Roman25 [XXV]

629 61 5
                                    

🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘
       *1441H/2019M.*

     💥 *FICTION STORY.* 💥

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

            '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼_*

*BY MISS XERKS✍🏼.*
*WATTPAD@ OUM-RAMADHAN1433.*

*DEDICATED TO UMMU NABIL.*

*IN THE HONOUR OF:-*
*{ANTY NICE & BINTA G. DAUDAWA.}*

*[SPECIAL GIFT TO MAMAN JIDDA & MRS KHALEED.]*

~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~

*~AR-RAFI'I:-THE EXALTER.~*


                     *Ꮢ-XXV*
                          *25*

*__________📖* "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".

Suhail ya karantota cikin tashin hankali yana mai kallon Mami.

wani kallo ta watsa masa na shashasha kawai kana tace, "yauwa ƙara karanto wa tinda gani annoba a gabanka, ina neman hanaka yin rawar gaban hantsi ko".

"ke!".
Mami ta kuma daka mata tsawa.

nuni da ƙofar parlo tayi mata tace, "tashi fita".

ita kuwa baiwar Allah Nabila hankalinta duk ya tashi tabi ta ruɗe, ruwan hawayen da suka gama taruwa cikin idonta suka shiga zuba a hankali.

"Mami wai mike faruwa? ki faɗi mani domin na fita daga cikin duhun da kika sanya ni, anya Mami kin san wace kuwa Nabila da kike kiranta da matar da bata dace dani ba kuma bata can-canci zama sirikarki ba".

"niko nasan wace, ta wuce akirata da tambaɗaɗɗiya mai zubar da mutuncinta akan titi, yarinyar da bata da tarbiya bata da kunya ba... ba... ɗinta har sunyi yawa, aikuwa in har mace ta amsa waɗan nan sunayen kasan tabbas bata can-caci ayi rayuwar aure da ita ba kuwa".

toshe kunnensa yayi haka itama Nabila, dan zantukan Mami duk sun daki kunnuwansu.

Mami ce cikin b'acin rai ta kuma juyawa ga Suhail tace,

"Suhail ka d'auki wannan fitsararriyar yarinyar marar kamun kai, wadda bata san mutunci kanta ba, kayi sauri ka  fitar min da ita daga gida".

Ta ƙare maganar tana nuna masa hanyar waje.

K'asa Suhail ya zube yana rok'on mahaifiyar tasa.

Cikin tsawa ta dakatar dashi tare da cewa,

"Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! kaji nayi rantsuwa uku ko, Suhail matsawar ina Numfashi a doran k'asar nan baza ka auri yarinyar nan ba, kuma koda bayan rai na matsawar ka aureta Allah ya isa ban yafe ba".

Gaba ɗayan su damuwa ce ta bayyana a fuskar su daga shi har Nabila, musaman ma Suhail daya gama shiga ruɗu.

Cikin matsanancin kuka Nabila ta tashi tazo gaban Mami ta durkusa ƙasa tana magana da cewa,

"Mami dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri ki yafe min kuskuren dana aikata maki bisa rashin sani amma dan Allah karki ce zaki raba tsakaninmu".

Tsawa Mami ta mata, nuna ta tayi da hannu tace mata,

"Ke dalla har kin isa kizo gabana ki nemi yafiya a wajena, ke dai zan bawa hak'uri kije can ki ƙarata ki gyara halinki da tarbiyar ki, ki koma kije ki samu mahaifanki ki su baki tarbiya mai kyau, ki zama kamilar mace wanda kowa zeyi sha'awarki, ba ballagazar mace mai faɗa akan titi ba, mai wage muryar data zama al'aura atare da ita ba, magana ta ta k'arshe dake shine idan ma baki sani ba ki sani koda na bar Suhail ya auri mara ɗa'a irinki to fa bazan lamunta daya auri yarinyar daba budurwa ba".

KULLU NAFSIN Completed.Where stories live. Discover now