DUKKAN TSANANI page 58

1.4K 124 16
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *58*

Gaba ɗaya suka danno kai cikin gidan suna ƙoƙarin shiga d'akinta, da sauri innah ta ƙarasa wajen su tare da dakatar da su.
"Haba bayin Allah ya za a yi ku shigo cikin gidan matan aure haka kai tsaye ba sallama kuma kuna ƙoƙarin shiga dakinta ba tare da neman izini ba"
A fusace suka bata amsa
"Kin san irin ɓarnar da tayi ne da xaki kareta, mutum fa ta kashe, ko dan ba ɗanki aka kashe ba"

Dafe kirji muka yi gaba ɗaya muna salati, nan da nan innah ta hau kuka tausayin Innah Salamatu ne ya kamata, cikin jimami muka tambaye su wanda ta kashe.
A nan suke faɗa mana malam Jibo ne, kafin su kammala bamu amsa har fusatattu daga cikin su sun faɗa dakinta sun fito da ita.

Bin ta muka yi muna kuka har aka isa kofar gida, sauran mutan gidan mu kuwa sai guna-guni suke yi suna gulmar ta, babu wanda ya bada hakurin a kyaleta. mutanen unguwa ne suka taru a kofar gidan mu kowa na tofa albarkacin bakinsa, ba ƙaramin mutuncin gidan mu ta xubar ba, duk da cewa dai kowa ya sani halinta, ƙoƙarin kai ta wajen yan sanda aka yi, sai mai unguwa ne yace a dakata a jira babanmu ya dawo, shi kuma malam Jibo aka wuce da shi asibiti.

Taimakon gaggawa aka shiga bashi cikin ikon Allah ya farfaɗo a daren aka sallamo shi, ita kuwa A'isha babu wanda yake ta tata sbd masifar da uwarta ta dakko, a kwance take a daki tana ta numfarfashi Inna ce tasa aka kaita chemist aka bata magani.

A daren aka samu aka kashe case din ba tare da an je wajen hukuma ba, sai dai malam Jibo ya yi rantsuwa ko tana so ko bata so sai ya auri A'isha sai dai ta rataye kanta sbd baƙin ciki.

A ranar daga ni har Rukayya a gidan Innah muka kwana sbd tashin hankali, sai washe gari bayan rana ta d'aga muka koma gida, ina komawa na bawa Adda labarin halin da Innah Salamatu taso jefa kanta da ƴaƴanta, ba ƙaramin tausayi ta bata ba don abin gaba ɗaya babu daɗin ji.

***********

Shirye-shirye sun fara nisa don yau bai fi sati uku ne suka rage a daura min aure da izuddeen ba, a kullum akwai irin kalar gyaran jikin da xa a yi min, ko kofar gida bana fita sbd ana so jikina yayi kyau ya gyaru, Adda ce ta ɗauki nauyin komai har gida wata yar Sudan ke xuwa ta gyara ni.
Baya ga kayan mata da ake ta bani gaskiya Adda na matuƙar hidima da ni, sai dai fatan Allah ya bani ikon saka mata da abinda tayi min.

Sallamar Innah naji da sauri na ƙarasa wajenta ina yi mata sannu da xuwa.
Kallona tayi cike da kulawa.

"kinga wani kyau da kika yi Sa'adatu lallai gyara yana yi"
A kunyace na kalleta.
"Ai babu abinda xamu ce da Adda sai godiya innah, amma tana ƙoƙari sosai a kaina"

Riƙe da hannun junanmu muka shiga dakin Adda a kwance muka tarar da ita, tana ganin innah ta miƙe tana mata sannu da xuwa ruwa naje na kawo mata da abinci sannan na fita na basu guri.

Inna tazo wajan addah ne don su yi shawara akan maganar yadda za a yi da kayan dakin da za a siya min, tunda Babana a yanxu ba shi da ƙarfin da zai iya yi min komai da ake buƙata.

Kallon Adda tayi sannan ta fara magana.
"Kin ji dai dalilin da ya kawo ni gidan nan, tunda yanzu ba mu da halin kuɗin kayan dakin Sa'adatu ba mu da dalilin su, me xai hana a siyar da gonata guda ɗaya, don mu samu mu siya mata 'yan kayan zamanin nan da ɗan abinda ba a rasa ba, kin ga dai yaron nan yayi mana hidima sosai kuma yadda naji ance ya gyara gidansa sosai bai kamata mu nuna rashin xuciya ba ko ya kika gani?"

Mayar da ajiyar zuciya Adda tayi
"Eh wlh yaya haka yayi dama anjima nake so nazo wajenki mu yi maganar sai kuma ga ki Allah ya kawo ki"

Tashi tayi ta shiga laluben kan gadonta, wata leda ta d'akko tare da mikawa innah.

