ADYAN 04

55 4 0
                                    

*ADYAN*

    NA AUNTY HALILOSS

Whattpad@AuntyHaliloss

*LITTAFIN ADYAN NA KUƊI NE MASU BUƘATAR SAYE ZASU MAN MAGANA A 09039080909.*

*Dedicated to Aunty Zahra Maman Mus'ab*

*FREE PAGE 04*

Cikin zafin nama Salim yayi kan Aleesha yana ɗaga hannu dan dukan ta Mutanan wajan suka riƙe shi dai-dai lokacin da Baba yake mashi tsawa,Salim ya ture wanda ya riƙe shi Baba yayi saurin riƙe shi Salim ya fizge hakan ya ƙara harzuƙa Baba ya ɗaga hannu ya na ƙara sauke ma shi wasu marurrukan.

Salim ya riƙe kunci ya na zare ido Baba ya fara magana"sai na ɓata maka rai kuma gata nan ka taɓata ka gani"

Mutanan wajan  suka fara maganar abinda Salim yayi dan basu san cewar yaran Baba bane,Baba ya juya ya kalli Aleesha "kin man dai-dai" yana maganar ya na murmushi, ya juya wajan Salim"to ka gani abinda nake gaya maka,abinda kake ba abu mai kyau bane,yanzu ina ranar rashin kuny.... "

" Baba marina fa tayi, ai wallahi bazan yarda ba"yana maganar ya na matsawa,Baba ya nuna mashi ƙofa"maza fice man da gani"

Salim ya san halin Baba sarai,sai dai tun da ya ke ba'a taɓa yi ma shi wulaƙanci irin wannan ba,yarinya ta mareshi sannan kuma budurwar ba wata mai ajiba,asalima aikin da take ba wani bane.

Kan motar shi ya buga yana dafe kan shi,wasu hawaye suke zubo mashi,yasa hannu ya goge yana nufa hanyar komawa, tuno mahaifin shi na ciki yasa shi buɗe mota ya shige.

Gida kawai ya wuce cikin babban falon gidan ya tadda Zinnira da Fa'iza,wasu glass ne na decoration ya ringa jefarwa ya na watsi da kayan falon.

Duka suka miƙe suna tambayar shi lafiya suna riƙe shi"wallahi bazan yarda ba,kwata kwata Baba baya sona, wallahi ni zan iya kashe ta"

Zaro ido sukayi"wai miye Brother? "

" Marina tayi zan rama Baba ya ƙaraman taya"

Yana maganar ya na ƙara zabura,Zinira ta tambaye shi dan abin ya ɓata ranta, labari ya basu yadda aka yi,wani zagi Fa'iza tayi"sakatariya kuma"

Zinira ta sa hannu ta bugi centre table ɗin falon take ya fashe a wajan"kwantar da hankalin wallahi zai ta gane kuranta, sai mun ɗau fansa"

"ku barni da ita ni zan horar da ita"

Fa'iza ta juya tana kwalla kira Mama,Zinira tace" Mama ta fita"

"wallahi shima Baban sai mun ɓata ran shi"

Zinira tace"Adyan kawai zamu taɓa ran shi ya ɓa ci"

Salim yayi kwafa yana wucewa.

Ɓangaran su Aleesha kuwa tun da ta san cewar zuciyar ta ta aikata abinda take buƙata hakan yasa ta juya tana sauke ajiyar zuciya dan bata san doguwar magana kuma.

Baba ya juya yana ba mutanan wajan haƙuri,Engr. ya kalli su Aunty yace"shikenan Kuci gaba da aikin ku"

Sannan yaba masu jiran shi hakuri.
Ita dai Aleesha dama ta koma mazauninta Baba ya juya suka shiga ciki Matar dake wajan tace"ke amma yarinyar nan kin burgeni haka kawai yaro yazo yana rashin kunya"

Aleesha ta ɗanyi murmushi kawai,Aunty tace"yaran ne baiyo halin mahaifin shi ba"

Ta kalli Aleesha dake latsa waya lokacin idan uwanta sun rage ja,ta anshe wayar"wai kinsan abinda kikayi kuwa? "

" nasani mana"

"kinsan waye Baban shi k..."

Aleesha ta katse mata zancan ta hanyar ɗaga mata hannu"koma waye wallahi zan bashi girman shi, shi yaran baiga abinda ya aika ta ba,wannan dake jira ai duk sun haife shi,taya zai aikata abinda yayi,Babban baƙin ciki na zagin Babana da yayi haka kawai yana cikin kabarin shi, ni ban haɗa iyayena da kowa ba"

ADYAN Where stories live. Discover now