chapter 5

2.7K 245 28
                                    

Here's a gift from your momma ozegya I heart you♥

I might never be the one in shining armor, I might never be the one you take home to mother... But I can always be the for you!

                 ~One direction~

^*^*^*

   Murmushi dauke a fuskarta har bus ya dropping dinta a kofar gida,takai minti biyar tana tsaye tana kallon gidansu...Gidan da batada farinciki a ciki, babu wanda zata kalla aciki taji dadi...tasan daga zaran tasa kafa ciki duk wani farin cikin datake ciki a yanzu zai gushe...ta tuna sanda faaris yace mata keep smiling...runtsa idanu tayi tayi breath in and out kafun ta knocking gate din tana kokarin maintaining fara'arta.

    A babban falo ta tarda mummy tareda friend dinta hajia kareema, wanda kowanni kulle kullensu tare sukeyi...gaishesu tayi babu wanda yadago ya kalli inda take...harta nufi stairs zata haura mummy tace "ke dawo nan."

A hankali sahresh tadawo ta tsugunna tareda cewa "gani mummy?"wani banzan kallo tamata hajia kareema taja tsaki.

Mummy tace "baki iya gaisuwa bane?"sahr batace komai ba saida takuma daka mata tsawa.

"Na gaisheku..."tabata amsa batare da ta nuna tsoro ko bacin raiba...mummy tace "ohh namiki karya kenan?"

Sahresh batace komaiba mummy tafara masifar data saba... "Wuyanki yafara kauri ko? Har takai ga kin wuce mu baki gaishemu ba, idan ni kin rainani ae ga bakuwa ko ita dinma saikin nuna mata halinki na munafurci?"

"Kiyi hakuri."shine kawai abunda ta iya cewa kana ta dubi hajia kareema tace "ina wuni."bata amsa mata ba sai daga kai datayi kawai tana wani yatsina... Takuma gaida mummyn itama bata amsaba....

"Tashi kiban guri kuma kinada hukunci dan ubanki."sahr batace komai ba tayi wucewarta sama...

Sallahn la'asar tayi tajima tana addu'a kafun tashafa... Agogon da faaris yabata ta daga tana murmushi, ta tabbata duk bata mata ran da akayi daga zaran ta kalla zai sata farin ciki... Lokaci daya faaris ya maye gurbin akhi dinta.

Tana cikin nade hijabinta taji an bangajo kofar dakin, fadeelah tagani a tsaye tana harararta tace "Kizo inji mummy..."ta amsa da toh har zata juya ta hangi agogon hannun sahr tace "ke ina kika samu wannan agogon?"ta tambaya tareda fisgewa.

Kallonta sahr keyi baki sake tarasa me zata ce, fadeelah kuwa sai jujjuyawa takeyi tace "ba tambayarki nakeyi ba."

"Kyauta aka bani..."tafada tareda cigaba da nade darduman.

"Ubanwa zai miki kyautar wannan agogon mai uban tsadan dan ubanki, inba iskanci kikayi ba wani mahaluki ne zaibaki ko kuma a ina kika sata."

Gaban sahresh ne ya fadi jin k'azafin da fadeelah ke mata "wallahi kyautar ta akamun anty fadeelah."

"Raina mun wayo sahr...tunda kin kasa fadamun ubanwa ya baki ko kuma inda kika sato zakifi iya bayani agaban mummy."tana fadin haka ta wuce fuuu...

Addu'a sahresh tafara dan tasan yau Allah kadai zai iya kwatarta gun bayin Allah'n nan dan duk abunda tafada musu ba yadda zasuyi ba.

   Tsugunne take agaban mummy inda ta kifa mata wani gigitaccen mari tace "bazaki fadamun dawa kikayi isakanci yabaki ba..."

Sahresh dake kuka tace "wallahi mummy ni banyi iskanci da kowa ba...wani dan makaran tarmu ne ya bani."

"Wayeshi a makarantar taku... Meye gaminki dashi dahar zai baki wannan tsadadden agogo wanda koni banada irin mai tsadarta..."tasake kaimata zunguri tareda hankada ta da kafa "ki fadamun wanene sunansa."

RABO...Inya Rantse!Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora