chapter 21-22

315 31 2
                                    

RAINA

By

SAFNAH ALIYU JAWABI

Wattpad SAFNAH ALIYU JAWABI

Face book SAFNAH ALIYU JAWABI

TAURARI 🌟 WRITER'S ASSOCIATION 🌟

(the stars that in the world of writers 🌟  🌟
            🌟   🌟  🌟

Bismillahi rahamanin rahim

Mikewa suhaila tayi tace, " bana da bakin da zan gode muku, saidai nace ALLAH ya biya ku da mafificin alkairi .

Murmushi Kalil yayi yace, "babu damuwa ina fatan ďaurewar zumunci atsakanin mu, ďago Kai haidar yayi cikin sauri jin abinda Kalil ya faďa.

Murmushi tayi tace, "IN SHA ALLAH yanzu muje ku kaini gida.

Matsowa haidar yayi yace, "ki sani duk abinda mukayi miki domin ALLAH mukayi Don haka bama bukatar ganin 'yayanki bare har suyi mana wata godiya ko kuma wani abu makamciyar kyauta.

"Kai kuma Kalil ka kiyaye ni  wallahi, kina iya tafiya yanzu.

Idanuwan Kalil har wani irin ja yayi daga kasa, jijiyoyin kansa kuwa gabaki ďaya sun mim miki tsabar yanda ransa ya baci.

Murmushi suhaila tayi tace, "babu damuwa yaya haidar Nagode sosai da taimakon da kukayi min ,amma inaso kasani zuwa gidan mu, ko kuma Godiyar da iyaya na zasuyi muku ba yana nufin shine sun biya ku ladar abinda kuka yimin ba, abadan basa da abinda zasu biya ku dashi, bazan tursasa muku ba idan kuna da Ra'ayi kuna iya zuwa idan ba kwada shi Nina tafi.

Tana kaiwa nan tafita daga ďakin,ďago jajayan idanuwan sa Kalil yayi ya Kali haidar wani irin kwarjini yayi masa gabaki ďaya yaji bazai iya ďaka koda kafar Saba.

Kwanciya haider yayi Don yasan babu inda Kalil zai tafi duk da kuwa tsananin bukatar haka da yake.

Jin shiru babu wanda yafito yasa ta share hawayan daya gangaro mata ta wuce.

*******

Gayun ridwan kuwa abakin hanya suka wurga suhaima sukayi tafiyar su, cikin sauri ta Kwance idonta don kuwa tun acikin mota suka kwance mata hannun ta, sosai jikin take rawa tana kiran sunan ridwan dan ita Atunanin ta tafiya sukayi dashi.

Tare adaidaita tayi ta nufi gida zuciyar ta cike da tsoron abinda zai biyu Baya, tana shiga ta same daddy da hajiya A zaune afalo wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke  sannan shige ciki.

tasowa daddy yayi ya rungume ta yana shefe bayan ta, aikuwa kamar dama jira take nandanan ta fashe da kuka,cike ďa tsantsar kulawa yake tambayar ta, "menene ki faďa min Waya tabaki?

Tsagaitawa tayi da kukan tace, "babu abinda akaye min daddy kawai sona ke acanza min makaranta, daddy W A E C  nakeso rubutawa.

"shine kika kuka? Maza share hawayan ki indai wannan ne angama.

"Nagode daddy.

Shigewa Dakinta tayi Tana addu'ar ALLAH yasa kar suyiwa ridwan ďinta komai.

******
Mummy kuwa gabaki ďaya ta rame tayi baki  kullum cikin kuka take da Addu'a ALLAH ya baiyanar da suhaila koda kuwa gawar  tane.

RAINA 2020Where stories live. Discover now