ADYAN 06

44 2 0
                                    

*ADYAN*

    NA AUNTY HALILOSS

Whattpad@AuntyHaliloss

*LITTAFIN ADYAN NA KUƊI NE MASU BUƘATAR SAYE ZASU MAN MAGANA A 09039080909.*

*FREE PAGES NE NI KE BA KU DA NA GAMA FREE PAGES BA ZA KU CIGABA DA KARANTA LITTAFIN ADYAN BA SAI WANDA SUKA BIYA KUƊI*

*MA SU TAMBAYA AKAN NA FARA SAIDA LITTAFIN ADYAN ƊIN,EH NA FARA SAIDAWA.*

*Dedicated to Aunty Zahra Maman Mus'ab*

*FREE PAGE 06*

Aleesha ta dawo cikin gidan cikin jin daɗi sai dai kuma ta cika da mamakin yadda aka yi Alhaji Husain ya san gidan su har ya yi ma su wannan abin arziƙin.

Tsaye ta tadda Ya Abdullahi ta kalle shi ta ce"Yaya wai ina ka gan shi ya aka yi har ya biya kuɗin? "

"wallahi kuwa ya ce ya zo ganin ki ne an ce mashi ba ki da lafiya ne"

Aleesha ta jinjina kai"Allah sarki amma gaskiya mun gode, in da bai zo ba da bamu san kalar wulaƙancin da zamu sha ba"

Inna tace"Allah kenan shi ne ya warware mana abin cikin sauƙi"

Abdullahi ya fara tafiya"Bari in je in yi wa Mustafa godiya har dubu biyu ya ba da amma mutumin nan bai kalle mu ba"

Mus'ab ya miƙawa Budaya jikka akan ta kai ɗaki ya dawo ya na faɗin"ai shi ma Alhajin sai an yi ma shi godiya"

"nayi mashi sai dai ita Aleesha ɗin idan ta koma aiki sai ta yi ma shi godiya ɗin"

Inna tace"ya na da kirki gaskiya ga ya ya zo dan ganin ta kuma bai samu ganin ta ba"

"ai kwata-kwata bai ji daɗin abin da ya gani ba shi ya sa bai tsaya ba yana biyan kuɗin ya tafi,ga alama baiso hakan ba"

Aleesha tayi shiru,sai dai ta na tunanin yadda mutumin ya kasance mai kirki haka amma bai yi sa'ar ɗa ba saboda abinda Salim ya ke aika tawa baiyo halin Baban shi ba.

            *****
Shi kuwa Baba ya na tafiya a mota tunani fal zuciyar shi dan sam ba ya san ya ga ana wulaƙanta talaka musamman waɗan da ya sani,balle kuma Aleesha da ya ke ganin mutuncin ta gata da ladabi wajan yi wa manya magana ga sanin ya kama ta,yarinyar ya na ganin tarbiyar ta sosai.

Gidan ya nufa ta gate ɗin baya ya shiga sai dai ya hango yaran gidan da Maman su a zaune wajan shaƙatawa.

Aliya ce ta miƙe dai-dai lokacin da ya yi parking ya na fitowa"welcom Baba"

Ɗan yaƙe yayi ya kama hannun ta suna komawa wajan su Mama,zaune su ke da lemuna suna sha har da Salim wanda shi ma bai jima da shigowa gidan ba,kan Zinira ya dafa tare da faɗin"ina kallabi? "

Turo baki tayi" nauyi yake man ni ban fito da shi ba"

"maza je ki ɗauko shi"

Mama ta taɓe baki,Aliya ta zauna tare da faɗin"ga kujera Baba"

"ina Adi kuke zaune ku kaɗai"

"to ya na ciki ai sai da aka ce ya fito ya ƙi fitowa tambaya ta me kuma?"

Aliya ta kalli Maman tuno ko kallon Adyan ɗin ba ta yi ba lokacin fitowar su,itace ma ta ce mashi ya zo su fita yace ba ya jin zai fita,dan ya na gudun zaman su inuwa ɗaya da su.

Baba bai zauna ba ya yi hanyar ciki,Aliya za ta bi shi Mama ta zaunar da ita kan kujera.

Adyan ya na zaune ya na danna waya,Baba ya yi sallama amsawa ya yi yana sauke wayar, tare da murmushi Baba ya nufo shi sai dai yau fuskar shi babu alamar murmushin da ya saba yi ma shi.

ADYAN Where stories live. Discover now