Babi na ashirin da biyar ( 25 )

925 92 5
                                    


Gidan Amarya

  Sai da ya kulle kofofin gidan gabadaya sannan ya karasa ciki. A ranshi yana tunanin duniya kenan juyi juyi, yau shine da kulle Gate in gidan sa da kanshi sabanin da yana cikin mota sai dai maigadi ya bude mai ya shigo. Karawa godewa Allah yayi ga dukkan arzikin da ya mishi. Bai samu Fadila a falo ba hakan ya bashi daman karasa dakin ta. Karan ruwan da yaji ya tabbatar mishi da tana wanka ne. Dakin ta ya bi da kallo cike da mamakin dumbin dukiyan da aka maka a ciki. Gado ne Royal na gani na fada ya sha kyau har ya gaji, kana gani kasan Naira ta sha kuka. Hakama kujerun ta royal in ne suma dai nairan ce ke magana. Girgiza kai yayi cike da takaici ya karasa dakin sa yana mai bakin ciki al'adun da Bahaushe ya daura wa kanshi. Shiyasa nan da nan kaji gori ya shiga tsakanin miji da mata. Ya so hana yin kayan dakin da sauran su amma ko da ya samu Mama Aisha da maganan, baki ta bashi akan kawai ya bari ayi tunda dai al'adan yazo da haka. Haka nan dole ya hakura Amman fa duk da haka shiyasa TV in shi da sauran kayan kallo gabadaya. Da fridge, freezer, washing machine, carpets da curtains in gidan gabadaya. Tabbas kudin shi sun ragu amma still akwai rufin asiri sosai. Abinda Sumayya ta kasa jurewa kenan saboda a da in tabbas ya sangartar dasu dayawa. Mostly hutun su a waje su ke kuma har da kannen ta su ke tafiya, dole zama ba wadannan ya gagare ta.

Shima wankan yayi ya sako jallabiyan shi mai laushi da gutun hannu mai botir a gaba. Cikin natsuwa ya gama shirin sa sannan ya nufi dakin nata bayan ya feshe jikin shi da turare. Zaune ta ke a kan gado tana danna wayanta ya shigo dakin. Kamshin turaren shi ya sanar mata da isowar shi. Its just very cool ba irin masu karfin nan da maza ke sawa ba. Tunda ta San sgi da irin su ya ke amfani dayawa ba iri daya ba Aa yana da perfumes kala kala kuma dukkansu are cool. A hankali ta amsa mishi sallaman da ya mata ta yi dan gefe kadan da wayan hannun ta. "Baki jin bacci ne kike danna waya?" Tambayan da ya mata kenan. Bata amsa sai saurin ajiye wayan ta yi akan side drawer in da ke gefen ta. Zumbulelen hijab in da ke jikin ta ya karewa kallo ya saki shu'umin murmushi ya ce mata "sanyi kike ji ne haka?" Maimakon amsawa kanta kawai ta sunkuyar kasa. "Kiyi alwala kizo ki same ni a dakina" fita yayi ba ta cika 5 minutes ba ta bi bayan shi cike da tunanin ya zata shiga dakin nashi. Tsaye ta ke a bakin falon shi tana kokonto ta ji yana fadin "shigo mana Fadila" luckily yana falon yana kallon TV. Tana sallama ya kashe ya juyo ya fuskance ta. Sallaya ya dauko su ka gabatar da sallan Nafila tare da addu'oi. Ba za ta iya tantace wani irin hali ta ke ciki ba a yanzu da ya ke ta faman addu'a kawai dai gata nan ne sabanin shi da rabin tunanin shi naga tsohuwar matar shi. Daman akwai ranar da zai kebe da wata mace ba Sumayya ba? Abinda ke ta mishi yawo kenan. Hakika Sumayya ta yaudare shi, taci amanar soyayya sannan kuma most importantly ta cuce yaran da ke tsakanin su. Gaskiya shi kam so ba ta mai rana ba, anya zai iya kara budewa wata ya' mace zuciyar shi kuwa? "Yakama ta kici abinci ko?" Saurin girgiza kai yayi tace "A koshe nake, naci abinci bayan magreeb" da okay ya amsan ta yace "bara na sa freezer to amma kayan ruwa kam zaki sha" nan ma girgiza kan tayi. Harara ya aika mata yana fadin "come on Be free with me Fadila, I brought your favourites. You will like them" Wani katon nylon ya dauka ya fita dasu. Karamin fridge in da ke Fallon shi ya bude. Youghurt in na gari, hollandia fresh milk da strawberry sai citrus five alive ya fiddo daga ciki. A gaba ya sa ta sai da ya tabbatar ya zuba mata kowanne a cup ta sha sannan ya gamsu she is okay. Hannun ta ya rike duka biyu ya dagota sannan ya ja ta zuwa cikin dakin nashi. Hannun ya sa ya cire mata hijab in da ke jikin ta ya nade ya ajiye a side "ban so ana samun hijab matukar mu biyu ne kadai a gida" hannun ta ya kara ja zuwa toilet ya miko ta sabon brush tayi . kunya ya hana ta tabuka komai musamman in su hada ido dashi. Rigan da ke jikin ta irin mai bin jikin nan ne silk mai laushi sosai gabadaya ya manner mata a jiki duk da dogon hannu shi kuma akwai tsawo. Karfin Ac in dakin kadan ya sa saboda yanayin garin na sanyi. Ba dankwali a kanta ta yi parking kan da babban ribbon. Gado ya nuna mata "kwanta man's faddi you looks sleepy" da Saudi ta hau kan gadon ta lullube cikin bargo. Daman akwai ta da jin sanyi nan da nan bacci yayi awon gaba da ita. Murmushi yayi ganin yanda ta ke baccin ta hankali kwance, yanda ta ke karawa dukunkune wa cikin bargo ya fahimci sanyi ta ke ji. Kashe Ac In yayi gabadaya ya kunna mata heater ya dan yi warming dakin sannan ya kashe. Baccin ta ta ke peacefully. Fadila, yarinyar ta dade tana burge shi, yana da alwashi akan ta sosai ganin yanda ta ke kula da alamuran shi sosai duk sanda ya je katsina, kai ko gidan shi ya dauko ta tazo hutu to fa tabbas ko Sumayya ba ta kula da lamarin shi kaman ta, ba ta taba barin shi ya zauna da yunwa. Unknowingly ashe shi ne mijin ta. Zai yi kokarin ya koya ma kanshi soyayyarta tunda daman can ya San akwai na yan'uwanta ka sosai, she is special ko a cikin kannen shi in na cire suhaila da suka fito ciki daya. Ya San she lacks nothing sai dai he is afraid to open up for now saboda har ga Allah ya gasu, gasuwan da ba zai yiwu yayi healing da wuri ba. Qur'anic ya karanta hakan ya kasance al'adar shi ce tun zamanin samartakan shi. Addu'oi ya kara musu sannan ya kwanta. Jawo ta yayi jikin shi ya rungume ta ya lullube musu bargon da kyau yana jin wani ni'ima na sauka a kirjin shi. Ya so ya kyale ta amma ina gangar jikin shi da zuciyar sun sha bamban da tunanin shi. Tuni labari ya sha bam bam. Juriyan ta ya matukar burge shi hakan ya sa yayi ta lallabata a hankali har ya samu ta koma bacci.

Asuba ta gari...

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now