Page 29 & 30

135 10 10
                                    

*SAI NA ƊAUKI FANSA*💦

            💦💦💦💦
        💦💦💦💦💦💦
*STORY, WRITTEN BY*

   *(THREE STARS)*

*AISHA ABUBAKAR*
           *(MRS BB)*
            
              *&*
*REAL NANA AISHA*
                *&*

*MANAB ƳAR BABA*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*DEDICATED TO*

*ANTY FAUZA YAR AMANA ADMIN KAINUWA WRITTER ASSOCIATION*

wattapad:    Humaira2019

*Page 29 & 30*

*✍️ ALKALAMIN AISHA MRS B B*

Tunda siyama ta ji labarin cewar Ishaq ba ita d'aya zai aura ba, take cikin matsanancin tashin hankali.
Ta fita daga hayyacinta zuciya ta ringa zugata akan ta aikata wani abun,saboda wani irin kishin Ishaq din take ji matsananci, duk yadda mommy ke lallashinta amman ta tub'ure sai hauka take masu, Fadila mamaki take yi don ita bata ga abun tashin hankali ba,saboda ganin an tilasta shi ya aureta ya amince da kyar,don ya ce zai hada da wacce yake so shi ne zai zama tashin hankali, amman ganin idan ta tanka ne haukan kanta zaidawo shi ya sa ta ja bakinta tayi shiru.

Dadyn nasu ya zaunar da ita cikin lallashi yake ce mata.

"Haba siyama me yayi zafi kuma,ki sama ranki ruwan sanyi abun da ma yarinyar kanwar bayanki ce, tunda na ji ance bana ta gama secondary tsaf za ki yi waje da ita ba tare da kin sha wata wahala ba,kinga ki kwantar da hankalinki na san siyamata gwana ce wajen sace zuciyar maza, kiyi kokarin ganin kawar da ita daga cikin gidan ya zama kece jagaba kar kiyi wasa kinji ko,amman duk wannan qbun da kike ba zai hana ba."

Tana hura hanci da turo baki ta ce.
"Dady wallahi nida sakawa zanyi a kashe mani jakar, don bazan iyayin sharing din ishaq da wata jaka ba wallahi."

"Aa ban saki ba kar ki fara idan kikai haka aishi Ishaq din sai yace ya fasa, bayan kuma dama daker ya amince kawai ki dauki shawarar da na baki."

"Shikenan dady zan gwada hakurin, in gani don gaskiya zuciyata sai tafasa take wlh."

💕💕💕💕💕💕💕💕

   *GIDAN ALH MANSUR*

ummi tasaka an hado mata lefe na gani na fada don duk hassadarka dole ka yaba,
Don akwatina dozin biyu shamsiyya da suhaila.
Babu ruwanta da na Siyma, kuma tayi hakan ne saboda ta nuna cewar siyyar ce tata ita ce zabinta,
Har cikin ran ishaq ya ji dadin haka  ba kadan ba,ya kara jin kaunar ummin tasu sosai cikin ranshi.

Shima Ahmad wannan lefen da ya gani ba karamin dadi ya ji ba, don ya san idan tadady ne ba zai yi masu irin shi ba don yana ganin yaran gidan talakawa za su aura.

An saka ranar zuwa Kai lefen daga ko ina hidima ake yi don kowa yana ji da nashi bikin,
Kamar yadda ummi tayi wa mama Kara bikinsu salma da hajjo,itama tayi iyakar kokarinta wajen ganin ta faranta ma ummin, duk da dai hidimar bikin namiji daban dana mace hakan bai saka tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kyautata ma abokiyar zaman nata.

💕💕💕💕💕💕💕💕

Anty fatima kuwa hidima take sosai, babu ji babu gani , kintsa kanwar tata take bilhakki da da gaskiya,don gidan kishiya za ta ba zata so a ce an samu matsala ba, so take ta siyo mata daraja wajen Ishaq din, amman siyya banda kuka babu abun da take aduk sadda tazo mata da wani Abu ta sha, sai tayi mata jan ido sannan ta ansa.

Ranar da aka kai lefen kuwa kulle kanta tayi cikin daki ta ringa garzar kuka, kamar ance za,a yankata hakanan take jin duk son da takewa Ishaq din taji haushi yake bata, saboda yayi mata magana biyu,bayan bai taba gaya mata cewar su biyu zai aura ba saidai kawai taji kwatsam, sannan kuma ace kar tayi fushi akan wane dalili za ta ki yin fushi da shi, duk da dai an yi mata bayani cewa dadyn su ne ya zaɓa mashi matar , amma dai har yanzu kishi take ji, da kyar ma take sakewa da shi, shima sai da Anty Fatima tayi mata faɗa ne.

💦💦💦💦💦

Aliyu yana can America fafutukar neman hanyar da zai anshi result dinsu duka, su samu suzo daurin auren don gaskiya ba zai taba jin dadin wannan auren bashi nan bah, don yana ji da siyya ita daya ce karama kuma mace cikinsu,bai kamata a ce baya nan ba.

Waya suke yi da Anty fatima akan zuwan nashi yake cewa,

"Anty wallahi ko basu bamu ba tahowata zanyi wulakanci ne ai ya hana su su bamu da wuri."

"A a Aliyu kuyi hakuri har zuwa lokacin da zasu baku,ba na son a samu matsala shekara da shekaru kuna karatu tukuru,baku matsu ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi za ku kasa hakuri,haba don Allah kuyi hkr zasu baku."

"Anty bakisan iskancin su ba , wallahi na fa gane take takensu, so suke su ce zasu rikemu a nan abun da kuma bazai yuwu ba wlh,shiyasa suke ta jama na aji tun wancan satin muke abu guda, har yanzu shiru to ni zan yi tahowa ta ko babu shi."

Cikin bada umarni ta ce mashi,
"To bada yawuna bah, kar ka sake ka fara wannan danyen aikin, kuyi hkr ko ma yaushe za su kai ba su baku ba, kuyi hakuri na dan lokaci ne, na san bikin siyya kake wa babu wani abu burinmu ka dawo lafiya ba tare da wata matsalar bah."

"Shikenan Anty amman wallahi idan ban samu bikin nan bah kwata-kwata ba zanji dadi ba."

"Kar ka damu adduarka take bukata ka yi zamanka har sadda Allah zai saka ku rabu lafiya."

Haka nan sukai sallama ba dan ya ji dadin yadda abun ya kasance,
Idan ya tuna saura sati guda daurin auren wani haushi yake Kama shi, gashi dama yana cike da bakincikin rashin ganin haler kwana biyu ga kuma na rashin samun bikin kanwarsa tilo.

Shagulgula aketayi kamar kamar me takowane fanni,
Anty salma da hajjo duk sun zo,
Don anty salma har fa ta kamu, ga matashin cikinta wanda yayi mata kyau sosai,
Duk Wanda ya gansu suna cinkin kwanciyar hankali  ba su da wata damuwa, duk da ance yau da gobe sai Allah,ba ka raba dan Adam da damuwa.

Ayi haƙuri da wannan i am sick😰

SAI NA DAUKI FANSAWhere stories live. Discover now