8-9

2K 127 2
                                    

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

8&9...

"But gobe in Allah ya kaimu da safe sai mu kaishi clinic dinmu a dubashi" kowa kasa magana yay afalon da kyar Abba yace "mungode" Sallama yamusu yatafi zuciyar shi cike da tausayin Khaleel, Aisha bata amma Khaleel kai Allah gamu gareka, girgiza kai yayi yatafi kawai. Gabaki dayan su a falon suka kwana dan sosai Khaleel ke surutai cikin bacci.
Around 8 baban Aisha yazo shirye cikin suit bakake da kyar Yusuf suka fito dashi suka sashi amota sanan aka tafi asibitin wani babban likita daya kware a bangaren mental Baban Eesha ya kaisu wajen shi, nan yazo gaban Khaleel ya tsaya ya dudduba shi sanan ya Kalli Daddy dayay shiru yana kallon ikon Allah yace "Ya sunan shi?" Abba ne ya iya yay magana yace "Muhammad Khaleel" rubuta wa Dr yay a file din daya shigo dashi ya maida duban shi ga Khaleel daketa motsi da bakin shi, "Khaleel" Dr yakira sunan shi, shiru kaman ma bada shi akeba, Yusuf ne ya matso wajen ahankali yace "Dr tun randa abin yafaru bai kara mana magana ba, is as if baima sanmu ba" rubuce rubuce Dr yayi, ya dauko wani abu kaman bindiga ya daura akanshi nakusa 1min sanan ya cire, rubuce rubuce yayi sanan yamika musu prescription sheet yace "asiyo mai wanan magungunan" Ahankali Abba yace "meke damunshi?" murmushi Dr yayi yace "post traumatic stress disorder, but zai dinga zuwa therapy bayan kwana bibbiyu, and zan sashi a medication, bayan 2 weeks inhar babu improvement sai musan abin yi" godiya sukamai sanan Yusuf yatafi siyo maganin suka tafi gida.

Yau kimanin 2 weeks kenan gidan nan babu wanda bai rame ba sabida Khaleel, babu wanda yake yadda dashi baya wanka, baya ma kowa magana abinci ma ko Ammi tasamai abaki wanda yaga damane zai hadiye sauran akasa, har yanzu Baffa da Family shi basu komaba dan bazai taba iya tafiya yabar kaninshi da wanan wahalar ba yasan yanda kaninshi keson Khaleel, bashi kadai ba duka familyn ma akwai wanda bayason Khaleel ne.
10 a office din Dr yamusu ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin ya Kalli Abba yace "Sir Khaleel yaki responding to treatment, inda acema ya yarda yay magana ne ko awajen therapy dinshi ne it would have been a great difference dakomi yazo mana da sauri"  "to to Dr yaza ayi yanzu?" cewar Abba "Alhaji yanzu is time for the second treatment abinda nakeso daku shine ku cire, kokuma ku fitar dashi daga environment din incident dinan, inma da hali yabar Abuja for now, ai zaku iya daukar mai excuse a wajen aiki na medical leave ni zanmai recommending, duk wani abu dazai dinga tunama kwakwalwan shi Aishan ku nisan tashi daga abin, kana ganinshi ahaka kome daya dangan ci Aisha yasani so ku nisan tashi daga memory and ku dinga cheering dinshi up now more than ever he needs love da pampering kome yakeso kumai koma menene shizai sa yay healing fast" godiya sosai suka mai sanan suka tafi.

Koda suka kai gida kwantar da Khaleel sukayi a dakin shi Yusuf ya zauna dashi, Ammi dasu Umma Abba ya kalla yace "kubiyo ni" falo suka fita suka zazzauna Abba ne ya Kalli Daddyn Khaleel yace "inason na wuce da Khaleel yola kaman yanda Dr yabamu shawar anisan tashi daga nan koya kagani achan saimuga Yaya zaiyi healing idan babu improvement saimu fita dashi waje koya kagani" gyada kai Daddy yayi ahankali yace "to Yaya nima nafison hakan, ke Amina saiki hadamai kayan shi ko" gyada kai Ammi tayi da sauri, Ihsan da hawaye ya cika mata ido tace "Abba nima zan biku" Ammi ne ta kalleta tace "exam dazaku fara next week fa? Don't worry duk lokacin dakukai hutu saikuje ku dubashi" murmushi Umma tayi tace "addu'an ku Khaleel yafi bukata yanzu bawani abuba, Alhaji tun jiya Gwaggo ke kirana tana tambayana yaushe zamu dawo bansan mezan cemata ba" "banason na tada mata da hankali ne, idan mukoma ma fadi mata meya faru" wani irin murmushi Mujiba tayi tana kallon fuskar Daddy Khaleel tana kada kafa.

