70 - End

5.9K 151 2
                                    

[6/30, 4:59 PM] Aishat Muhammad: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

71 & 72

Dafe kuncinta tayi tana shafawa, jikinta har wani irin barbar yake sabida yanda taga fuskar shi bata taba ganinshi hakaba, nuna ta yay da yatsa cike da bacin rai, dawa ta irin kakausar murya yace "ni kike gayama magana haka akan wacce ta kusan kaiki lahira? Ni kike ma rashin kunya?" kasa magana tayi saima jada baya da tafara yi tana kuka sabida yanda taga idonshi ba karamin tsoron shi taji ya shige ta ba, wani irin kallo yamata abubuwan data fadin mai yana yawo akanshi juyawa yay yafita daga dakin tareda bugo kofar sabida tsabagen yanda ranshi yabaci.
Zubewa tayi a wurin tafashe da kuka sosai tafi hour daya tana kuka daga baya bacci yay gaba da ita anan kasan.

Dakin Ihsan ya shiga ya zauna tareda dafa kanshi yafi minti biyar ahaka dan rashin yay bala'in baci da kyar ya mike tsaye tareda fuzar da iska yawuce ya shiga bayi ya dauro alwala yadawo dakin yasaka jallabiyar shi daya dauko ya kabbarta salla.

Ahankali take bude idonta ganin gari yay haske yasa ta mike tsaye da dan sauri, cije baki tadanyi sabida zafin dataji ta bude kofar bayi ta shiga brush tafara yi sanan ta gasa kanta tai wanka ta dauro alwala tadan lumshe ido sabida yanda taji kanta namata ciwo, towel ta daura tabude bayin tafito hada ido sukayi yana sanye da jersey ya zauna abakin gado yana daure igiyan sport shoe din kafarshi, kallo daya yamata ya dauke kai tareda cigaba da abinda yakeyi kasa karasowa cikin dakin tayi ta tsaya a wurin tana wasa da yatsun ta wani irin shakkar shi taji tanayi karan fesa turare dataji yasa tadaga kai tadan kalleshi yana tsaye gaban mirror yana fesa turare ahankali tace "ina kwana" ijiye turaren yayi bayan yagama fesawa yajuya zai fita daga dakin batare daya kalleta ba yace "kintashi lpy" baijira mezata ceba yabude kofa yafita daga dakin, kofan tabi da kallo yanda yabuga kofar har cikin ranta saida taji ta runtse ido, wani irin kuka ne taji yazo mata tafara kukan da kyar ta shiru tawuce wardrobe taciro wata simple doguwar riga ta saka tadau hijabi tasa tai salla, ta dade zaune tana azkar daga baya tamike ta cire hijabi ta ijiye jin tanajin yunwa sosai. Dakin tafara gyarawa tass tafashe ko ina da turaren daki sanan ta shiga dakin Ihsan din nanma ta gyreshi tass sanan tawuce falo ta gyara dudda babu wani datti ta shiga kitchen din, shiru tayi tana kallon ko ina wani irin kuka ne taji yazo mata, Indomie da tagani kawai ta iya dauka da kwai daya ta dafa ta juye adan karamin plate tadau fork tawuce dakinsu tadan ci dan jitayi batada wani karfin cin abincin, magungunan ta dake gaban mirror tagani wani kuka takara ji yazo mata inda yana nan dashi zai bata da kyar ta mike tsaye ta dauko su tasha tahada da paracetamol duk tasha tafito da kwanon tazo ta ijiye ta kwanta akan doguwar kujera tana kallon TV ahaka bacci yay gaba ita. Wuraren 2 ya shigo gidan na rana ya dade tsaye afalo yana kallonta karfin yawuce ciki yayo wanka ya fito daure da towel ya zauna akan kujera yaja laptop dinshi booking flight yamusu dazai tashi gobe dan shima jitayi duk ya gaji da garin gwara ya koma Abuja kawai yafara aikin shi, karfe 11 nadare jirgin nasu zai tashi gobe mayar da laptop din yayi yarufe ya dauko mai ya shafa sanan yadau kayan dazaisa yafita daga dakin yakoma dakin Ihsan yay kwanciyar shi.

Karan dataji yasa ta bude ido ahankali tana karema falon kallo, a kitchen ta ganshi tsaye yana kokarin daukan heater kettle yana sanye da farar singlet dayar 3 quarter kafarshi cikin slippers, tashi tayi daga kujeran tazo wajen kitchen din yanajin ta amma yaki kallonta hanunta yaji ta daura kan nashi cikin sanyin murya tana kokarin karban kettle din tace "kawo nasama, mekake so nama?" batare daya kalli fuskarta ba yasa dayar hanunshi yacire hanunta dake kan nashi ya bude tap yatara kettle din yana diban ruwan, saida ya dibi daidai wanda yakeso sanan ya kashe tap din yarufe kettle din yajona shi da igiyar shi, dan juyowa yay ya kalleta yace "i can manage" ta gefenta yazo zai wuce tariko hanunshi da sauri muryan ta har rawa yake tace "am sorry, dan Allah kayakuri idan kaji haushin abinda nace jiya ne, babu yanda zanyi ne Farida yar uwata ce, my only sister kaji" takarashe tana wani rera sabon kukan dan juyowa yay ya kalleta hakan yasa tadan tsagaita kukan datake yi, hanunshi ya fizge daga nata yakara mata wani kallo sanan yace "nasani i know she's ur only sister" ya maimaita mata maganar da tamai na karshe yawuce wurin kettle din ganin yana tafasa ya kashe ya dauko mug zai juye ruwan aciki da sauri ta tsayar da kukan datake yi tazo wurin tace "kawo natayaka" daukar kettle din yayi ya tsiya ya ruwan aciki batare daya kalleta ba yace "zan iya da kaina" ajiye kettle din yayi ya dauko nescafe ya zuba aruwan da honey sanan yadau spoon yafita daga kitchen din yawuce falo ya barta anan, yana gamasha anan falo yabar cup din ya shiga ciki ya chanzo kaya zuwa Jean da t-shirt daya daura jacket akai yazo yafita daga gidan, wani irin abu taji ya tsaya mata arai hawaye kawai taji yana fita ta dinga goge wa ranan hartai bacci bata ganshi ba, da safe ma data tashi bata ganshi ba tadai ga note a gefenta kan gado daya rubutu ta hada kaya yau zasu tafi wani dadi ne taji ya lullube ta zataje taga Farida, bayan sallan Isha ya shigo gidan afalo ya sameta zaune da doguwar riga ja ajikinta ga akwatin su babba data hada kaya ta fito dashi falo, baiko kalleta ba ya shigo yaja jakar yafita da ita waje sanan ya dawo duk tana tsaye, tashi jakar yafito dashi batare daya kalleta a yace "muje" bayanshi tabi jikinta duk asalube suka fito ya kulle gidan yabama Raymond dake waje key da wasu kudi Yaron yarakasu har wajen mota suka shiga yana daga musu hannu suka wuce airport. Bayan sunyi checking in suka zazzauna suna jiran afara boarding, goma dayan kai aka fara boarding suka shiga jirgin nan jirgin ya tashi jarida yake ta karanatawa abinshi chan yaji kanta akan kafadar shi Jaridar yarufe yadan kalli fuskarta bacci yaga tanayi hakan yasa yadan gyara mata kwanciya tareda sauke ajiyar zuciya shima ya lumshe ido.
Karfe tara da minti arba'in jirgin su ya sauka a airpot din Abuja, ahankali take bude ido harta bude su duka hada ido sukayi hakan yasa ya dauke kai da sauri, daga kanta tayi daga kafadar shi tana zare ido, fara fita akayi daga jirgin hakan yasa yatashi itama ta tashi sauka sukayi wata mota tazo ta dauke su ta ijiye su a gaban luggage claim nan suka jira akwatinan su suna zuwa ya kwasan musu ya gungura tana bishi abaya suka fita daga arrival din wani driver sune da Ammi ta turo musu yazo ya karbi akwatinan daga hanun shi yana gaidasu cikin fara'a, Khaleel ne ya amsa suka shiga motar sukabar airport din. A wuse gaban wani babban gida driver yay horn aka bude musu suka shiga ahankali tafito daga motar mai gadi yazo ya cicciro akwatinan daga bot shikuma driver yakoma cikin mota yamusu sallama yabar gidan, kofa ya bude ya shiga haka yasa tabi bayanshi duk agajiye wani hadadden duplex ne, falon anmai fentin brown da milk, furniture din cikima kalan su kenan, upstairs dataga yayi yasa tabi bayanshi dadan sauri wani falon tasake gani a upstairs din sanan ga dakuna uku, wani daki taga ya shiga kasa binshi tayi tabude dayar dakin akwatin ta da tagani adakin yasa ta gane nanne natama, karasa shiga dakin tayi tana karema dakin kallo anma dakin fentin baby pink ga akwatin ta da aka jera asaman wardrobe kaya tacire ta shiga bayi tai wanka Koda tafito abinci tagani lafiyayyen white rice da stew ga farfesu agefe duk anjera mata a tray, salla tafara yi sanan tazo ta zauna taci iya cinta ta ijiye sauran akan drawer gefen gado ta kwanta sabida ta mugun gaji within 2min bacci yay gaba da ita.
Koda tatashi da asuba tai salla tai karatun al Qur'ani sake komawa bacci tayi sai wuraren 7: 30 ta farka bayi ta shiga tadan kuskura bakinta tafito tasaka hijabi, ahankali tabude kofa tafito daidai shima yafito sanye da uniform dinshi na navy bakaramin kyau yayiba, dauke kai yayi da sauri daga kallonta, harda dan saurin ta takarasa gaban shi ahankali tace "good morning" batare daya kalleta ba yace "morning" juyawa yay zaibar wajen ta bishi da saurin ta ahankali tace "uhmm dan Allah kadan kiramin Abba inaso inyi magana da Farida ne" batare daya kalleta ba ya cigaba da sauka daga kan stairs din sanan yace  "bazan kiraba" da kyar ahankali tace "to yaushe zamuje yolan?" baiko kalli fuskarta ba yace "babu inda zaki" wani irin kuka ne taji yazo mata, fita daga gidan yayi da sauri, ta dade tsaye a wurin tana hawaye sanan takoma dakint.
Saida taji yunwa na neman mata illa sanan ta sauko kasa tana neman kitchen sallama dataji yasa ta amsa wata ma tace da zatai 29 haka tanadan murmushin ta tashigo tace "sunana kande nice mai tayaki aiki mai gidan ne ya turo ni, ai tunda akazo akai jere nike zuwa kullum Ina gyara gidan, yau da safe ya kirani yacemini kun dawo nazo natayaki aiki" dan murmushi tai ta gaishe da Matar, tare suka shiga kitchen suka dafa abinci mai rai da lafiya sai kallon yar torch light phone din matar take ahankali tace "indan ari wayar ki?" da sauri Kande tace "eh gatanan" ta dauka ta mika mata karban wayar tayi tafita daga dakin taje parlor ta zauna number Abba tasaka tai dailing ringing biyu Abba ya daga da sallama da sauri tace "Abba Ummi ce" murmushi Abba yayi yace "Ummi dazuko nake tambayan mijin ki ke yake sanar dani yana wajen aiki toya kuke ya karfin jikin naki" ahankali tace "Alhamdulillah Abba ya Farida" ajiyar zuciya ya sauke yace "ga Farida nan sai addu'a batama San wanda ke kanta ba" wani kuka ne taji yazo mata hakan yasa ta taushe bakinta "amma muna ta addu'a in sha Allah zata sami lpy so karki damu kanki ki kula da kanki kinji kinsan kema baki dade da samin lpy ba, Allah muku albarka duka" kasa amsawa tayi ta katse wayar tafashe da kuka sosai, kande tafito daga kitchen din da gudu tana lpy, kasa amsawa Islam tayi saima kukan datake yi da kyar tai shiru ganin yanda Kande dukta damu ta mika mata wayarta dadan murmushi tace "Ya tace batada lpy" Kande tace "to ai addu'a zaki mata ba kukaba Allah bata lpy" ahankali tace "Ameen nagode" share idonta tayi tace "dan Allah tayani diban abinci kibama su mai gadin, kema ki diba" murmushin dadi kande tayi sanan tace "to" diba tayi ta kaima su mai gadi Sanna itama tazo tadiba a yar kula tamata sallama ta tafi.

JARABTA Where stories live. Discover now