ADYAN 05

66 3 2
                                    

*ADYAN*

    NA AUNTY HALILOSS

Whattpad@AuntyHaliloss

*LITTAFIN ADYAN NA KUƊI NE MASU BUƘATAR SAYE ZASU MAN MAGANA A 09039080909.*

*Dedicated to Aunty Zahra Maman Mus'ab*

*FREE PAGE 05*

Ƙasa ta faɗi ta na Salati ta yi sauri ta na miƙewa sai dai ta kasa saboda yadda ƙafarta ta riƙe dan haka ta ja jiki ta koma gefen ti-ti dai-dai lokacin da Salim ya fito daga mota ya na dariya.

Aleesha ta zaro ido ta na waigawa sai dai babu mutane unguwai tsoro ya kama ta sosai, Salim ya duƙo ya na dariyar mugunta "wato ki na ganin kin mari Salim kin mari banza ko?"

Aleesha ta yi ƙoƙari ta yi saurin miƙewa tare da nuna ƙarfin hali sai dai ƙafar dakyal ta aje ta ƙasa,Salim ya na nuna ta da yatsa ta sa hannu ta aje mashi Hannu ƙasa"kai wane irin mutun ne wai? tabbas kai dabba ne cikin dabbobin ma wanda basu da....."

"keeee kar ki..."

Duƙawa Aleesha tayi ta ɗauki jakarta ta ɗangisa ta na komawa ta ƙetare cikin sauri ta koma layin gidan su dan ba ta san Salim ya ɓata mata rai zafi ƙafar ke yi mata dan haka ta samu ta isa gidan.

A bakin ƙofa ta samu Ya Mus'ab ya fito za ya wajan sana'ar shi, cikin sauri ya nufe ta "ke lafiyar ki kuwa"

"wallahi Yaya abin hawa ya ture ni" ta na magana tana ɗaga siket ɗinta sai lokacin taga yadda duk ta gurje guiwa"to wuce muje chamists ai kinji rauni"

Aleesha ta bishi ya na riƙe hannun ta, sai dai basu samu mai chamists ɗin ba saboda safiya ce,dole suka dawo gida, hankalin Mama tashi da taga Aleesha, haka ta yi ta tambayar ta Aleesha ta yi ta bada labarin ƙarya hada cewa ita tace wanda ya tureta ya tafi, dan tabbas bata so su Inna suji.

Sai da Ya Abdullahi ya shigo gidan ya tadda ta zaune ta miƙe ƙafa ga ƙafa harta kumbura"wai garin ya kika ji ciwo"

Inna ta ba shi labari kamar yadda Aleesha ta faɗi mata"to kuma sai ayi ta zama ƙilama tayi targaɗe tashi muje ayi ma ki kamu"

Dole Aleesha ta tashi suna zuwa mai ɗorin yace tsagewar ƙashi ce,haka aka yi mata kamu aka daure ƙafar,suka biyo ta chamists akayi mata aikin inda ta guggurje tare da bata magunguna.

Lokacin data dawo ta samu miss call a wayar ta,ta gyara zama"Mama baki ji wayata ta yi ƙara ba? "

" ina naji, wayar da kuke rufe sauti,sai ku kaɗai kuke sani idan an kira ku"

Aleesha ta yi murmushi tana danna kiran Engr. Dan ta san ya ga ba ta zo ba ne  ya kira ta,ya na ɗauka ta ke sheda mashi ta na hanyar zuwa mota ta tureta amma da sauƙi, sannu yayi mata tare da fatan samun sauƙi,Aleesha tace"nagode sosai"

"to shi kenan zan turo a duba ki,sannan na baki hutu zuwa ki warke"

Aleesha taji daɗi sosai tayi mashi godiya,ta juyo ta kalli Inna tace"Inna yace ya bani hutu zuwa in warke"

Dariya Inna tayi"ai hutu dole ne,tun da dai ba zaki iya zuwa da wannan ƙafar ba"

Aleesha za ta yi magana sai suka ji sallama Hindu ƙawarta,Hindu ta iso ta na zare idu"wai ashe ciwo sosai? na fito ɗazu naji ana faɗi a unguwa an banke ki"

"bari ke dai gani nan zaune"

Hindu ta zauna gefenta"Allah ya sawake"ta juya "Inna ina yini"

"a'a gama gaida ƙawar taki"

Dariya suka yi Inna ta miƙe dan tafiya ɗora sanwa,Aleesha tace"ke matso kiji wallahi abin ɗan iskan yaran nan ya ishe ni"

"wane yaro kenan"

ADYAN Where stories live. Discover now