DUKKAN TSANANI page 20

1.7K 125 11
                                    

💋💋💋💋💋💋
*DUKKAN TSANANI*
💋💋💋💋💋💋
            *Na*
*Jeeddah Tijjani*
         *Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*

*Follow me on Wattpad @jeeddahtou*

               *20*

*Wannan shafin gaba ɗaya naki ne halak malak na bar miki shi kiyi yadda kike so da shi, kawata aminiyata maxumunciyata abokiyar shawara abokiyar faɗa AISHA SABO ABDULLAHI (mrs khamis) Allah ya bar min ke ko ba kai ba ƙafa ko dan naci dariya🤣🤣🤣*

Muna isa bakin kofar gidan umman Rukayya ta umarce ni da yin Bismillah tare da shiga da kafar dama don neman sa'a, ban yi gardama ba nayi abinda ta umarce ni,  daga saka kafata a soron gidan na fara cin karo duwatsu da kawazzabai saura kiris na fadi, haka na daure na buɗe idona don gudun kada na fada wani ramin sai da muka isa tsakar gida na rufe fuskata, hayaniyar da ake yi a gidan ne ya daki kunnena yara ne ƙanana waɗanda baxa su wuce shekara biyar ba xuwa shida suke ta wasanni da tsalle-tsalle, ilahirin tsakar gidan a jike yake baka jin komai na tashi banda warin banɗaki, gidan dai babu sha'awar gani saboda tsafta bata wadaci mazauna gidan ba, yaran gidan na ganinmu suka hau ihu suna ga amarya har da masu kokarin kama mayafin jikina sai da Rukayya ta kai musu duka sannan suka tarwatse.

kai tsaye dakin uwar gida aka shigar da ni, tare suke a dakin ita da ragowar matan nasa biyu, gefen gadonta aka samu aka xaunar da ni ragowar yan rakiyata kuma suka tsaya daga waje, kasancewar dakin baxai dauke mu gaba ɗaya ba, gaisawa suka yi da su umma sama sama saboda uwar gidan ba sosai take da kirki ba, ragowar kishiyoyin nata sun ɗan fi ta sakin fuska, sun fi karɓar mu hannu biyu-biyi. umma ce ta fara magana "To ga kanwarku kuma amaryarku mun kawo dan Allah ku riketa amana, duk abinda ya dace na gyara ku rika yi mata, kuma ku riƙa hakuri da gazawarta"
Duk bayanin da umma tayi basu ce komai ba ƙaramar cikinsu ce tayi ƙarfin halin yin magana "to xamu riketa amana Allah ya bamu ikon zama lafiya da junanmu"
Gaba daya aka amsa mata da "ameen"

Tashi muka yi muka nufi ɗakin da xan xauna tunda na hango kofar dakin wani baƙin ciki ya daki xuciyata, ilahirin bangon dakin duk yayi jirwaye, ita kanta farar ƙasar ba mai kyau ya siya ba, duk macewar gidan mu ya rufawa na Malam jibo asiri, mukulli Rukayya ta karba ta bude kofar dakin, a hankali na saka kafata na shiga babu komai a dakin sai uban duhu, wayar Rukayya aka kunna don ganin hanya, duba dakin na shiga yi naga bangon duk ya lalace, wani ƙarin abin takaici ko labule ba a saka min ba, ledar ma bata shimfidu dai-dai ba saboda ramukan da ke dakin, kukana ne ya tsananta yanzu nake kara tabbatar da irin cutar da aka yi min.

Kama hannuna umma tayi ta zaunar da ni kan tamulalliyar katifar da aka shimfida min wacce ko arxikin zanin gado bata samu ba, kusa da ni ta xauna hannunta cikin nawa a hankali take min rada a cikin kunnena"kiyi hakuri Sa'adatu kinga dai yadda Allah yayi da mu, ba yadda xamu yi tsarin Allah shi ne tsari kuma duk yadda ya tsara haka xa a yi, a kullum addu'ar alkhairi muke yi kuma muna nan insha Allah xai tabbatar mana da alkhairin, kiyi hakuri ki daina kuka wata rana komai xai xamo tarihi, ki yiwa mijinki biyayya ki xauna da kowa da xuciya daya, insha Allah xaki cinye wannan jarrabawar cikin sauki kuma baxa ki tabe ba har abada fatana a gareki shi ne ki riƙa Allah tare da addu'a duk rintsi kada ki manta da karatun Alkur'ani da kiyamullaili ki kuma saka a ranki DUKKAN TSANANI yana tare da sauki"
rungume ni tayi muna ta kuka tare, ita kuwa Rukayya tun shigowar mu take ta kuka kamar iya ce Amaryar babu abinda take iya faɗa banda Allah ya saka miki Sa'adatu.

Sun ɗan yi zama na yan awowi don sai da aka kira sallar isha muka yi sallah tare da su sannan suka tashi don tafiya gida, kana kallon fuskokin ya'yan gidan mu xaka tabbatar da cewa suna cikin farin cikin abinda aka yi min banda fara'a babu abinda suke yi, ganin idon ummansu Rukayya ne ma ya hana su magana amma da babu ita da sai na gudu don habaicin da xasu yi min.

DUKKAN TSANANI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora