Page 67&68

99 13 1
                                    

*💦SAI NA DAUKI FANSA*💦

            💦💦💦💦
        💦💦💦💦💦💦
*STORY, WRITTEN BY*

   *(THREE STARS)*

*AISHA ABUBAKAR*
           *(MRS BB)*
            
              *&*
*REAL NANA AISHA*
                *&*

*MANAB YAR BABA*
____________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*DEDICATED TO*

*ANTY FAUZA YAR AMANA ADMIN KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

wattapad:    *Humaira2019*

*Ya ɓace ɓat, kamar ɓatan dabo.; Yabon kai, jahilci ne! Yautai mugun tsuntsu, masha miyarka sai ya yi dare; Zaman duniya, iyawa ne; Yar bori, ba ta kallon bori; Ƙwai a baka, ya fi kaza a akurki; Abincin wani, gubar wani; Aikin banza, harara a duhu; Na zaune, bai ga gari ba; Ƙadangaren bakin tulu, a karka a kar tulu, a bar ka ka ɓata ruwa; Ƙarfe duka ƙarfe ne, amma a cikin ƙarafa akwai zinari da azurfa; Rigakafi, ya fi magana; Rumbun ƙasa, a tashi a barka; Sama ta yiwa yaro nisa, sai dai ya miƙa kai ya yi kallo;*

BARKA DA RANAR HAUSA 2020❤️

Na Sadaukar da wannan shafin ga duk marubutan littafin Hausa da kuma Hausawa.
Ina gaishe da waɗannan grup ɗin
*MARUBUTA*
*KAINUWA WRITTER*
*KAINUWA FANS*
*SAI NA ƊAUKI FANSA FANS*
*REAL NANA AISHA FANS*

   *Page 67&68*

*✍️✍️AƘALAMIN REAL NANA AISHA*

"Sunana Barister Muhamud Isma'il ni ne lauyan mai wakiltar masu ƙara"
Ya ida maganar haɗe da komawa ya zauna.
"Sunana Barister Salisu Sumaila" ni ne lauyan mai kare wanda ake ƙara" cewar wani katon mutum ya ida maganar yana zama a mazauninsa.
Alƙali ya yi rubuce-rubucensa sannan ya ce kotu tana son ganin Alhaji Mansur,
Alhaji Mansur da yake can tare da su mama zaune da Hajjo da Salma sun yi jungum ya taso ya iso inda aka tanadar masa, kallo ɗaya za ka yi masa ka gane yana cikin tashin hankali, bayan ya fito sai Alƙali ya tambaya ko akwai mai tambaya ga Alhaji Mansur, Barister Muhamud ya ce yana da, ya tashi ya nufi inda Alhaji Mansur yake, wanda kallo ɗaya za ka yi masa ya ba ka mugun tausayi saboda ramar da ya yi. Ya ce masa yana so ya fada wa kotu cikaken sunansa da kuma alaƙarsa da iyalen gidan Na Sidi. Sai ya ce
"Sunana Alhaji Mansur mai dala, ni haifafan ƙauyen Na Sidi ne da take ƙaramar hukumar Kaduna, daga baya ne na dawo Kaduna da zama, kuma ni bani da wata alaƙa ta jini da iyalan na Sidi kawai dai zaman gari ne ya haɗu mu da su"
Sai Barister Muhammad ya ce "Don ba ka da alaka da su shi ne ka sanya aka ƙone ƙauyensu.."
"Objcetion my Lord ya kamata Barister Muhammad ya gyara kalamansa saboda har yanzu ba a tabbatar da wanda ake tuhuma shi ne ya aikata laifin" Cewar Barister Salisu. Sai Alkali ya ce
"Ka gyara kalamanka Barister Muhamud"
Ya ce " Na gode ya mai Shari'a" ya ida maganar yana kallon Alhaji Mansur sanan ya ce
"Me ya sa ka aika a ƙone ƙauyen Na Sidi? wane laifi ne suka yi maki da za ka yi masu haka?"
Barister Salisu ya ce "Objection my Lord" Alƙali ya ce "ƙorafi bai ƙarɓu ba ka cigaba da tambayarka Barister Muhammad"
" Na gode ya mai Shari'a" cewar Barister Muhamud ya ida maganar yana kallon Alhaji Mansur haɗe da ce masa
" Ana saurarenka"
"Ba ni ne na aikata ba, sahun ɓarawo na taka saboda sharri ne Alhaji Halilu ya yi min saboda ya ce min mu ƙone ƙauyenmu nida shi sai mu gina kamfani kuma in tare da ni ne babu wanda zai tuhumu tunda ƙauyenmu ne sai a zaci gonata ce na gine, sai ni kuma na ce masa ba zan ci amanar ƙauyena ba don shi ne tushena ko gobe da shi zan tunƙaho don bani da inda ya fi can, shi ne ya ce matuƙar ban yarda ba to zai laƙa min sharrin duk ranar da asirinmu ya tonu, kuma sharrin da zai min wanda har in mutu ba zan mance shi ba, abin da nake tunanin ya sa suka laƙa min wannan sharri dayake mun taɓa zuwa tare da shi ƙauyen wajen mai gari Na Sidi, kuma su ƴaƴansa ba su san Alhaji Halilu ba ni ne suka sani shi ne suka laka min wannan sharrin don yaronsa ƙarami ya taɓa isko mu a gidan lokacin da muka yi wani zuwa ni da shi Alhaji Halilu ɗin har ya ce na rakka sa wajen mai garin, a lokacin ban san me za mu yi ba sai bayan mun tafi ne yake tunkarkar mai gari da maganar to shi ne fa da suka ji sai suka zaci ni ne nake son garin har ma na sanya aka ƙone masu su" Inji Alhaji Mansur ya ida maganar yana zubar da kwalla kamar da gaske ne abin da ya faɗa.

SAI NA DAUKI FANSAWhere stories live. Discover now