Roman18 [XVIII]

795 76 4
                                    

🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘

         💥 *Fiction Story* 💥

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

           '''🎐G•W•A🎐'''

*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*_By Miss Xerks_*🌺
*_Wattpad@ OUM-RAMADHAN1433._*

*_Dedicated to my Masoyiya_*
*_Ummu Nabil💖_*

~Al-wαhhαв- thє вєѕtσwєr.~

'''①6/11/②0①9••⏰20:00pm.'''

~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~


*🤔NIKO KU TAIMAKA KU ƘYALE MIN NABILA TAH HAKA KARKU CINYETA ƊANYA😂*

                       *Ꮢ-XVIII*

*__________📖* sakinta Anty tayi cikin ɗimauta take tambayarta da rawar murya,

"kika ce mene? ya cuceki fa kike cewa Nabila, yanzu shikenan kina so kice min yayi nasarar rabaki da budurcinki?"

saita zube ƙasa tasa ihu tare da ɗora hannu aka, "shikenan na shiga uku na lalace, na shiga uku ni Hansa'u, ƴa ɗaya tilo da Allah ya bani yau an samin ke acikin musiba, Nabila wazai aureki? Allah ka tsinewa wannan bawa naka"

Mama Samira,Gwaggo Amina dasu Maimuna ne suma suka shigo a wannan lokaci hankula a tashe duk sukai kanta.

Maimuna na zuwa ta rungumeta tsam tamkar uwar dake shirin maida ɗiya ciki tana, "Lovly tah"

"na'am Lovly"
tai maganar tana jan majina a hanci.

tambayar da kowa ke jero mata shine ya lafiyar jikinta take, ita kam ta kasa basu amsa ita da Anty sai kuka suke.

Kakus ta shigo, kai tsaye wurinta ta nufa ta kamo hannunta ta miƙe tsaye, kallonta take daga sama har ƙasa kamin tace da ita, "miya haɗaki da ƴan iska har suka sace ki suka zubar maki da mutunci?"

bata iya magana ba Kakus taja hannunta ta damƙawa Anty, "Hansa'u ki ƙara bincika min ita yanzun nan, ba kuma naso ki munafurce ni, in har kikai hakan Allah ya isa tsakanina dake kuma kisani sai Allah yay mana hisabi"

ta juya gasu Gwaggo Amina dake tsaye dasu Mama Samira tace, "ku fita daga waje"

kowa ya fice ya rage daga Anty sai Kakus sai Nabila.

Anty tace da Kakus, "ina da buƙatar kayan aiki kamin aiwatar da komi"

dake itama Anty RN ce.

Kakus ta amsa mata da, "to" sannan ta fita tasa Munir ya kira mata Nabil.

yana zaune a office ɗin Dr Affan yay jugum kai daka gansa kaga mutumin dake ɗauke da tsantsar damuwa, magana Munir yay ta masa amma sam bai jisa ba har saida ya taɓasa tukunna ya dawo hayyacinsa.

"bai kamata ace kana sawa kanka wata damuwa ba Conel, ka bata lokaci ƙila halin data shiga yasa ta kasa fahimtarka"

zamansa akan kujerar ya gyatta yace dashi, "Hmmm bana tinanin Nabila zata sauya Munir, anyway ya akai?"

"ehhh Kakarta tace dama ai mata magana da kai yanzu kaje"

da faɗuwar gaba ya miƙe ya fita, saida ya fara knocking ƙofar Kakus tace ,"bismillah" sannan ya buɗa ya shiga.

KULLU NAFSIN Completed.Where stories live. Discover now