💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
*Na*
*Jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)**Follow me on Wattpad @Jeeddahtou*
*3*
A makaranta ma dai ban wani mayar da hankali nayi karatu ba saboda yawan tunane-tunanen da na riƙa yi har malam sai da ya fuskanci ina cikin damuwa. Tare da Rukayya muka dawo muna tafe muna hirar mu irin ta kawaye, gidanmu tace zata je saboda kawai tana so ta ɗebe min kewa na manta da dukkan damuwa ta, sannan kuma ummansu bata nan ko ta koma gidan babu abinda zata yi sai zaman kaɗaici.
Sallama muka ji a bayanmu gaba ɗaya muka waiwaya ba tare da mun amsa sallamar ba, wani kyakkyawan saurayi ne mai cikakkiyar kamala sanye yake da shadda fara ƙall wacce aka yiwa aiki da brown din zare, takalminsa ma brown ne, kansa babu hula wanda Hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawan kwantaccen gashin sa, bai gajiya ba wajen sake yi mana sallama wucewa muka yi muka kyale shi ba tare da mun amsa masa ba, biyo bayan mu yayi. "Haba bayin Allah bai kamata ku ƙi amsa min sallama ba, ga alamu sun nuna min ku malamai ne baxa ku wulakanta ni ba wannan dalilin ne ma ya ja ni har nayi kwadayin yi muku sallama nasan baxan samu matsala ba ya kamata ku amsa min kada ku watsa min ƙasa a ido" kanmu a ƙasa muka amsa masa da "wa alaikumussalam" muna gama amsawa muka juya don cigaba da tafiya, saboda idan da abinda na tsana na tsaya ina magana a hanya ko da yar uwata mace ne ban so ballantana kuma da namiji.
Ganin yadda muka wuce muka kyale shi bai sa yayi zuciya ba sake bin bayanmu yayi, ku yi hakuri na tsayar da ku a hanya ko, na san kuma hakan ba dai-dai bane amma na kasa hakuri ne sbd daya daga cikin ku ce tayi min sata"Gaba daya muka juya muna yi masa kallon mamaki Rukayya ce tayi ƙarfin halin yin magana sbd ta fi ni baki, gaba ɗaya na kasa cewa komai sbd mamakin jin fitowar kalmar sata daga bakinsa "sata fa kace bawan Allah?? Sake wani zancen dai ba wannan ba, mu bama sata kuma bamu taɓa satarwa wani dan adam komai ba, muna bakin kokari wajen dogaro da abinda Allah ya wadata mu da shi"
Murmushi yayi wanda sai da fararen hakoransa suka bayyana sannan ya dan sha kunu "ba ke nace kin min sata ba kawarki ce, amma ita ma bata san ta min satar ba" A razane na dube shi kirjina na dukan uku-uku sbd bana so na sake dakkowa innah abinda xai xame mana abin gori da bak'ar Magana, cikin rawar murya na fara magana "ban taɓa yiwa wani sata ba tunda nake malam watakila mai kama da ni ka gani" ban jira amsar da zai bani ba na ja hannun Rukayya muka cigaba da tafiya.
Sake shiga gabanmu yayi "ku tsaya mu warware matsalar mana ko su ku ke yi sai Maganar ta je gaba? Idan haka ku ka zaba shikenan, amma ni shi ne abinda bana so. Tsayawa muka yi cak muna sauraron shi, gyara tsayuwa yayi tare da tambayata kin san satar da kika yi min. Da sauri na amsa masa da ban sani ba, rausayar da kansa yayi.
"To zuciyata kika sata"
Gabana ne ya fadi mamaki ya mamaye ni wai yau ni wani da namiji yake cewa na sace masa zuciya abinda ban taɓa ji ba kenan, sbd tunda nake babu wanda ya taɓa tunkarata da sunan na burge shi ballantana har ya furta yana sona.Ganin dogon tunanin da na tafi ya sanya shi yi min magana "lafiya naji kin yi shiru ko ba gaskiya bane abinda na fada?" Ban bashi amsa ba na juya na tafi tare da Rukayya na bar shi suna Magana ban san me take fada masa ba.
Sai da na shiga gida da kusan minti biyar sannan na ganta, sallama tayi na amsa mata duk jikina yayi sanyi.
Masifa ta fara yi min "ke shikenan daga fara magana sai ki wani tafi ki kyale mutane sai ni nayi masa bayani, na fada masa sunanki da kwatancen gidan nan dan haka ki shirya yau kina da babban bako"
Fito da ido nayi "Haba ya xaki min haka ban so kika bashi kwatancena ba" hararata tayi "ok so kike ki xauna a cigaba da miki gori ba mai tayawa ko, ai ko ba aurenki xai yi ba yana da kyau kema a ga kina xance kin huta gori" dakatar da ita nayi "Kinga ni duk wannan bai dame ni ba sama da yadda idan nayi aure xan tafi na bar innah a wannan gidan shi ne abinda ya fi tayar min da hankali"

YOU ARE READING
DUKKAN TSANANI
RomanceYunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta t...