ADYAN 01

254 6 3
                                    

ADYAN

Na AUNTY HALILOSS

Whattpad@AuntyHaliloss

Littafina na kuɗi ne,kada ku fara karantawa ku daina ganin shi kuce sai da na ga ana neman shi na mayar dashi na kuɗi,masu buƙatar saye kuyi man magana ta a WhatsApp @09039080909.

Ƙirƙirarran labari ne banyi shi dan wani ko wata ba,idan anyi katari yayi dai-dai da labarin rayuwar wani akasi aka samu.

Yabo da godiya ga Allah da ya bani idon farawa lafiya,Allah ka bani ikon gamawa lafiya,kasa mu amfana Ameen.

Bismillahir Rahmanir Rahim

Free page. 01

Zaune ya ke saman wasu maka-makan kujeru da su ka ƙara ƙawata falon,kyakykyawan saurayi ne da shekarun ba zasu gaza shekaru talatin da ɗaya zuwa da biyu ba,sanye ya ke da riga da wando na wani fakistan launin ruwan madara sai ƙaramar rigar saman wato falmara kalar ja,ga wasu takalmi dake ƙafarshi na fata.

Farin gilashin idon shi ya ƙara fito da tsinin hancin shi,saurayin ya na da kyau sosai,wayar hannun shi ya ke dannawa ga duk kan alama chating ya ke yi.

Ya jima a wajan zaune sai dai shi ɗaya ne a falon,wata mata ce ta fara saukowa daga matattakalar benan dake can gefen falon,babbar mace ce sosai tasha wani ɗanyan leshe da kayan ado a wuyan ta da hannuwan ta,wato sarƙa da ƴan hannu.

Hango saurayin da tayi yasa ta saurin ɗaure fuska tana sauko ta nufo wajan da ya ke,tare da ɗaga murya tana kiran "Musa Musa Musa!!!"

Jin miryarta ya sa shi saurin ɗagowa yana gyara zaman shi tare da faɗin"sannu Mama"

Wata harara ta jefeshi da ita,dai-dai lokacin wanda aka kira da Musa ya shigo falon da sauri yana faɗin"Hajiya ga ni"

"wato kana ji ina kiranka ba zaka iya amsawa ba,har sai kazo nan zaka ishe ni da Hajiya ga ni" tana maganar tana kwaikwayon muryar shi.

"yi hakuri Haji..."

"ni dalla kauda man shi daga nan falon baƙi zanyi suna gab da zuwa"

Musa ya juya ya kalli Adyan daya kauda waya yana kallon Matar, sai dai daka gani zaka gane bai ji daɗin maganar matar ba"Adyan ina zaka zauna? "

" wato saima ka tambaye shi ko? "

Adyan ya kalli Musa yace"ka kaini baya zan sha isaka"

Wata dariya matar ta sauke ta matsa wajan shi"kai nan har iska kake son sha? "

Saurin kauda kai Adyan yayi yana ɗan ƙebta idanuwa saboda yadda yake jin ciwo a zuciyar shi,Musa ya turo wani keken guragu keken yana da kyau sosai na farar azurfa ne,yana tsayawa wajan Adyan,Adyan ya aje waya gefe,ya miƙawa Musa Hannu alamar ya ɗora shi sama kujerar.

Musa ya kama hannun Adyan yana taimaka mashi dan zama saman kujerar guragun,ya na zama Musa ya ɗauki wayar shi yana bashi,ya koma bayan keken yana tura shi.

Wani filin shaƙatawa dake gidan ya kai shi kusa da swiming pool,ya jawo wata kujera shima ya zauna,Adyan yace"Musa na gode idan aiki kake kaje ka ci gaba. "

Sosai Musa ya gane damuwar dake tare da uban gidan na shi,hakan yasa ya fara dariya ya na faɗin "Abin so na ne Yaron Baba"yana maganar kamar yana yin waƙa.

Adyan ya fara dariya yana kauda damuwar shi dan babu abinda ke mashi daɗi irin a maimaita mashi maganar mahaifin shi"ka ga yau Baba bai dawo da wuri ba"

"nasan aiki ne yayi mashi yawa"

Adyan ya jawo wayar shi"bari in kira shi"

Ya na maganar ya na danna lambar Baban na shi"Hello Baba"

ADYAN Where stories live. Discover now