chapter 5

358 38 1
                                    

RAINA

BY

SAFNAH ALIYU JAWABI

Bismillahi rahamanin rahim

Kyara kwanciyarta suhaila tayi tana Mai cigaba da sauraron wakar ta hankalinta kwance tunda ridwan ya tabbatar mata da babu komai cikin zuciyar suhaima,saboda yanda take jin daďin wakar har wani lumshe ido take.

Ahankali cikin sanďa yake takowa har yakai inda take, ihu yamata saman Kai,  ihu ta kwalla tsabar tsorata da tayi banda bari babu abinda jikin ta yake.

Shikuwa banda Dariya babu abinda yake harda rike ciki, jin shiru babu abinda yasame ta yasa ta shiga buďe idonta Ahankali harta buďe gabaki ďaya, ganinsa yasa ta Murtuke Fuska hanyar toilet ta nufa cikin sauri,baiyi tunanin tsayar da itaba Dan tunanin sa wani abun zatayi.

Aikuwa tana shiga ta datse kofar daga cike tace, "yaya fauzan katafi bana son ganin ka nafaďa maka ka daina shiga hanyata, karasa maganar tayi cikin kuka.

Jin kukanta yasa ya rikece, magiya yashigayi kanta buďe kofar amma ina haka ya hakura yatafi.

Tana jin Fitarsa kuwa ta buďe gabaki ďayan idanuwanta sun kumbara.

Kwanciya tayi Tana sakin ajiyar zuciya.

Koda daddy yadawo ganin baiganta tare da mummy ba yasa yakalle ta yace, "wai nikuwa ina mama na?

,"kamar tana ďakin ta.

"kamar tana ďakin ta fa kika ce?

"Eh.

"amma nikam wallahi idan baďan agabana kika haifi suhaila ba wallahi sainace canzanta aka miki bake kika haife taba, wannan wani irin rayuwa ne, kinji yarinya shiru amma baki tashi kin duba lafiyar taba, tashi yayi ya nufi ďakin ta.

Murmushi kawai tayi Tana yaba yanda yake nuna soda kulawa ga gudan jinin sa suhaila.

Akwace yasame ta, jikin ta alullube da bargo, kiran sunan ta yayi, ahanki ta buďe idonta wanda tuni suka kaďa sukayi ja.

Ganin haka bakaramar tsoratar da shi yayi ba, cikin sauri yashiga yaye bargon, taba jikin ta yayi yaji safe sosai ajikin.

Tambayar ta abinda ke damunta yashiga Yi, aikuwa nandanan ta fashe da kuka, cikin sauri ya fitar  da wayar sa daga aljihu,kiran family Dr ďinsu yashigayi ďagawa yayi bakinsa ďauke da sallama, sanar dashi abinda yake faruwa yayi sannan ya ije wayar.

Da sauri yafita yasanar da mummy itama sosai ta rikece da ganin jikin nata, kuda likita yazo dubanta yayi sannan yasaka mata ruwa haďa da magunguna.

Godiya sukayi masa bayan ya sanar dasu kawai dai firgici ne  da rashin samun Hutu,sallama sukayi masa bayan ya nuna musu yanda zasu cire ruwan idan yakare.

Koda ruwan yakare aka cire mata, ruwa Mai ďume mummy ta haďa mata tayi wanka bayan ta fito tea mai zafe mummy ta kowa mata Tasha, bayan ta gama  ta kwanta.

Mamaki sosai ciwon nata yabasu musamman jin wai firgita tayi, to meya firgitar da ita? ganin  kalau ta dawo daga makaranta.

RAINA 2020Donde viven las historias. Descúbrelo ahora