Roman34 [XXXIV]

741 58 4
                                    

🔘 *KULLU NAFSIN* 🔘
       *1441H/2020M.*

     💥 *FICTION STORY.* 💥

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

            '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•🏇🏼_*

*BY MISS XERKS✍🏼.*
*WATTPAD@ OUM-RAMADHAN1433.*

*DEDICATED TO UMMU NABIL.*

*IN THE HONOUR OF:-*
*{ANTY NICE & BINTA G. DAUDAWA.}*

*[SPECIAL GIFT TO MAMAN JIDDA & MRS KHALEED.]*

~Wattpad @ GaskiyaWritersAsso.~

*~AL-MU'IZZ:-THE GIVER OF HONOUR.~*

'''DEDICATED TO HUSSEIN 80K.''''

*_Alhamdulillahi Na Dawo, Ina Mai Bawa Masoyana Haƙuri Masu Kira na A Waya Da Masu cigiya ta,shirun da kuka ji ba wai hakana bane, ina exams ne shi yasa,amma yanzu zamu ɗora bi'izinillahi, ina ta godiya gare ku da ƙaunar ku._*



Avoid Error Mistakes, Aradu A Gajiya Nayi.

                     *Ꮢ-XXXIV*
                           *34*

*__________📖* *NABILA ABDULLAHI SHATTIMA.*

His Excellency Abdullahi Shattima asalin mahaifan sa ƴan garin bauchi ne, aiki ya dawo da mahaifin sa da mahaifiyar sa nan garin sokoto, anan suka haifi yaran su uku biyu suka rasu ya rage saura Abdullahi kawai, Abdullahi ɗan siyasa ne wanda ya riƙe muƙamai da dama, ya riƙe muk'amin governor a garin sakkoto  shekaru hud'u da suka wuce .

Hansa'u itace matar sa ta farko shekarar su takwas da aure amma ko b'atan wata bata tab'a yi ba.

Hansa'u ta kasance mai tsananin son y'ay'a dan ko na mutane ta gani kamar ta d'auke haka take ji dalilin hakan yasa take yawan yiwa Daddy magana akan ya k'ara aure , shi kuwa Dady ko kusa baya son ana yi masa maganar k'ara aure sabida gani yake kamar matsalar rashin haihuwar daga wajan sa ne.

Haka dai Hansa'u tai tatausar sa tana lallashi da bashi baki akan ya ƙara aure tinda dai asibiti sun basu tabbacin matsalar haihuwa daga gare ta ne.

ganinsa idan har ya ƙara aure to yaci amanar ta ne, duk kuwa da takurawar da mahaifiyar sa ma ke masa akan hakan, dan burin ta a duniya bai wuce taga jikan ta ba tinda Abdullahi shi ɗaya ya rage mata.

wata rana Abdullahi shida Hansa'u suna kan hanyar su ta dawo wa daga bauchi sun kai ziyara kwatsam sai motar su ta sami matsala, gashi titin ba kowa saboda dare ne gashi masu gyara ma babu.

Ya ɗauka waya ya kira da azo a ɗauke su, kamin driver'n ya ƙaraso Allah ya kawo wata mota tazo ta wuce, har motan tayi gaba sai ta dawo, macece aciki ta fito tai masu sallama.

ta tambaye su halin da take ciki suka faɗi mata nan ta taimaka masu da battery'n tata motar suka tada tasu, godiya sose sukai mata tare da nuna jin daɗi, Hansa'u da Zainab sukai musayar numabn waya, tin daga wannan rana suke ta zumunci abin su sose.

tinda Hansa'u ta san Zainab bata da aure take murnar ta sami abokiyar zama, ta ƙudura a ranta da yardar Allah zata sa Alhaji ya aure ta, da ai mata kishiyar da bata san halinta ba ƙwamma ai mata ta gida dama can sun san halin juna tinda dai ta san dole ko su daɗe ko su jima sai ya ƙara aure babu fashi tinda mahaifiyar sa na so.

bayan ya dawo daga tafiyar da yayi akan wata seminer a england tasu ta politicians, ta same shi da maganar auren ta bashi shawara akan ya nemi auren ta saboda Zainaba macece mai nutsuwa da hankali, ga tarin ilimi da tarbiya.

KULLU NAFSIN Completed.Where stories live. Discover now