Washe gari jirgin Rana sukabi suka koma yola, haka gidan ya dawoma Ammi da kanen Khaleel wani iri, ba karamin wani iri Ammi takeji ba da kyar ta lallaba kanta ganin zazzabi nason kama su Ilham.

Yau kusan watan shi daya kenan a yola, yana zaune a dakin Goggon wacce ta hadamai fura take bashi abaki, yana sanye da farin t-shirt wacce ba karamin dambe suka sha da Yusuf ba kafin yabari asamai, ahankali Goggo ta ijiye kofin furan, tadau handky ta share mai bakin shi da rigar jikin shi dan gabaki daya fura zubewa yake wanda ya shiga bakin shi ne yake lashewa, Abba dake tsaye akansu ta kalla tace "Sama'ila ni ni wlh jikan nan nawa tausayi yake bani, ace yaro yafita daga hayyacin shi baima sanmuba yanzu" kecewa tayi da kuka sosai ta kwance bakin zani tana share fuska zama Abba yayi yace "to Mama idan kina kuka haka mumuce mene, namayi magana da baban shi dazunan, jibi zamu fitar fashi waje saudiyya zamu, akwai wani likita dana sani a wajen yace mukawoshi in sha Allah zai sami lpy har magana zai fara" da sauri Goggo tace "dagaske Sama'ila" gyada mata kai Abba yayi tace "Alhamdulillah" shafa kan Khaleel din tayi tace "Allah nagode ma, dazaran ya warke zan nemo yarinya yar kirki mai hankali da natsuwa na auramai hakan zaisa ya wartsake" tashi Abba yayi yace "bari nadan fita" "adawo lahiya" part din Mujiba yatafi a uwar daki ya sameta tana kan gado tana watsapp baiko kalleta ba ya bude wardrobe babban rigar shi ya dauka yasa sanan yace "kihada min kaya jibi zamu fita da Khaleel waje" adan zabure ta kalli Abban tace "Alhaji maisa zaka wani kashe kudin ka Yaron nan yariga ya haukace bazai taba warke wabafa" wani irin kallo dayamata yasa tadanyi murmushi ta kwantar da murya tace "bahaka nake nufi ba, ni gani nayi tayaya treatment din zaiyi progressing bayan baya cewa uffan balle asan meke mai ciwo daka bari yafara magana tukun, duk kawani damu saikace Yusuf ne baida lpy" wani irin kallo ya watsa mata ya nunata da yatsa cikin fushi yace "ki kiyaye ni Mujiba, ki kiyayeni fa, and Yusuf da Khaleel basu da bambanci awurina duk yayana ne, baki isa kiraba kan family naba kinajina ko" fita yay daga dakin ranshi abace, sosai abin ya konama Mujiba rai, ai wlh yanda naso kaninka yakini, dasonshi nake wahala da dawainiya, bankara ganin farin ciki ba, haka danshi ma zai wahala bazai taba samin farin ciki ba arayuwar nan ba, ko Allah ma nabaya na, ai saisa ya kashe yarinyar batare danai komiba, warke wa dai bazaiyi ba bi'iznillahi, koma ya warke farin ciki yakare mai arayuwa. Tsaki tayi ta wurgar da wayar ta tashi ta shiga bayi.

Saudiyya.
Ba karamin cigaba aka samu a treatment din Khaleel ba, dan yanzu dazaran yaji kiran salla zai tashi yay alwala yayi, magana ne idan anmai saiyaga dama zai amsa, gabaki daya ya chanza ya dawo shiru shiru kaman ba Khaleel mai rahan nan ba, idan Ammi tabashi abinci zaici kadan ya ijiye mata, idan yagaji ya kwanta ya daura kanshi akan cinyar ta ya lumshe ido, sosai aka dage damai addu'a dudda haka sunji dadin yasoma samin cigaban nan. Dr yahana amai maganan Eesha ko kadan. Ganin cigaba sosai yasa Dr ya sallame su suka dawo Nigeria Ammi da Daddy suka wuce Abuja, Baffa da Yusuf suka wuto dashi nan yola.

JARABTA Where stories live. Discover now