Babi na hamsin ( 50 )

1K 88 7
                                    

Meema kam ba ta samu zuwa Kadunan ba dole sai suna. Wata patient Dr Aliyu ya hada ta da ita ta dinga kula da ita. A cewar shi cousin in shi ce. So aiki biyu ya hade Mata gashi shi ba zuwa asibitin ya ke ba sai akai akai. Da yazo zai sa a Kira tana yana inquiring akan patient in tashi. A hankali hiran ya fara tashi daga kan patient ya fara koma personal. Sai dai ga dukkan Alamun meema ba ta son hakan domin kaucewa ta ke.

"Ke yar jigawa ce kenan?" Nodding Kai ta mishi kawai

"Amma a can kuke zama ne?"

"A Abuja" ta bashi amsa Kai tsaye.

"Au kice can zanje inga baba kenan?" Ya tmby hade da kafa Mata idanu. Hade rai tayi tace "sorry sir akwai patient in da zan duba a ward, can i go"

"Okay then i will call you later, I need to talk to you. If it okay ma I may need to visit your dormitory tomorrow"

"Ehmm sorry sir am traveling to kaduna tomorrow"

Kallon ta ya danyi yana kokarin karantan fuskan ta "shknn in kin dawo we will talk"

...

Satin haihun Fadila na zagayo wa aka yi sunna. Kai tsaye Najib yace shi burin shi ya sa wa yarshi suna Aisha tun tuni don haka mama Aisha zai ma mai suna. Aiko tuni yarinya ta amsa suna Aisha ana ma ta lakabi da Humaira. Yan katsin da yawa sun zo haka yan Kano da Abuja. Mai jego da baby kam sunyi goshi sai San barka. Asmau kaman tayi tsuntsuwa ta zo haka ta dinga ji Amma ba dama sai dai kam an Sha video call kala kala. Sosai tayi farin cikin sunan da ya Najib yasa Amma tace wa Fadila "maimakon ki ce a sa mana Ummi sai kice a sa mama, haka ake yi?"

"Naga ai kina da numban Yaya Najib in. Ita kanta Ummin ta yi farin cikin balle ke mai uwa" dariya tayi tace "shknn a gaida mana maman mu sannan kice wa Yaya Najib na gano shi wato dan mama ta mishi bikon matar shi shine..."

Katse ta Fadila tayi da cewa "Ni dai wlh babu ruwa na ba zan fada ba. You can call him" dariya tayi bayan ta ajiye wayan tana kallon mukhtar tace "Ya Mk kana jinmu da Faddi?"

Yace "to ya zaki yi? Struggle in kina son Ummin ki haifo ta da kanki"

Hararan shi tayi tace "sai kace a hannu na abin yake"

"Oh afuwan a hannuna ya ke ashe? To zo muje in baki" zille wa tayi ya bita da gudu...

....
Muhsin ya maida su Zaria su uku. Meema, Suhaila da kuma matar shi Rahma. Through out the journey hiran su su ke yi sai dai su kan sako su a ciki, meema kawai ke sa musu baki. Mutuniyar tashi ko kaman mai bacci haka tayi likimo tana sauraron su.

Rahma ce ke tmbyn Meema "suhaila bacci tayi ne? Na ji ta shiru" meema da ta dago abinda ke faruwa cewa tayi "kinsan Suhaila da rashin son hayaniya  yanzu haka kan ta ke ciwo"

Caraf Muhsin yace "kuma ba ta Sha magani ba" girgiza Kai meema tayi tace "may be inta tashi ya tafi ai"

Shiru su kayi su ka koma wani hiran. Sai dai cikin ranshi dankare ya ke da damuwa. He is feed up with his feelings towards her don haka if is not going to  work he ought to end everything between them ko ya samu mind in shi ya zama at ease.

Ranar da dare ya Kira ta ya sanar da ita zuwan shi. Da ke she is feeling some how ranar dogon hijab in ta kawai ta sa kan kayan da ke jikin ta ta nufi wajen. Kallo daya ta mai ta San something is not normal.

"Ya ciwon kan ya tafi?" Ya fada bayan sun gaisa.

"Na warke"

Nodding kanshi yayi, ya dauka wasu manyan littatafai ya mika Mata. "Ga waddannan ki kara da sauran littatafan ki"

Amsa tayi tace "nagode sosai"

"Ba wani matsala ko? Game da karatu"

Girgiza Kai tayi tace "I think everything is normal"

"Great, we have learnt a lot. Munyi nisa sosai ko ba haka ba?"

"Hakane" ta amsa tana mamakin canjawan shi a yau.

"Then Ina ga zamu tsaya a haka, duk abinda baki gane ba ga littatafan Nan da wancan su zama guide" gabadaya jikin ta sanyi yayi at his words, she can't believes he is telling her this. Amma bakomai bai San da wa ya ke dealing bane.

"Ai hakan ma nagode sosai, Allah ya saka da alheri" duk da shi ya kawo idea in tsayawa da karatun, sai yaji wani iri da amsan ta. At least he expects her to put up some fight ko yayane.

Bai gama tunani ba sai ji yayi tana fadin "Nagode, bara na shiga ciki, sai da safe" tana maganan ta na bude kofa. Har ta isa ko waiwayo wa ba tayi ta dube shi ba. Ya Kai mintuna a wurin ya kasa tafiya yana mamakin daman duk wani abu da ya ke tunanin tana having akan shi misunderstanding ne kenan? He don't want to believe it even though it so obvious.

To ga Suhailan ma hakan ne ya kasance. Taurin rai irin na ta be kadai ya hana ta kuka. Shin ya za tayi da rayuwar ta akan Muhsin ne? When she thought she can't have him yazo ya shigar da kanshi a rayuwar ta. Ya sa tayi mugun sabo dashi yanzu kuma zai zo Mata da maganan Nan.

Duk wani ways da ta ke ganin zai jawo attention in shi gare ta tabi dama duk shawarwarin da Yan uwan ta su ka bata. Ta nuna mishi caring, haka kuma har interest ta nuna mishi a fakaice kaman yanda shi ma ya ke Mata. Abu daya ne ba za tayi ba shi ne confessing to him. She respect herself so much not to do that. In ko haka ne to za tayi kokarin sa wa kanta rabuwa da Muhsin da soyayyan shi da ke addaban rayuwan ta.

Ranar dai kusan kwana su kayi dukkan su ba su yi bacci kowa da dawainiyar da ya ke fama dashi. Shi Muhsin tsoron shi daya kar ta turo mahmud wurin Abbah kaman yanda ya fada ma ta kuma ta nuna amincewan ta da hakan.

Ba su yadda abin da gaske bane sai da su ka kwashe kwana biyu ba wani abu da ya shiga tsakanin su. Wannan kwana biyun jin ta su kayi kaman shekara. Ita Suhaila Alkawari ta daukan wa kanta ba zata taba neman shi ba sai in har shi ya neme ta. Shi kuma yana expecting ko Yaya ne ta neme shi ta hakan zai gane tana da interest komin ko kankan tar shi. Amma shiru kake ji no action is taken.

ABINDA KAKE SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora