7

629 37 0
                                        

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@mamsuhaimerh

*VII*
             "ku fitarmin Mana kun tsayamin a ka"

Fita mukayi Ina ri'ke da flask d'aya Yana ri'ke da d'aya,ya Usman da uncle Hashim na gani tsaye gefen motar sunata yabawa,gaidasu nayi da kyar sannan na wuce cikin sauri

Ina shiga tsakar gida na ajiye flask din a gaba na zuba Masa Ido nayi tagumi,bud'e miyar nayi na dandana,Ni nasan ban saka tafarnuwa a ciki ba

Kuka sosai na fara Ina tuna maganganun hajiya meyasa takeson saka iyayena a ko yaushe

Maimakon naji Ina bu'katar cin abinci sai naji abincin ma ya fit daga Raina,wainar da na kusa rasa maki Mai yawa a kanta gatanan hajiya ko tabawa batayi ba ta dawomin da ita

Palour na koma na hau kujera na kudundune Ina kuka,yanzu haka zanci gaba da rayuwata?me Zan yiwa hajiya ta Soni ko ta Dena min wannan tsanar

Qarar wayata naji Ina dubawa Naga mamana,goge fuskata nayi na saita kaina sannan na amsa Kiran,dukda haka Ina magana tace

"Mura kike ne naji muryanki haka?"

"Eh mama,yau da safe na tashi da ita"

"To Allah ya sauke,Kisha magani,ya abokan zaman naki?"

Dariya na kakalo nace

"Kai mama kaman wasu kishiyoyina?duk suna lafiya na dai shiga mun gaisa dasu"

"To yayi kyau,a zauna lafiya sannan cikin mutunci,ya ita Mahaifiyar tasa?"

Ambato hajiya da mama tayi kadai yasa naji kwalla na neman zubomin

"Itama Tana lafiya Lau,dukkansu alhamdulillah basuda wata matsala dukda Yan uwane"

"To Allah ya Kara muku zaman lafiya,ga yayanki yace na gaidake"

"Mama ki fad'a Masa fushi nake dashi,tunda yaki zuwa ganina"

Dariya mama tayi tace

"Wannan ragon?to ai yana Nan saura kiris yayi Kuka saboda Babu ke a gidan,har wani rama yayi a kwana ukunnan"

Murmushi nayi inajin kewar gida na kamani nace

"To mama kice shima ya fito da Mata kawai a kaishi ya cika Miki gida,ai na kusa zuwa insha Allah"

Sallama Saleh yayi na amsa,mama na Jin haka itama tamin sallama ta katse Kiran

Gyara zamana nayi ya zauna gefena,hannunshi ya Sanya a kafadata ya Jani jikinsa yace

"Kuka kikai ko?"

Shiru nayi Domin ba sai na fad'a ba daga ganin fuskata yasan Kuka nayi

Shafa bayana yake cikin lallashi yace

"Laifina ne da ban sanar dake hajiya Bata son tafarnuwa ba,I'm sorry,nasan hajiya nada fad'a Amma kema duk abinda zai hadaki da ita ki kauce Masa kinji?"

Gyad'a Kai nayi Domin na lura ya fara goyon bayan mahaifiyarsa,hawaye ne ya sake gangaromin nace

"Baka sanarmin yanayin da zan shigo ba da na shiryawa tararsa tun a waje,kaga fa duk Yan uwanka basa Sona"

Dagoni yayi ya d'aura hannunsa a lips Dina yace

"Karkice haka star shine,Yan uwana Ni suke Jin haushi saboda na'ki karbar zabin da hajiya ta yimin,Amma a hankali zasu karbeki na maki wannan al'kawarin,Dan yimin dariya Mana nagani"

Dariyar ce ta kwacemin yaja kumatuna yace

"Ko kefa Yar matata ta kaina,zanje shago yayanki ya kirani yace ya koma gida,yara ne kawai a wurin"

NAYI DACE.Where stories live. Discover now