabawa kowa aikinsa ita kuma rayyana aka bata gyaran d'akin da kuma dafa abincinsa har sai randa zai koma bakin aikinsa domin ya d'auki leave dan yazo yaga ummansa da abbansa. Tunda sassafe ta tashi ta karbi mukullin dakinsa ta nufi sashenshi dan gyarawa. Wani hadadden flat mai dauke da daki biyu da kuma falo mai tsananin girman gske har da kicin aciki. Side din kamar ba'a taba zama a cikinsa ba dan komai tsaf tsaf yake sai dai ya d'an yi kura. Share share ta hau yi cikin sauri domin ance jirginshi karfe sha biyu ne yanxu kuma karfe shida da rabi ne dan haka ta zage damtse sosai wajen gyaran koda karfe goma tayi har ta kammala komai hatta girki duk ta kammala amma sai da taje ta tambayi Umma me za'a dafa tace mata ai shi yafison abinci simple dan haka ta dafa mishi fried rice da pepper chicken sai lemon juice ta kuma hada mishi coffee tasa mishi a flask domin shi ma'abocin shan coffee ne idan bai ganshi ba ransa na matukar b'aci Dan haka ta kiyaye duk da safe da rana ta tabbata ta hada mishi. Toh wannan shi kuma wane irin d'an ra'ayi ne mutum d'aya sai kace dubu rayyana ta fad'a a ranta a fili kuwa cewa tayi toh Umma in Allah ya yarda zan kiyaye. Umma tace amm rayyana kinsan abunda yasa na xabe ki a amtsayin mai hidima da d'ana?ummar rayyan ta jefo mata wannan tambayar. Rayyana tai kasa da kanta tace a'a. Umma tace abunda yasa na zabeki saboda naga duk cikin masu aikin gidannan kinfisu kama jiki wajen aiki Dan baya son sanyin jiki. Ina fata kin gane Dan haka kiyi kokari kiyi duk abunda zai ummarce ki kinji. Rayyana tace insha'allahu Umma zanyi yanda kikace Umma tace jeki kicigaba da aikinki ta amsa da toh ta fice tana mai jin haushi wannan mutumin mai shegen kilinbibin tsiya.

Karku manta wattpadians yawan votes dinku yawan updates.

#Vote
#share
#comment

*har yanxu taku ceh
💋Anty pink
Ayi karatu lfy

🌹💐Ni da Rayyan🌹💐Where stories live. Discover now