chaptar 4️⃣1️⃣➖4️⃣2️⃣

268 39 8
                                    

Raina~🌹

⬅️⬅️⬅️⬅️

🏵️Written 🏵️

🌻By 🌻

🌟SAFNAH ALIYU JAWABI 🌟

🌳Wattpad 🌳

🌹SAFNAH ALIYU JAWABI 🌹

⬅️⬅️⬅️⬅️⬅️⬅️⬅️

🌟Taurari🌟 🌟writers 🌟association🌟

(🌟🌟The Stars 🌟🌟that shine 🌟🌟in the world 🌟) 🌟🌟🌟

(🌟Of writer's🌟)🌟

Bismillahi rahamanin rahim

Suna gama cin abincin ammi suka zauna afalo ana ɗan taba hira, sama sama suhaila ke amsa duk abinda ammi ta sako ta ciki,ammi na lura da ita gabaki ɗaya hankali tana gun ridwan .

Murmushi ammi tayi tace,"suhaila ko zaku tafi ɗaki ne?

Sukuyar da kai suhaila tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Sosai kunyar take kara sonta da kimar ta cikin zuciyar ammi,(mata mu sani itafa kunya ga mace ado ce?

Tashi ammi tayi ta rike hannunsa ta nufi sashin su dashi,harta dawo suhaila na zaune a inda ta barta.

Murmushi tayi tace,"suhaila tashi ki shiga ciki ,yauwa dama nace idan bazaki iya masa wanka ba ,akwai dama wanda yake zuwa ya taimaka masa,wansa ne ɗan wajan yayata sai akira shi.

Shiru suhaila tayi don kuwa wannan amsa tafi ƙarfin suhaila,"hmmm to shikenan babu damuwa kina iya zama a bangare ne idan suka kammala saiki koma ko?

Buɗe baki tayi da kyar tace,"to ammi.

Tashi suhaila tayi ta nufi sashin ammi,kanta a sunkuye.

Murmushi ammi tayi tana jin tsantsar sonta na shiga zuciyar ta.

*****

Zaune yaya take gabaki ɗaya ta rasa abinda ke mata daɗi jinta take kamar ba itaba tsabar yanda take jin ciwon abinda mummy tayi mata ,kwafa tayi tace,"hmmm wallahi zaku san kunyi dani,saina nuna muku kuran ku.

Tashi tayi ta saba gyalanta ta fita.

******

Mummy kuwa bayan jama'a sun watse gabaki ɗaya jin gidan take kamar babu kowa domin kuwa har yanzu Abba bai sauko daga fushin da yake ba.

Sallamar yaya da taji ne yasa taji hanjin cikin ta na juyawa,jiki na rawa ta miki tanai mata Barka da zuwa.

"Sannu da zuwa yaya ya g...

Daka mata tsawa tayi wanda saida Abba ya tashi daga barci da yake tace,"Malama bana bukatar gaisuwar ki,domin kuwa daga safe zuwa yanzu Allah kaɗai yasan adadin mutanan da suka gaishe ni, don haka bana bukata,tunda kin zama munafuka algunguma,makira mai mance alkairi dole ki saka min da wannan butulcin ,aidama ƴan uba basu gaji halilci ba,gadon uwa kuma ai dole dama ai kin taba ganin inda barewa yayi gudu ɗanta yayi rurrufe?

RAINA 2020Where stories live. Discover now