42 - 50

4.1K 138 1
                                    

[6/19, 12:31 PM] Aishat Muhammad: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

42...

Dan ajiyar zuciya ya sauke wani irin abu yaji yana fizgar shi, ahankali ya kama lips din nata kokarin kawad da kanta takeyi amma bai bata daman yin hakan ba, sunkai wurin 2mins ahaka kafin ya saketa da sauri tareda dukan bangon wajen har saida ta tsorata yajuya da sauri yabar backyard din yana share kwallan dayaji tana zubomai batare dayama lura da gabanshi ba, karo yaji yaci da mutum hakan yasa ya dago kai tareda saukar da hanunshi dayake goge kwallar yaga Anty Hindu ce tanamai wani irin kallo da muryar shi daya dishe yace "sorry" da sauri ya wuce tsakar gidan ya shiga mota yay horn yafita daga gidan yama Yusuf text "please kabata kudin dazaka bata kafito ina waje".

Ahankali Anty Hindu ta cigaba da tafiya harta karasa backyard din toculan wayarta ta haska jin sheshekan kuka taga Islam a tsugunne hakan yasa tace "ke lpy ki lau, mekike yi" da sauri Islam ta mike tana goge fuska tadanyi murmushi tace "am fine" bude kofar kitchen tai ta shiga ta wuce sama da dan gudunta Indomie dabataci ba kenan.
Anty Hindu tafi minti biyu tsaye a wajen sanan ta girgiza kai ta bude kofa ta shiga cikin gida.

Washegari Friday gidan ya cika da mutane Ibrahim da Ya Abdallah ne kawai basu sami daman zuwaba, Ibrahim nafama da exam shikuma Abdallah training bazaka iya tafiya ba sai bayan training din wata shida.
Tana zaune adaki ita kadai da kumburarrun idanunta kadaici yamata yawa gashi bawaya balle koyar wassap ta shiga, Farida ne tabude dakin ta shigo da wasu kawayen ta su kusan biyar kallon banza sukama Islam hakan yasa ta saukar da kanta tareda daukan littafin azkar dinta dake gefen pilo tabude tana karanatawa, Farida ce tai tsaki ta matso wurin gadon tana hararan ta ta rike waist sanan tace "naceba, kindaiga I come peaceful yanzu kawai zan fadamiki ne karkizo wajen walimana banison evil eye dinki yay affecting anything koba hakaba ladies?" ta kalli kawayen ta da sauri sukace eh hakane, Farida takara kallonta tace "idan kuma kinzo u know wat I can do wlh saina kusa ballaki" tai tsaki ta kalli sauran yan matan tace "kumuje" binta sukai abaya tabisu da kallo hawaye taji zai zubo mata da sauri ta girgiza kai dan batason tayi amma kasa daurewa tayi tadau pillow ta cusa fuskarta aciki tana kuka sosai ita kadai tasan yanda takeji.
Haka tawuni adakima ranan Mum sai shigowa da kawayen ta take tana nunata, karfe 4 aka tafi walimar tashi tai tai salla takara watsa ruwa kotadanji dadi tazo ta kwanta, Koda daddare ma da kyar bacci ya kawsheta.

Wani irin mugun ciwon ciki ta tashi dashi ranan asabar din, da kyar ta tashi ta dauko jakarta tadau maganin ta tasha sanin Mp ne, sanan ta wuce bayi tai wanka tafito ta kintsa ta kwanta bama taso tafita waje taga mutanen biki, Maman Miemie ne tashigo dakin sanye da kayan anko tai kyau abinta hanunta rike da kula tace "Anty Islam ga abinci Anty Hindu tace nakomiki" karba tayi ahankali tace "nagode" fita tayi daga dakin, daukan flask din tayi tabude tafara cin jellof Rice din ciki aka bude kofa aka shigo Farida ne taci wani ubansu leshi pink anmata makeup sai uban kamshi takeyi tsayawa tayi agaban Islam tawani juya tarike kwankwaso tana murmushi tace "Ya kika ganni ta Allah bataki ba yar bakin ciki" kawad dakai Islam tayi ta cigaba dacin rice dinta, tahowa gabanta Farida tayi ta fizge flask din rice din ta ijiye agefe hakan yasa Islam ta mike a zuciye tace "Farida leave me alone" ta nunata da yatsa idanunta sunyi jaa, wani dariyan dadi Farida tayi dan kana ganin fuskar Islam kasan dauriya kawai take but abuna cinta azuciya, komawa baya da baya Farida tayi tana murmushi ta nunamata agogon dakin tace "3 hours from now nadawo ta My superman so start counting, yanzu karfe goma my darling haha" tafashe da dariya wani irin kuka Islam taji yazo mata data rasa name pillow ta dauka ta jefama Farida tace "get out of here" kome ta raruma jefama Farida take tana kuka da sauri Farida tafita daga dakin tana wani irin dariya harda kama ciki sabida dadi, zama Islam tayi akasa tasanya kanta acikin kafafunta tana kuka sosai data rasa na menene, shinkafar kulan ta ture da kafa ta zubar tana kuka, kofa aka bude Anty Hindu tagani rike da kayan anko a hanunta tana karema dakin da ita kallo da sauri ta ijiye akan gado ta karaso ta daga Islam tace "ke lafiyan ki kalau kuwa mekike yi haka" da kyar tai shiru ta share fuskar ta sanan tace "kaina ke ciwo" paracetamol Anty Hindu tabata tasha sanan tadau kayan ankon ta bata tace "oya ga dinkin ki nan jekisa ina jiranki" karba tayi ahankali badan ranta yasoba ta shiga bayi tasaka kayan sanan tafito doguwar riga akamata da akabi pattern din atampar da stones yay mata kyau sosai dan yadan kamata ya fito da shape dinta sosai, Anty Hindu ta tasata agaba ta shafa yar farar hoda sanan takama hanunta ta tafi da ita dakin ta da wasu kawayen ta ke ciki, zaunar da ita tayi akan gado sanan ta zauna itama sunata fira da kawayen ta.

JARABTA Where stories live. Discover now