"kinga wannan kuɗi ne Abban su Ihsan ya bayar a baki, yace babu yawa ki karba da hakuri, wannan kuma kuɗin wajan Dr ne da yake bawa Sa'adatu, shi ne muke ajiye wa, kinga duk su ma zasu taimaka a rage wani abin, sai mu shiga kasuwa mu siyo kayan kitchen da sauran abubuwan buƙata, a yadda nake so ma idan Allah yasa kuɗin sun yi ragowa sai a haɗa mata har da gararta insha Allah"

Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Innah ba ƙaramin dadi taji ba.
"Kai Alhamdulillah na gode, shikenan duk abinda kika ce haka za a yi, Allah ya saka muku da alkhairi ALLAH ya bar mana zumuncin mu"
Amsawa tayi da "Ameen"

********
zaune nake kan sallaya na idar da sallar azahar, Kur'ani ne a hannuna ina karantawa,
wayata naji tana qara, cikin nutsuwa  na kai hannuna na ɗauka sunan Dr na gani yana yawo a kan wayar, a hankali na saka hannu na na danna.

Sallama nayi masa, cike da girmamawa ya amsa, shiru muka yi na wani ɗan lokaci, shi ne ya katse mana shirun cikin marairaicewa ya fara magana.

"Nayi fushi kanwata dama abin yar haka ne ko missed call dinki bana gani, wannan ya nuna bana ranki ko kaɗan kanwata, ko baki tambayi lafiyata ba ai kya kira ni ki tambayi yaranki ko?"

Cikin muryar tausayi kamar zanyi kuka nace
"Allah ya baka hakuri yayana wlh gaba ɗaya yanzu ba ni da wani ishashshan lokaci, amma kana raina kada kayi fushi da yar kanwar ka, ya aikin ya gida ina yarana?"

Siririyar ajiyar zuciya yayi
"Uhmm Sa'adatu kenan duk suna lafiya"

A hankali na sake tambayarsa
"To ina kawata ko Aunty Ruqayyah ma zan dinga ce mata?"

Siririyar dariya ya saki
"Ke dai kika sani wannan ai kun fi kusa, ko da yake yanzu mun fi kusa da ita, saura kaɗan ma ta dawo hannuna sai kin cike form xaki riƙa ganinta"

Da sauri nace
"A'a gaskiya ban yarda ba"
na faɗa ina mai jin dadin kalamansa.

Murmushi yayi
"Baza ki gane ba yarinya ni kin ƙi ma ki bari kiji abinda na bugo na faɗa miki"

A hankali nace

"To ina jinka yayana"

"Kiyi hakuri abin ne yazo min lokaci ɗaya, ban san biki ya matso haka ba, sai jiya Rukayya take faɗa min, dama so nake ki faɗawa Addah zan zo mu je da ke, ki zaɓi kayan da kike so na siya miki na aure tawa gudummar kenan"

Suman zaune nayi jina na wasu mintuna suka ɗauke, ji nake kamar ba da gaske yake ba

"Hello" ya faɗa
"Kina ji na kanwata?"

Cikin rawar murya na amsa
"Ina jinka yayana" ji nayi kuka na shirin kwace min.
A kasalance yace
"Aa kuka kuma zaki min kanwata? bama 'yar haka fa da ke, kin xama jinina Sa'adatu duk abinda nayi miki ban yi asara ba, kece silar haɗa ni da macen da nake ganin xata xama gatana, zata bani farin cikin da na rasa a rayuwata, kin yi min komai Sa'adatu, duk abinda nayi miki ban yi asara ba"

A hankali nasa hannu na share hawayen da ke ƙoƙarin bata min fuskata.
"Na gode na gode yayana Allah ya raya zuri'a Allah yaji kan mahaifa"
na faɗa ina mai sake fashewa da wani sabon kukan"

Cike da damuwa yace
"Bari na kashe wayata idan kin gama kukan na sake kira, kin san bana jure zubar hawayen ki, idan da abinda na tsana shi ne naga idanun ki na xubda hawaye"
Da sauri  ya kashe wayar.

Tashi nayi na fita ina zabgawa Addah kira da sauri ta fito muka haɗu a bakin kofar shiga dakinta, Allah ya tsare bamu yi karo ba.

Dubana Addah tayi "Menene Sa'adatu kike ta faman kirana haka"
ta faɗa tare da daura dankwalinta da ya kusa fad'uwa, a guje na faɗa jikinta ina dariya mai haɗe da kuka.
Muryata na rawa nace
"Dr ne Adda"
A hankali ta dube ni
"Ki faɗa min mana Sa'adatu me ya faru?"

Share hayawe nayi
"Addah wai cewa yayi na shirya gobe zai zo muje na zaɓi kayan dakin da zai siya min a matsayin gudunmawar sa"

Wani farin ciki ne ya lullube xuciyarta "Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah abin godia kai masha Allahu, Allah sarki wannan bawan Allah, Allah ya saka masa da alkhairi gaskiya doctor mai kaunar ki ne da gaskiya Allah ya biya shi da aljanna"

Wayar mijinta ta kira ta faɗa masa, shi ma ba ƙaramin farin ciki yayi da haka ba.


*Jeeddahtulkhair😘*

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now