ADYAN 07

113 7 2
                                    

*ADYAN*

    NA AUNTY HALILOSS

Whattpad@AuntyHaliloss

*LITTAFIN ADYAN NA KUƊI NE MASU BUƘATAR SAYE ZASU MAN MAGANA A 09039080909.*

*Dedicated to Aunty Zahra Maman Mus'ab*

*FREE PAGE 07*

Ƙarfe Huɗu  saura Aleesha ta iso gidan sai dai ta samu Inna ta na sallah dan haka ta aje jaka da mayafinta ta fito domin yin Alwala sai da ta koma ɗakin ta kabbara Sallah itama sai ga Mus'ab ya shigo Lokacin Inna ta gama ta ta sallai dan haka suka cigaba da fira. Inna har ƙagara ta yi Aleesha ta idar dan ta yi mata albishir aikam ta na gamawa Inna ta miƙa hannun ta kan gado ta fiddo takarda ta ba Aleesha sai da ta Haɗa da tambaya kafin ta gane  abinda takara dar ta ƙunsa Murna ta hauyi tana rungume inna tare da tambaya"inna sunan ki ne a jiki fa?"

" tabbas Aleesha suna na ne, sannan kuma Alhajin da ya biya mana haya shi ne ya bamu gidan"

Arazane ta cigaba da yi wa Inna tambayoyi sai dai Inna ta kwantar mata da hankali akan har gida ya shigo su ka yi magana dashi Aleesha yanzu kam ta rasa wane kalar kirki ne ga Alhaji Husain ba ta san lokacin da ta fara kuka ba dan taimakon da ya yi ma su.

Aleesha tace"Inna tun da na ke ban taɓa ganin mai kirki irin shi ba"

Har dare gaba ɗayan su suka haɗu Budaya da Aleesha sun kasa ɓoye farin cikin su Abdullahi yace"gaskiya dole zamu je muyi mashi godiya"

Inna tace"dole kam inma bakuje ba ai baku kyauta ba"

Aleesha ta jinjina kai"ya Allah kayi mashi sakaya da mafificin alkhairi"

"Ameen ya Allah"

A ranar kamar ba za su yi bacci ba dan daɗi Aleesha ta so kira sai dai tana tsoran kada wani ya ɗauka ba shi ba,sai dai Inna ta matsa ma ta akan kiran ita kam ta fara tunanin dole zata jira yazo Office ɗinsu tayi mashi godiya,ganin Inna ta nace hakan yasa Aleesha tace dare yayi sai dai zuwa safe.

Da safe Aleesha ta na ta shiri Inna ta shigo ɗakin"Aleesha kin kira shi kuwa? "

" a' a Inna da wannan safiyar duka yanzu takwas da ƴan mintoci"

"ke ina ruwan ki da safiyar ai ƙara ki kira da Ace baki kira ba" Aleesha ta jawo waya Inna tace"ina kika aje kalaci? "

" ya na nan cikin kula na juye"

Dai dai lokacin take danna waya,lokacin Baba yana tare da Adyan suna kalaci a baki ya ke ba shi falfesun dan kalin turawa wanda aka haɗa shi hanta.

Adyan ya janye Bakin shi"Baba kaima kaci ka ga ka na ƙara makara"

"ba ni da wasu Abubuwa sosai yau dan haka idan na dawo da wuri ma fita zamuyi da ku"

Adyan ya ɗauki lemun farm dake kan table ɗin gaban shi ya kurɓa tare da faɗin"ban dani za ku dan zamu fita da Musa ne"

Baba ya jinjina kai"ina za ka? "

" gidan Baba Engr. Da na yi wa alƙawarin zuwa"

Baba zai yi magana wayar shi tayi ƙara ya juya yana dubawa sai ya ga baƙuwar lamba kamar ka da ya ɗauka sai kuma ya ɗauka.

"Hello"

Aleesha tayi shiru dan tana san tantance mai maganar Jin shiru Baba yace"Assalamu Alaikum"

"Amin wa alaikumusslam Ina kwana?"

"lafiya lau dawa nake magana?" sosai Aleesha ta gane shi ne ke magana dan haka tace"am dama Aleesha ce"

Sakin fuska Baba yayi ya gyara zama yana kallon Adyan dake gyra agogon hannun shi yace"Allah sarki ɗiyata ce kenan ya gida? "

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 27, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ADYAN Where stories live. Discover now