Page 21& 22

113 13 0
                                    

*💦SAI NA DAUKI FANSA*💦

💦💦💦💦
💦💦💦💦💦💦
*STORY,WRITING BY*

*(THREE STARS)*

*AISHA ABUBAKAR*
*(MRS BB)*

*&*
*REAL NANA AISHA*
*&*

*MANAB YAR BABA*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*DEDICATED TO*

*ANTY FAUZA YAR AMANA ADMIN KAINUWA WRITERs ASSOCIATION*
wattapad: Humaira2019

*PAGE 21&22*

✍✍ *ALK'ALAMIN AISHA ABUBAKAR MRS BB*

Wani kuka ta fashe da shi tana cewa
"Na shiga uku na lalace ummi kin tafi kin barni an samu wani mugu yana gana min azaba, wallahi ban yafe ba,ina ruwanka da ni? da zaka takura wa rayuwata,to ba zanje gidan ba, nace bazu.......ji tai ya lik'e mata baki da hannunsa aiko ta gantsara mashi cizo, babu shiri ya cire hannun cikin sauri yana kallon ta.
Bai san ma murmushi ya subucce masa ba,, can gefe ta koma ta ci gaba da kukanta babu hawaye,don tunda ya d'auketa hawayen suka kafe.
Kunya ce ke cinta ta rasa yanda zatai,, gajiya tayi da kukan k'aryar tayi shiru. Motar ta tsaya get d'in gidansu, ya zaro kudi'nsa ya bashi ya zagaya yabud'eta yace
"Bismillah. ko nan ma sai na d'auke ki?"

Shiru tayi don da gaske kunyarsa take, murmushi yayi yace
"Aiko bazan d'aukekin bah don naga kinji dad'in wacan d'aukar,shiyasa kikeson yanzu ma sai na d'aukekin ko?"
Yafad'a yana lek'o fuskarta, saurin kallonsa tayi ta na zaro kyawawan idanunta,jiyai sunyi mashi masifar kyau.

Kauda kai tayi ta mike tana fitowa tana turo baki tace
"Allah ya sawak'e ni wallahi banji komai ba,, ka matsa na wuce gida ni"

"Bama zakiyi mani godiya ba na kawoki gida cikin jin dad'i ba?"

Tafiya ta ci gaba da yi fuskarta murmushi ne kawai take, ba ta ce komi ba sai da tazo bakin kofar shiga ta juyo,har lokacin yana tsaye ya saka hannuwansa duk cikin aljihun wandonsa ita kawai yake kallo,ya na jin bai taba ganin yarinyar da ta d'auki hankalinsa ba irin wannan. Cikin wani salo da ba ta san ta yi ba tace
"Thanks and good night"
Ta juya ta shige ciki, jingina yayi da get d'in gidan yana d'age kanshi sama tare da lumshe idonsa,fuskarsa wani irin murmushi ne yake da baisan yana yi ba,kafin ya mike yanufi gidansu,don gidaje uku ne tsakanin su.

Bangaren haler kuwa bayan tashiga gida,
Baba lantana tazo takamata cikin damuwa tace"y'an nan hankalina tashe yake akan na baroki wajen wanda ban sani ba, fatan babu abunda yafaru ko?"

Murmushi tayi tace "kikwantar da hankalinki baba lantana, abokina nane a makaranta kuma babu abunda yayi man lafiya lau nake"

Ajiyar zuciya tayi tace"ai ina nan ina tatunanin na baroki wajensa,yanzu me zakifi?"

"Aa kije kiyi kwanciyarki baba lantana banajin yunwa,idan ma inaji zansha coffee ya isheni"

"Shikenan Allah yayi maki albarka,bari naje nakwanta"

Suka wuce d'akunan su tunda haler tagama komai ta kwanta, tunaninsa yazo yashige mata zuciya,sai dai ta juya nan ta koma can tana murmushi tare da rungumar film.
Har ga Allah tanajin wani irin yanayi akanshi, tarasa taya zata fasassara abun,dak'er tasamu tayi bacci shima baccin cike yake da mafarkai kala kala nashi don sai da ta makara sallar Asubah.

SAI NA DAUKI FANSAWhere stories live. Discover now