DUKKAN TSANANI page 25

1.5K 133 14
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

              *25*

A soron nake tsaye kamar wacce aka kafe na kasa komawa cikin gida, duk fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata addu'a ɗaya nake yi Allah yasa kada malam Jibo yaje ya fadi karya da gaskiya ya kunno min wani shirrin a wajen Baba, ban iya komawa cikin gida ba a soron na tsaya don jin abinda zai dawo min da shi, fatan da nake yi Allah yasa wannan zargin da yayi mana ya zama silar rabuwar auren gaba ɗaya.
Jan salim ya riƙa yi tamkar ya kamo barawo shi kuwa bin sa kawai yake kamar raƙumi da akala.
Cikin soron gidan su suka shiga, sallama malam jibo ya shiga yi, jin muryarsa da Baban Sa'adatu yayi shi ne dalilin da yasa ya fito da sauri don duk lokacin da yaji malam Jibo yana irin wannan sallamar yasan ba lafiya.
Ganin shi riƙe da kwalar rigar salim ne ya bashi mamaki gami da tambayarsa ko lafiya, yana huci ya fara bashi amsa.

"Wlh yaron nan naku ɗan kwangilar kwartanci ne, masifa yake ƙoƙarin kunna min a gidana, shi ne yake ƙoƙarin kashe min aure, yanzun nan daga wajen Sa'adatu yake yaje yana xugata, a kan ta rabu da ni ban dace da rayuwarta ba, har faɗa yake idan tana son guduwa xai bata mafakar inda zata buya, kuma zai bata kuɗin motar da zata tafi"
Wani kallo Baban Sa'adatu ya bi salim da shi tare da girgiza kai. "tabbas duk abinda aka zargi yaron nan da shi baxan yi musu ba Malam, sbd tun tana gida shi ne mai shige mata gaba ta rika yin shashanci"

Cikin fushi ya shiga nuna Salim da yatsa "Wannan ita ce tarbiyyar da muka baka ko salim? dama duk abinda Sa'adatu take yi kaine kake goya mata baya ko, cin amanar da xaka yi min kenan me nayi maka kake bina da sharri haka? Allah ya isa tsakanina da kai"
yana ƙarasa fadar haka ya shige cikin gida.
Bangaren su salim ya shiga inda ya kira mahaifinsa, ganinsa a gigice ne yasa ya fara tambayarsa amma bai saurare shi ba ballantana ya bashi amsa.
Hankalinsa a tashe ya sake dubansa "lafiya yaya na ganka a hargitse haka Allah yasa dai ba wani abin ne ya taso ba, don naga kamar baka cikin nutsuwarka"

Kofar fita ya shiga nuna masa "mu je soro kaga irin maganar da salim yake shirin dakko mana muna zaman mu lafiya" jin ya ambaci salim ne ya sa ya fita da sauri hankalinsa a tashe ko takalmi bai saka ba ya fita.
Har yanxu dai malam Jibo rike yake da wuyan salim yaƙi sakinsa, ba don bazai iya kwacewa bane yasa ya kyale shi kawai don yana gani mutuncin wanda ya girme shi ne.

Cike da mamaki mahaifinsa yake magana "Lafiya malam Jibo wani abu salim yayi maka haka naga ka riƙe masa wuyan riga, Allah yasa dai ba aika-aika yayi maka ba"
Gyara tsayuwa yayi fuskarsa a murtuke ya fara magana
"Na Kama su suna lalata shi da Sa'adatu, kaga abinda yayi yafi ƙarfin mu kira shi da aika-aika sai dai lalata"
Cike da tashin hankali salim ya dubi malam Jibo "ka rantse da Allah abinda ka kama mu muna yi kenan, da girmanka ka rika karya kaji tsoron Allah duk abinda ka faɗa yana kallonka kuma Mala'iku suna rubutawa, kuma zaka tsaya ranar shaida" Daka masa tsawa mahaifinsa yayi "yi min shiru mutumin kawai kada na sake jin bakinka, na shiga ban dauka ba ai bata fidda barawo, me yasa kaje masa gida? da baka je ba zai ce kayi masa haka ne, ko kai kaɗai ne ɗa a cikin gidan nan, duk abinda ya faɗa dole mu yarda tunda daga gidansa ya kamo ka"

Sauke ajiyar zuciya Baban Sa'adatu yayi "gaskiya yarinyar nan ta cika lalatacciya, dama abinda take yi kafin aure shi ne bayan tayi auren ma baxa ta sallata ba sai ta ɗora daga inda ta tsaya, amma kuwa yarinyar nan bata ji daɗin halinta ba, malam Jibo kada kaga laifin salim ka fara ganin laifin Sa'adatu sbd ita ce ta gayyato shi yazo mata, da bata kira shi ba baxai zo ba, idan kayi aiki da hankali xaka ga cewa sai da ta lura baka nan sannan ta kira shi, ya zama dole na ɗauki mummunan mataki a kan yarinyar nan sbd idan nayi sake ƙarshe ni xata jawowa abin kunya"
Cikin nutsuwa mahaifin salim ya dube shi
"A'a yaya ba haka za a yi ba a bi abin nan a hankali, sbd abu ne da yake buƙatar bincike ka bar min komai a hannuna zan san yadda za a yi" kallon salim yayi tare da cewa "tashi ka shiga ciki ka jira mu da irin hukuncin da zamu yanke maka"

DUKKAN TSANANI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora