DUKKAN TSANANI page 54

1.3K 115 6
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
        *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

               *54*

Da sauri da sauri mahaifin Sa'adatu yake tafiya, sbd yana so yaje ya sanar da sauran 'yan uwansa maganar auren Sa'adatu, gida-gida ya riƙa bi yana sanar musu gobe xa a kawo kayan aurenta, mutane sai farin ciki suke tare da yi mata fatan alkhairi sbd sun san bak'ar wuyar da ta girbe a gidan su.

Ɗakin innarta ya nufa, da sallama ya shiga tare da samun wajen zama ya xauna, a sanyaye ta amsa masa tare da mi'kewa daga kwanciyar da tayi, fuskarsa yalwace da murmushi yace

"Ya kamata a san abinda xa a shiryawa mutanen nan kinga gobe ne zasu kawo kayan aure, kuma bai kamata a bar su haka nan ba me kike ganin ya dace a yi?"
Ya faɗa tare da gyara zamansa.

A hankali ta fara magana "kwarai kuwa hakan yana da kyau xan je gidan su Rukayya anjima mu yi shawarar abinda ya kamata a yi"

Murmushi yayi "to babu laifi sai kin je ɗin"
Kuɗi ya miko mata dubu biyar"Ga wannan idan da ciko sai ki faɗa min"
Karba tayi tare da yi masa godiya.

Tashi yayi ya nufi ɗakin Innah Salamatu, ita ma irin abinda ya faɗawa Innah ya faɗa mata, nan da nan baƙin ciki ya bayyana a fuskar ta, ji tayi kamar ta fad'i sbd baƙin cikin da ya tokare mata zuciyarta, yanzu kamar Sa'adatu da take bazawara har xata riga yan matanta aure gaskiya da sake, katse mata tunani yayi da cewa.

"Ya naji baki ce komai bane?"
A yatsine ta amsa
"Me kake so nace dama maganar aurenta y shafe ni ne, kaje ka faɗawa wadanda abin ya shafa, ina ruwana da rayuwar su"

Ta ƙarasa maganar tare da kawar da kanta gefe guda.
Jikinsa babu karfi ya tashi ya fita ya barta tana ta balbala masifa.

Fitar shi ke da wuya ta fashe da kuka, tana ta Allah ya isa wai innar Sa'adatu ce tayi mata asiri ƴaƴanta suka ki auruwa, Aisha ce ta shigo ta tarar da ita a wannan halin.

Cike da rikicewa ta dubeta.
"Me ya same ki Innah wani abin aka yi miki?"
Cikin kuka tace
"Ba ni aka yi wa ba har da ku, domin da ni da ku duk muna cikin bala'i wannan yaƙin namu ne gaba ɗaya, don haka dole sai mun tashi tsaye mun yi fito na fito da mutanen nan"
Cike da firgici ta dubeta tare da neman waje ta xauna.
"Ban fahince ki ba innah me kike son faɗa min ne?"
Share hayawenta tayi.
"Gobe-Goben nan za a kawo kayan Sa'adatu da wannan tsohon saurayin nata wanda naje gidansu na soke auren amma da yake maye ne Sai da ya sake dawowa"

Zaro ido A'isha tayi
"Me kika ce Innah wlh baxa ta sabu ba, dole ki tashi mu tafi wajen malam Jibo mu xuga shi, yaxo yace bai yarda ba sai an mayar da aurensa da ita, yace shi bai saki matarsa ba kinga dole maganar auren ta warware"

Ba ƙaramin daɗin shawarar A'isha taji ba da sauri suka saka takalman su suka fita, a soro suka ci karo da Baba, a hankali yayi musu magana.

"Ina xaku je haka da sauri?"
Ko kallonsa basu yi ba suka wuce suka kyale shi. Bin su yayi da kallon mamaki don ya san ba komai ke damunsu ba illa hassada da baƙin ciki.

A kofar gida suka tarar da malam Jibo, tare da wani mutum suna magana har ƙasa suka tsugunna suka gaida shi, umarni ya basu da su shiga daga cikin shagon gidan su jira shi.

A hankali suka taka suka shiga ciki, zuciyar su na musu sa'kar irin sharrin da zasu kunnawa Sa'adatu a wajensa.

Basu dade da xama ba ya shigo, hannun shi riƙe da xarmakeken carbi, cike da farin ciki ya tarbe su don ya san labarin Sa'adatu suka zo faɗa masa, waje ya samu ya xauna tare da yi musu sannu da zuwa.

DUKKAN TSANANI Where stories live. Discover now