Babi na talatin da biyu ( 32 )

1K 93 10
                                    

City hotel G.R.A, Zaria.

Zaune ta ke a daya daga cikin hadaddun kujeru da aka sa a hall in, gefe guda inda is less noisy ta samu ta zauna hade da crossing legs tana sipping chilled shampen in da ke gaban ta. In har ka sa ido akan ta to tabbas ba za ka so daukewa ba sakamakon masifaffen kyau, Kira  da wadatar gashi da Allah ya mata. Sanye ta ke da wani arniyar peach gown da ta wuce mata guiwa da kadan, rigar armless ce amma tana hook wurin wuya, just  picture the lady in half girlfriend on her birthday party. Musamman ta yi ordering irin gown in sak online. Ba shape in jikin ta da bai nuna gashi ta ba za gashi sai kace actress in Indian, tsabagen burge ta da su ke ya sa ta ke ganin su as role models. Wurin ba gabadaya ba Wanda zaka kalla ka raina domin hadaddun guys da babes ne Wanda kudi ke magana a gun su su kayi organizing party in. El-mustapha saurayin Suhaila kusan shine ogan party in da suka shiryawa budurwar abokin shi na kut da kut. invitation na musamman ya aikawa Suhaila da friends inta. Sosai su ka shiryawa party in har saloon su kaje gyaran gashi, pedicure da manicure. Ita kam Suhaila wacce ta wa celebrity kwalliya ita mata nata simple make up in amma duk da haka har celebrity in sai da ta sara mata wurin kyau. Ko dan abin natural ne.

Rawa ake a filin, da celebrants da mutanen ta sauran ko sun riga sun tafi ga duniyan sama ciki har da daya daga cikin friend in Suhailan da ba ta San duniyar da halin da ta ke ciki ba. Su khadija na tsakiyar filin rawa ana damawa dasu ita ko Fatima tuni ta bi wani cikin hotel, daman anan ta fi kauri ita dai kawai taji dumus ne matsalan ta.

Abinda yasa Suhaila ba ta shiga filin rawar ba gani ta ke is too messed for her a ganta a tsakiyan mutane tana rawa. Special dance su kayi ita da El-mustapha tun a farkon event in, daga ita sai shi a filin. Sanin ba za ta koma ba da mutane ya sa bai ma tunkare ta da zancen ba.

"Can i please get the special dance?" Abinda taji an fada kenan, sai dai ko darajar kallo bai samu ba balle ta tanka shi.

Ai ko kafin ta ankara sai jin hannun mutum tayi yana shafa gashin da ta zubo har gadon bayan ta yana fadin "I love this" karan marin da ta sakar mishi ne ya tsayar da duk wani bushasha da ake yi a cikin Hall in. A razane ya dago yana kallon ta sai dai ita ko kara kallon shi ba tayi ba balle  ta ji zafin abinda ta mai. Tunkarar ta yayi gadan gadan yana niyyan fada mata sai dai mutuniyar ko alamun tsoro ba ta nuna ba balle ta gudu.

Karan bindigan da El-mustapha ya harba ne ya tsayar da saurayin, a zafafe El-mustapha ke fadin "don't you dare lay your dirty hands on her if not, I will destroy you" dariyan shu'umanci saurayin ya saki kafin ya fiddo nashi makamin ya harba sama nan da nan kowa ya fara yin ta kanshi. Amma fa banda Suhaila, sai da Khadija ta zo ta ja ta karfin tsiya tana fadin "lafiyan ki? Ba ki tsoro" Jan ta tayi har waje hall in su kayi haraban hotel in.

Tsaki Muhsin ya ja yana hararan Faroukh yace "i told you, kar mu kwana a garin nan kwanan hotel ba namu bane ka ki ji ji abinda ke faruwa a hotel in, kara bindigogi na ke ji, ga mutane na gudun tsira yanzu za kaga hukuma sun zo nan, me aka yi kenan" ya fada yana reverse da motan yace "ba zan kwana ba Faroukh in ka matsa mu canja hotel in" karan da yaji ne ya sa shi tsayawa da sauri ya fita bayan motan yana ganin wanene ya shigo mishi bai lura ba. Zamu iya cewa dishi dishi Muhsin ya koma ganin sakamakon abinda ke mishi gizo a gaban shi, ji yayi wani jiri na neman zubda shi kasa yayi saurin dafe motan. Four eyes su kayi da Khadija da Suhaila suna nishi. Kallon mamaki me ya kawo shi nan Suhaila ke bin shi dashi cike da bakin ciki don ta san yau mai raba su sai Allah kuma dan Ko Abbah bai da daman nan. Kallon takaici ya bisu dashi suna neman wuce shi bai yi wani tunani ba ya fisgi hannun Suhaila ya wulla a bayan motar shi hade da zuba mata marin da sai da ta kusan shidewa, gudun abinda zai faru yasa ba tayi nacin fita motan ba a lokacin. sai lokacin Faroukh ya gane mai ke faruwa. Ko kafin Faroukh in ya fadi wani abu Muhsin ya fara tada motan idanun shi sun yi ja da kyar ya ke kallon gaban shi. Da kyar Faroukh ya shawo kanshi ya amshi tukin. Suna isa gadar kwangila Suhaila ta fara kokarin fita daga motan kallon da Muhsin ya mata yana huci ya sa ta koma ta kwanta.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now