2

2.9K 152 0
                                    

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

2...

Shiga dakin Dad yayi yabi Ammi da kallon tambaya murmushi kawai tayi tadau man shafawan ta tsayaya a hannu tace "wlh Alhaji dan nan naka baida kunya cewa yayi wai nacema tunda Aisha zata gama exam next week wai please ayi bikin upper week he is tired of waiting" murmushi Abba yayi tareda daukan news paper shi dake kan gado yace "Zan sami baban Aisha da maganar gobe" da sauri Ammi ta kalleshi tace "what?" bude jaridan Dad yayi yace "I said zan sami Baban Aisha da maganar" da sauri Ammi tace "haba Alhaji kuwai maza maisa tunanin ku daban ne, mu bangaren mu mata bamu gamaba fa ina aka gama shirya yarinya eyeh" tabe baki Alhaji yayi yace "ke yanzu baki gaji da ganin katon matashi a gidan nan ba, abin dadi ne ma yaran sun kosa suyi auren gwara mumusu kafin shaidan ya shigo lamarin" yatsine fuska tadanyi tace "ai shikenan".
Saida yay shafa'i da wuturi sanan ya kwanta a kan makeken royal bed dake dakin shi, wayarshi ya jawo tareda kashe bedside lamp din dailing number dayay saving da heartbeat yayi saida wayar yakausa katsewa sanan ta dauka batare datace komiba, shiru shima yayi hakan yasa ta lumshe idonta shima lumshe idonshi yayi sanan yace "my one and only Eesha" cikin siririyar muryarta tace "kana gida?" murya Chan kasa yace "yes dear, tell me how are was your day?" ahankali tace "my day was bad" da sauri yace "why? Maisa my Eesha?" shiru tadanyi nayan sakanni kafin chan kamar wacce zatai kuka tace "I don't wanna talk about it" lumshe ido yayi in so much pain  yace "maisa baki yarda daniba, there's nothing going on between me and her, my Eesha I love you don't you get it? Zuciyata taki ce kadai, I don't think wanan zuciyar nawa zata taba son wata mace aduniyan nan sama dake, my Eesha trust me please or kinason nafara miki kuka ne?" da sauri ta girgiza mai kai kaman yana wurin murmushi yadanyi sanan yace" don't worry bayan bikin mu zan lallasheki da kyau okay" make kafada tayi tareda cewa "oh'oh" dan murmushi yayi mai kara yana kara jin wani irin zafin sonta na ruruwa a rashin, ahankali yace "wani paper kukeda shi gobe?" cikin sanyin muryanta tace "GNS221" "hope you read very well?" ahankali tace "eh" "wat time is the exam" murya chan kasa tace "afternoon paper ne 2 to 4" ahankali yace "okay" shiru sukadan yi na kusan 5 min ahankali yace "My Eesha" murya chan kasa tace "uh" kara kwantar da murya yayi yace "ina sonki dayawa, I love you so much my Eesha" murmushi tayi tasa hannu ta rufe fuskarta dashi murmushi yasakeyi yace "bazaki cemin you love me ba" turomai baki tayi tace "su Faty fa na nan" ware ido yayi yace "nizakima wayau yaran da tuntuni sunyi bacci" murguda mai baki tayi tai shiru kara kwantar da murya yayi yace "haba babyn khaleel yakuri to fadamin kodan kadanne that you love me please my Eesha" shiru tadanyi hakan yasa ya lumshe ido yana jira ahankali da dan karamin muryanta tace "I love you Ya Khaleel" dip ta kashe wayan wani irin dadi ne ya lullube shi da sauri yasake dailing number amma bata dauka ba yasan dama bazata daukaba text ya tura mata "good night my Eesha, I love you" yay sending sai bayan ta karanta message din sanan ta rungume wayan tareda yin addu'an bacci.

Shirye yake da uniform dinshi na navy bakaramin kyau dan farin rigan yasake haska bakin fatar shi, dining ya karaso ya gaida Dad da Ammi dasuke cin abincin su wayar shi ya ijiye da car key akan dining yay sama dakin kanenshi ya bude ganin suna gaban mirror Ilham nama ihsan makeup yasa yawani ja dogon tsaki yace "wlh if I count 3 baku tafi dining ba yau saida kuje school da kafa, one two" da gudu suka tashi suka dau jakunkunan su ta gefenshi suka fito ajiye cup din tea Ammi tayi tace "da kyau haba Yara sai sufi awa uku ana shafe shafen banza" zama sukayi daidai lokacin ya karaso dining Shima ya zauna ihsan tai serving nasu, Abba ne yafara gamawa yaciro 5k yabama Ihsan yace "gashi nan kuyi amfani dashi a school" ya kalli Mum nina tafi, godiya sukayi sukamai da addu'an Allah kiyaye. Shiya fara mikewa hakan yasa Ilham ta langabar dakai tana kallon Ammi, Ammi tace "Son kadan jirasu su gama nasu break din mana" hararan su yayi yace "Mum sunsan zasuyi break suka tsaya fentin fuskan su, my friend will u get up ko na tafi abina" hakanan suna kunkuni suka tashi sukama Ammi sallama. A bakin gate din Baze university yay parking kaman zasuyi kuka suka ce "Yaya Khaleel dan Allah ka shiga damu daga nan zuwa lecture hall danisa wlh" wani yar dariyar mugunta yayi bayan ya kalli kafafuwan su yace "gashi anci uban hill fa" yakara fashewa da dariya Ilham sarkin kuka harta fara matsar kwalla Ihsan tace "kai Yaya Khaleel bazamu kara batama lokaci ba" saida yagama daddana wayar shi sanan ya kunna motar ya shiga dasu sabida sundan bashi tausayi abakin lecture theater ya ajiye su tareda basu 5k sanan ya wuce aiki dan yay latti.

