Page 9

109 15 0
                                    

💦 *SAI NA DAUKI FANSA* 💦

💦💦💦💦
💦💦💦💦💦💦
*STORY ,WRITTEN BY*

*(THREE STARS)*

*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*

*&*
*REAL NANA AISHA*

*&*
*MANAB YAR BABA*

___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________

*DEDICATED TO*

*ANTY FAUZA YAR AMANA ADMIN KAINUWA WRITTER ASSOCIATION*

*Wattpad*: Humairah2019

*Page 9*

''''BISSIMILLAHIR RAHAMIR RAHIM'''''

*✍✍ALKALAMIN REAL NANA AISHA*

Sameer ne ya ce
" Cikin ranan ga zaki islamiya, tab yaushe aka musulmta..?"
Cikin tsiwa ta ce
"Da can ni kafira ce ko ?.."

Siyama ta ce
"A gaida matar liman sai kin dawo.."
Su dai iyayen suna zaune sai kallon su sukeyi,,babu wanda ya ce 'kala a cikin su..
Fadil ne ya ce
"Yaya Fadila nima zani.."
Ta ce
"Kayi zaman ka Fadil islamiyar mata ce zalla babu maza.."
Ya ce
"Ni ma ina so na ri'ka zuwa islamiya.."
Fadila ta ce
"Kaga kar ka tsayar da ni zan bincika maka ta maza,, mommy dady ku samin albarka na tafi neman ilimin addinin islama.."
Dady ya ce
"Fadila cikin wannan ranar zaki fita.? in islamiya kike so ai sai ki fad'amin in d'auko miki malami da zai ri'ka koyar da ke a gida,, amma ba wai ki fita ba a cikin rana ke bakya tsoron kar fever ta kama ki..?"
Haj Batula ta ca'be zancen tace
"Wallahi nima tunanin da nakeyi kenan dadyn su,,wannan ai sai tasa a ri'ka yi mana wani kallo.."
Fadila ta ce
"Mommy daddy ku dai ku samin albarka,,zan tafi ba nesa bane inda zan tafi,, nan kusa ne bayan layin mu wannan islamiyar ta matan aure.."
Daddy ya ce
"Allah ya kiyaye hanya.."
Haka ma Mommy tace mata,, ita kuma sai ta ce
"Nagode daddy & Mommy,,zan tafi sai na dawo.."
Har ta kusa fita daga palour sai daddy ya ce
"Dreba ne zai kaiki ko kuma da motar ki zaki tafiya..?"
" Aa a 'kafa zani dady,, sai na dawo.."
Tana fad'ar haka tayi saurin sa kai ta fita daga palour,, saboda tasan in ta tsaya daddy yana iya cewa ta tsaya dreba ya kaita ita kuma bata muradin tafiya tare da dreba,,nan da nan tafiyar da ko minti goma ba zatayi ba sai a ce wai sai dreba ya kaita..
Tunda ta fito daga gida yan unguwar su ke kallon ta cike da mamakin ganin mace ta fito da ni'kab,,da yake tsallaken gidan su akwai majalisar da samari ke zama,,shiyasa wasu daga ciki suke zancen wa kuma ya fito daga gidan Alh Halilu da 'katon hijabi harda ni'kab,, wasu ma cewa sukeyi watakila bakuwa ce akayi tazo gidan,,toh kuma wajen wa zata zo a gidan su?? yaran gidan da duk ba suda tarbiya balle har suyi abota da ustaziya haka dai suka cigaba da gulmar su..

_(Please mu kula tare da gyara attitudes d'inmu sisters saboda yanzu duniya an daina kiwon damba yanzu wallah³ kiwon mutum ake yi please ya 'kara kiyayewa).._

Tana zuwa islamiyar dama tayiwa mallama magana tana so a fara koya mata tin daga Alif har ta samu ta iya bakake sannan sai a biya mata fatiha,, abinda ya sa kenan tazo islamiyar matan aure saboda in tazo ta 'yan mata zata sha wahala kuma ajin yara za'a kaita,, shiyasa ta yanke shawarar fara zuwa nan d'in in tayi nisa sai ta koma ta 'yan matan..

Ai kuwa sosai mallama ta koya mata yadda zata fahimta sosai,, bayan an tashi mutane sun tafi kuma sai da ta tsaya aka sake biya mata yadda zata gane,,sosai take son koyon karatu musamman yadda ta ga wasu kananen yara suna kira'a sai abun yayi matu'kar birgeta,, ai kuwa saura kad'an kuka ya kubce mata su gasu can kan su yana cikin duhun tukunya har yanzu basu iya komi ba ban da rayuwar boko da aka ginasu akai fatiha ma in suna karata errors yafi goma...
Haka ta dawo gida jikin ta a sanyaye tana ta nanata karatun da aka koya mata,, haka ta cigaba da zuwa islamiyar ta kullum da rana 'karfe 2 ake shiga a taso karfe 4 na yamma,,shima Fadil ta kar'bo masa form na isilamiyar da take zuwa da yake section section ce ita tata ta matan aure ce,,shi kuma ta kowa da kowa ce babu 'bata lokaci ya cike form d'in ya fara zuwa kuma Alhamdulillah suna fahimtar karatun..

SAI NA DAUKI FANSAWhere stories live. Discover now