ADYAN 03

64 7 3
                                    

*ADYAN*

Na AUNTY HALILOSS

Whattpad@AuntyHaliloss

*Masu buƙatar sayan littafin ADYAN su neme ni a 09039080909.*

*FREE PAGE 03*

Da sauri Baba ya isa wajan yana ƙoƙarin ɗauke kujerar daga kan Adyan,ya ɗaga shi yana mai dashi kan keken na shi,Aliya kuma ta kasa miƙewa,Adyan ya ɗan duƙa ya kama hannun ta,ya na ɗaga ta.

Baba ya kaɗa kai yana nuna Mama da yatsa sai dai wannan lokacin hawaye ne a idon shi"kin hanaman kwanciyar hankalin gida,taya zaki turasu,yanzu idan suka ji ciwo fa"

Fuuuu tayi ta bi hanyar shigewa,Baba ya juyo yana kallon Adyan da yake duba guiwar hannun shi da ya gurje,Adyan ya ɗago yana kallon mahaifin shi,sosai ya shiga damuwa ya sa hannu yaja kujerar shi ya isa wajan Baban ya riƙo ahi"Haba Baba ka daina kuka dan Allah"sai dai shima ɗin hawayene fal idon shi.

Aliya ta kama hannun Baban ita ma,hannu yasa su duka yana azasu saman jikin shi,Adyan ya cire farin gilashin idon shi yasa hannu yana goge hawaye,Baba ya ɗaga Aliya ya na kallon ta"ka da ki yi Halin Maman ki Ƴata"

"Mama bata da tausayi..." Adyan ya rufe mata baki"kada ki fara kalamai mara daɗi akan ta Aliya ke ƴa ce"

Ya na maganar yana rushewa da kuka"da yawa masu shekaru kamar nawa suna harkokin su, saboda suna da ƙafa,nifa Baba Kaga inada ƙafa sai dai batamin amfani a yanzu, inda ina fita nasan ba ko yaushe Mama zata ganni taman wani abin ba"

Kwata-kwata Baba baya iya magana dan yadda yake jin ɗaci a zuciyar shi,sumar kan Adyan yake shafawa,Aliya tasa hannu tana goge mashi hawaye,Adyan ya riƙe hannunta"Nagode sosai Sister"

Baba ya koma bayan kujerar yana tura shi zuwa falo.

            ****
Aleesha tana zaune Office ɗin ta wanda itace sakatariyar wani ma'aikacin kwamnati, duk wanda zai ga Ogan nata to tabbas sai ya gan ta,itace zata baka damar hakan saidai idan dama ka shirya tun kafin zuwan naka.

Office ɗin ciki da falo ne can cikin ne Ogan ya ke ita kuma tana farko, yau babu mutane sosai hakan yasa ta ɗan kishin giɗa saman table ɗin tana hutawa.

Musa ne ya kai Baba wajan dan zaiyi meeting da Ogan Aleesha,Musa ya buɗewa Baba ƙofar Office ɗin, suka shiga, jin motsi Aleesha ta ɗago,lokacin data ga mai shigowa hakan yasa ta miƙe tsaye tana faɗin"Sannu da zuwa"

Baba ya kalle ta yana nazarin ganin baƙuwar fuska"ina sakatariyar take"

Sakin fuska tayi tare da faɗin"Ta koma wani ɓangaran ni ce ana yanzu"

"OK Allah yabada sa'a, inasan ganin Egr. ne"

Aleesha ta koma wajan wasu takardu ta buɗe wani file ta jima tana dubawa ta ɗago"Alhaji sai dai babu Apointment na zaka yi magana dashi"tana maganar cikin girmamawa.

Ya ɗago ya kalle ta ya koma kan wata kujera ya zauna"ok bari in kira shi"

"to" tace kafin ta koma tana zama saman kujerar ta.

Ya yi wayar babu jimawa wata na'ura tayi ƙara, Aleesha ta miƙe ta shiga Office ɗin ba'a jima ba ta fito tana sakin fuska"zaka iya shiga Yallabai"

Baba ya miƙe yana murmushi"to nagode"

Aleesha ta koma ta zauna,ta jawo wayar ta tana danna game.

Ƙarfe Ukku ta ta tashi hakan yasa ta isa gida da wuri,Budaya ta tadda tana jan ruwa a rijiya,Aleesha ta kalle ta tana faɗin"yau baki je makaranta ba"

"Aunty Aleesha kinsan fa nace ciwan kai nake" Aleesha ta jinjina kai,ta shiga ɗakinsu anan ta tadda Inna zaune,sai dai tayi shiru kamar mara lafiya.

ADYAN Where stories live. Discover now