Tun daga nesa ya hangota tana sanye cikin sky blue hijab mai hula fuskarta fayau ba makeup, lips dinta sunyi jaa sosai hakama hancin ta, ahankali take tafiya tanadan yatsine fuskarta fitowa yay daga motar ya jingina da motar tareda rungume hannayen shi a kirji bata lura dashi ba hakan yasa ta cigaba da tafiya, dan yatsine fuska tasakeyi tareda cire Jakarta data rataye a kafadar ta bude tissue ta ciro tasa akan hancin ta ta rike sabida atishawa takeji ahankali yafara tafiya harya karasa inda take a tsaye muryan shi kawai taji akanta "My Eesha meke damunki" dago idanunta tayi ta kalleshi yana sanye da uniform alamun daga office yake idanunshi boye cikin black shade wani sassanyar murmushi ta sakin mai, hannu ya mika mata ya karbi jakan hanunta har lokacin yana kallon fuskarta yace "baki da lafiya ne?" yatsine fuska tasake yi tace "am fine just mura nake yi" ganin yanda yan school din ke ta kallonsu wanda apparently shi suke kallo yasa ta gimtse fuska tace "mutafi" bude mata front seat yayi ta zauna sanan ya koma mazaunin driver ya zauna ya tada motar suka fita daga school din ganin yanda taketa atishawa yasa yay parking agaban wani pharmacy, maganin mura yasiyo mata da bottle water sai kuma cold farm fresh yogurt, bude side dinta yayi ya tsaya ahankali ya bude kwalin maganin ya ballo guda biyu yabata tareda bude marfin goran ruwa ya mika mata yatsine fuska tayi kaman zatai kuka murya chan kasa yace "please my Eesha for my sake" hakan yasa tasha da kyar kaman zatai amai da sauri ya karbi goran ruwan sanan ya bude mata yogurt din yabata yace "take this sabida karki amai" karba tayi ya maida kofan ya rufe mata sanan ya koma mazaunin driver ya tada motar, batawani sha dayawa ba ta rufe ta ijiye,  ahankali yace "are you okay?" gyada mai kai tayi kafin ta lumshe ido within one minute bacci yay gaba da ita, murmushi yayi dan yasan tana tashi cikin dare tayi karatu ahankali yake tuki haryakai anguwan su, abakin gate dinsu yay parking ya juya yana kallon ta yanda take baccin ta hankali kwance hancin ta yay ja sosai abunku da farar fata, hakama lips dinta wani irin sonta yaji nakara shigan shi ahankali yakira sunan ta "My Eesha, My Eesha" bude ido tayi kadan kafin tabude su duka magungunan da yogurt din ya dauka yasa acikin Jakarta yabata, ahankali tasa hannu ta karba yace "ko muje hospital ne?" da sauri ta girgiza kai ahankali tace "am fine idan naje gida zansha ginger tea I will be fine" dudda baiso ba hakanan yace "okay on ur phone to, I will call you later" gyada mai kai tayi ahankali ta bude kofa ta juya zata fita da sauri yace "My Eesha" juyo dakai tayi ta kalleshi murmushi yamata yace "I love you" murguda mai baki tayi tafita da sauri, dan murmushi yayi tareda girgiza kai saida ta bude gate dinsu ta shiga sanan ya kuna motar yay reverse office dinsu ya wuce dan excuse ya dauka yafita dama.
Zaune yake akan kujera yana rubuta report da laptop dinshi knocking akayi hakan yasa yabada izinin shigowa wata kakkyawar baby ce ta shigo office din wacce akallla zatai 26 tana sanye da daoguwar riga ta yafa gyalenta idanunta a cikin black shade kallo daya yamata ya dauke kanshi akanta yacigaba da abinda yakeyi, ahankali taja kujeran gaban table din ta zauna tareda ajiya handbag dinta akan table ta cire dark shade din ta ijiye kan table idanunta har sundan kumbura sunyi ja alamun taci kuka sosai take kallonshi bataki suyi ta zama ahakaba har karshen rayuwan su at least yarage mata wahalan da take ciki. Kusan 20mins yayi kafin yagama report din yatura head quarter dinsu na Lagos sanan ya kashe laptop din batare daya kalleta ba yace "what brings you here Zainab?" da kyar ta iya tattaro courage din dayadan rage mata ahankali tace "nazo nabaka hakuri I know I shouldn't have picked d call, please forgive me khaleel" takarashe maganan tareda ciro tissue daga jakanta tana goge hawayen daya zubo mata sosai ta bashi tausayi shiya rasa mesa Zainab ke sonshi haryau bai tabajin koda digon sonta aranshi ba. Ahankali yasauke ajiyan zuciya yace "am sorry too Zeenat I shouldn't have acted d way I did jiyan, Zeenat you are too good and Charming soul, banason kiyi wasting precious time dinki akaina, u know dis, duka duka bikina baifi two weeks ba, am sorry to say but my heart belongs to Aisha kadai, please move on and kimanta dani kinji Zee" sosai hawaye ke bulbulo mata ita kadai tasan yanda takeji ahankali ta mike tsaye tadau jakanta da shade dinta tafita daga office din da gudu. Lumshe ido yayi tareda fuzar da iska ba karamin tausayi tabashi ba sosai yamata addua Allah yahada ta damai sonta haka, ganin 5 tayi yafara shirye shiryen tafiya gida.

JARABTA Where stories live. Discover now