4 - 5

2.2K 136 0
                                    

*JARABTA*

Maman Abd Shakur

4&5...
Dankakaren falon gidan su acike yake dam da yan uwa dan yau Alhaji Ismail wan baban Khaleel wanda suke kira da Abba ya iso daga Yola tareda yaranshi da matayen shi biyu, Hajiya Amina wacce itace babba yaranta uku Mustapha babban danta da yanzu yay aure matar shi bata haihuwa, sai Yusuf shine na biyu shine saan Khaleel tare suka taso sun shaku sosai, sai autar su Fa'iza wacce ke SS3 a boarding school. Amaryan Abban Kuma Mujiba yarta daya wacce takeda shekara daya aduniya, gabaki daya falon ya kachame da hira idan ka gansu gwanin ban Sha'awa.
Yusuf ne ya kalli Khaleel dake danna waya yana shan tea yace "kai tashi muje mu amso dinkin mu, and su Shareef na jiran mufa a barrack dinku" yatsine fuska yayi sanan ya maida wayar aljihu ya harare shi yace "muje" tashi sukayi Yusuf yace "Abba zamudan fita" da sauri Ihsan tace "Ya Yusuf ku dawo dawuri fa, 4:30 daidai ne walimar babu afircan time" ta kalli Fa'iza da Ilham tace "ku tashi muje gidan su Aisha ma, nasan amma fara lallen tanata min flashing" Car key Khaleel ya dauka suka fita dukan su tare.
Karfe 4 aka fara tafiya da kawayen amarya wajen event din ganin su Eesha basu fitoba yasa Mama ta shiga dakin nasu, su Ihsan ne da wata kawar Eesha wacce suke aji daya anan University Abuja. Kasa magana Mama tayi ganin yanda Eesha tai mugun kyau abunka da wacce bata saba kwalliya ba, murmushi su Ihsan sukayi, Ilham tace "Mama tai kyau ko, Fa'iza ce tamata makeup dinan" murmushi kawai Mama tayi tajuya tabar musu dakin, ahankali Aisha ta dago kanta ta kalli fuskar ta a madubi murmushi tayi sabida taga tama kanta kyau, Khadija ce ta dagata tace "tashi muje, yau idan Khaleel ya ganki na tabbata hmmm" dariya sukayi bakaramin kunya taji ba ta turesu tafita daga dakin da gudu, binta sukayi nan suka shiga motar da aka barmusu driver ya jasu zuwa wajen venue walimar.
Wa'azi aka musu mai ratsa jiki, mai sanyaya rai mai kara Imani, sosai kowa yay hawaye, barinma amaryar, bayan angama aka rarraba kyaututtuka akai ciye ciye sanan aka fara kawo motocin komar dasu gida. Gaban wata babar jeep Khadija ta kaita kirar Brabus, bude marfin motar tayi ahankali ta shiga sanan ta mayar da kofan ta rufe juyawa tayi da sauri ta wuce ta shiga wata motar daban. Kin dago kanta tayi dudda taji yanda kamshin turaren shi ya bude motar, cikin wani irin calm voice taji yacema driver mutafi. sundan jima suna tafiya kafin ahankali ta dago kanta ta kallai karaf suka hada idanu hakan yasa ta juyar da kanta da sauri tana murmushi.
Parking motar taji anyi anbude gaban motar anfita matsowa yay kusa da ita kadan dawani irin murya chan ciki yace "wife" duk yanda taso karta kallai hakan ya gagara samin kanta tayi da juyowa ta sauke mai kyawawan idanunta akanshi, ganin kallon dayake mata yay yawa yasa ta huramai iska a fuskar murmushi yayi, ahankali tace "Mesa kake kallona haka?" takarashe maganan tana turamai baki, murmushi yasakin mata kafin yakara matsowa kusa da ita, da sauri tai yunkurin matasawa hannunta yarike yana wani irin kallon fuskar ta, jikinta ne yafara rawa ta bude baki zatai magana, dayan hanunshi ya daura akan lips dinta yana girgiza mata kai da idanunshi dasuka xhanza launi kaman basuba, ahankali yadaura goshin shi akan nata lumshe ido yayi jin yanda take numfarfashi, dawani irin murya yace "ina sonki sosai my Eesha" Ahankali ya dago da kanshi hannu yasa yay cupping fuskar ta sauke idanunshi yay akan lips dinta dake shining sabida Jan bakin dasuka ji wani irin abu ke fizgar shi ahankali yakai bakin shi zai daura da sauri ta kawad da kanta kirjinta na mugun bugawa dan tunda take dashi baitaba mata hakaba, wani irin hawaye ne ya zubo mata tai sauri  ta share sanan tadan kalli fuskar shi wanda ita yake kallo da idanunshi dasuka kankance kofa ta bude da sauri tafita ta bude gate ta shiga gidan su. Yafi minti uku a zaune kafin ya bude kofar ahankali yafito front sit yakoma ya kunna motar yaja yabar wajen.
Gaishe da kawayen Mama tayi dake falon a kunyace ta wuce sama, su Khadija da Ihsan ne ke gwada kayan ankon su da aka kawo musu, zama tayi a gefen gado tana yatsine fuska tace "wash Allah wlh nagaji" dariya duka yan matan sukayi Khadija ce tace "ai dole sannu kinji" yanda tai maganan yasa Ilham ta kwashe da dariya tace "ai Yaya Khaleel shegen naci shi bazaima bari gobe tayiba yawani..." hararan ta Eesha tayi tace "yan sa ido Yaya Khaleel dina baida naci duk cikin sone" kama baki dukan su sukayi suna kallonta cike da mamaki, Ihsan ne tace "iyye kike karemai muma Allah bamu mai sonmu" dariya tayi tareda cire doguwan rigan jikinta ta yarage saura shimi da dogon sket, ta ninke ta ijiye akan gado, murmushi tayi ganin fuskar Khaleel namata gizo, hannu tasa ta cire dan kunnen kunnenta ta ijiye agaban mirror sanan ta juyo ta kallesu ganin duk ita suke kallo yasa tasake murmushi tace "bazaku gane yanda nakeson yayan nan naku bane, inama Ya Khaleel son da ina ganin ko bayan namutu banjin son zai mutu ba, Ya Khaleel namijin tal da har yau banga irinshi ba, mutum ne mai tausayi, kirki ga amana da addini, nasan yanada matsalan zuciya da yawan fushi but alkairan shi sun mamaye wanan, sabida Ya Khaleel ne Auta ke raye da yanzu ya mutu, kuntuna randa gidan mu yakama da wuta duk anfito damu but Auta na ciki, Ya Khaleel was d one daya koma duddu uban wutan nan yaje ya dauko Auta, saida ya kone a hannu garin hakan, haryau tabon na jikin shi"  share dan guntun hawayen daya zubo mata tayi ta mikama Ilham da Ihsan hannu tace "Yaya Khaleel dina is my everything bazan taba son wani sama dashi ba" murmushi tayi ta sake su ta wuce bayi danyin wanka.

Banjin daga Khaleel har Eesha wani daga cikin su yay wani bacci mai kyauba, Eesha su Ihsan da Khadija ne suka tasata agaba wai takosa, shiko Khaleel abangaren shi Yusuf da friends dinshi ne suka tasashi gaba wai yakosa yaki bacci dariya yay yaki musu magana.
Misalin 9:30 nasafe na ranan bikin mutane sun cika gidan makil, Aisha ce zaune akan gadon dakin ta tasa wata atampa English wax da aka mata stone work yay kyau sosai, wayarta ta dauka tai dailing number Khadija ringing daya ta dauka, tace "Eesha am coming back yanzu na siyo agogon, gama ninan nafito daga Dunes Abuja taxi nake nema nahau" murmushi Eesha tayi daya mugun kara mata kyau tace "nagode Tawas, kiyi sauri please inaso nabashi yasa kafin lokacin daurin auren ne" katse wayar tai tana murmushi tun jiya bai kirata ba tasan hala fushi yakeyi, murmushi tayi tadau wayar Flashing tama su Ihsan dan sun tafi gidan su dauko kayan makeup din Faiza sunki dawowa.
Wuraren goma da rabi Khadija ta dawo da sauri Eesha ta karbi ledan da akwatin agogon ke ciki, ciro agogon tayi ta bude daga box din wow tace, agogo ne mai kyau Rolex wanda tasaimai da kudin ta 75,000 naira, gashin golden color rufewa tayi ta dau wayarta dailing number Khaleel tayi saida takusa katsewa sanan ya amsa. Murmushi tayi kafin yay magana tace "am sorry Yaya Khaleel" Ahankali ya lumshe ido danji yayi wani sanyi ya ratsa zuciyar shi, dawani irin murya tace "kana ina kana gida ne?" dan murmushi yayi sanan yace "a'a muna bakin layi shagon dinki Ibrahim tela, kayan dazamu sa gabaki daya fashion designer damuka bama dinki yamana wandunan sunyi tsawo sosai shine muka kawoma Ibrahim yarage mana, Mesa kike nemana Kuna bukatan wani abune, nazo?" girgiza kai tayi tace "a'a kabarshi bari nina zo, I want to give you something, something special" da sauri yace "kina amarya kifito akalle min ke lallai to naki, bari am coming" dan dariya tayi sanan tace "ni to ai kofar gidanmu da mutane banaso su ganmu tare ne saisa, Kuma su daddy ne da friends dinshi, saisa nakeson nazo am coming" katse wayar tayi tadau dogon hijabin ta har katsa tasa, Khadija dake shiryawa tacema "Ina zuwa, insu Ihsan sunzo afara miki makeup din, bari nakaima Khaleel wristwatch din" tafita daga dakin a tsakar gida taci karo dasu Mama da yayyin ta, kallonta daga sama har kasa Mama tayi tace "ina zaki haka" Kaman zatai kuka tace "Mama abu zanbama Khaleel a waje plzz" Mama zatai magana Yarta dasuke Kira da inna asabe tace "tafi kinji Eesha" ta kalli Mama tace "kibarta mana daga yauma gidan mijinta zata koma tabarmiki gida, tunda yana kiranta aisaitaje" da sauri tafice tana dariya dan tasan Mama da hanata zatayi, hango su Baba tayi a barander waje hakan yasa taja gaban hijabin ta dan karsu ganeta tazo ta wuce tafita sadaf sadaf daga gate din, da sauri take tafiya hartakai bakin titi, yana tsaye a shagon ya hangota zata tsallako kasan cewa kofar glass ne a shagon, murmushi yayi yacema Yusuf "am coming my queen wanna see me" hararan shi Yusuf yayi shikuma yajuya yafita daga shagon, tana hango shi ta sakin mai murmushi, murmushi yamata sanan ya mata alamu da hannu ta tsaya bari shi ya tsallako, murmushi tasake yi ta make kafada sanan ta kalli titi ganin babu wani abun hawa yasa ta shiga titi ta tsallake first lane, hakan yasa shi ya tsaya yafasa tsallakowa yana mata tattausan murmushi. Kaman ance ya waiga nan yaga wani trailer daya dauko yashi yataho dawani irin mugun gudu tsaki yayi yace "Wayan nan reckless drivers dinan ko" alamu yakara yima Eesha da hannu ta tsaya, gyadamai kai tayi Dan trailer kawai take jira yawuce ta tsallake titin nabiyu, kara taji hakan yasa ta kalli trailer da sauri tayan gaban ne yafashe hakan yasa motar fara kwana, ganin motar yayo dakalin tsakiyar titin datake tsaye zai fadi akai yasa tai ihu "subhanallah Wayyo Allah" tai baya da sauri ta fada titin bayan ta, kararrarraaa naji wani irin kara dayasa gabana bugawa.

JARABTA Where stories live. Discover now