42

458 33 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@ mamsuhaimerh

        *Wannan page d'in kyauta ne ga NAYI DACE FANS group, thanks for your support 🥰🥰*
*41*
            Hira ke tasowa yayin Danna doshi palon, shiga nayi tareda sallama na tsaya cikin mamaki nace "Aunty Aisha?"

"Oyoyo 'yata sannunki da dawowa" Aunty Aisha ta fad'a tareda hugging d'ina, kallona su Raudah sukayi amal tace "wai dama aunty B kinsan Mum?"

"Ta sanni mana, rashin zumunci yasa baku san juna ba, Bilkisu ya kike ya aiki?"

"Lafiya lau Aunty Aisha" na fad'a ina kallon Aunty, meyasa bata cemin su Raudah yayan Aunty Aisha bane? Dukda banida zumunci ta 'bangaren dangin mahaifina, ko taron sallah da akeyi ban fiye zuwa ba haka nan nake jina out of place duk da suna nunamin gata ba laifi, amma ban ta'ba ganin su Raudah ba a d'an zuwan da nakeyi sannan Aunty Aisha ma zan iya 'kirga sau nawa na ganta, kusan dai duk bamuda zumuncin.

Mun gaisa sosai anan na san aikinta ita babbar likita ce wanda kasancewata mai aikin lafiya ya sake birgeta, kamar bata gajiya da surutu hakanan muka zauna muka yita yi tsakaninmu.

Sai bayan magrib muka nufi kar'bo d'inkin mu, gidan Mama muka nufa anan muka bud'e kayan muka duddubasu, d'inkin yayi kyau sosai dukda ansha kud'i, 5000 zuwa 6000 a kan kowane set d'aya.

Washegari ji nake kamar zanyi kuka saboda kewarsu, zuwansu ba 'karamin d'ebe min kewa tayi ba yanzu zasu tafi su barni da kad'aici.

D'aga musu hannu nake ina danne hawayena yayin da suka shige departure, kiran Raudah na gani na d'aga tace "we will miss you too Bilkisu, amma tunda kinyi al'kawarin zakizo mana dan Allah karki karya al'kawari muna nan muna jiran ki".

"INSHA ALLAH zanzo Raudah Allah ya kaiku lafiya".

Jiki a sanyaye na juya, tun kafin na bar airport d'in naji wani emptiness na dibana, ni ba wata 'kawa ba a yanzu da zanyi shawara da ita, tunda nayi aure dalilin matsalar gidan Saleh tasa na dena Jan 'kawaye a jiki ina tsoron abinda zasu zo su gani, a haka har na yanke ala'ka ta da duk wata 'kawa tunda friends d'ina na makaranta sukazo Hajiya ta bani kunya a gabansu, ga sa'annina sunyi aure, haka dai zanci gaba da danne damuwata har Allah ya kawomin mafita.

************
*SALEH*

Saleh ya saukar da kansa ga Hajiya, matu'kar dai hakan zai bashi abinda yakeso to zaiyi komai da tace, sati biyu kafin kai lefe ta takura masa yaje ya sake ganin Hadiyya, wannan karon da rana yaje.

Zuba mata ido yayi cikin mamaki, meyasa Hajiya zata masa haka? Yaya zata had'ashi da wannan 'karamar yarinyar?

Hadiyya yarinya ce da bazata wuce 17 ba, dan kyau tanada kyau irin black beauty d'innan idanunta farare ne 'kal gasu manya, d'auke kansa yayi yayin da ya kalli idanunta.

Dukkansu sunshi shiru tana tsugune tana wasa da 'kasa da tsine shi kuma yana tsaye, dur'kusawa yayi taja gefe yace "kin gama makaranta kenan ko?"

Gyad'a kai tayi yace "wacce?"

"GGSS goron dutse" cije le'bensa yayi cikin bacin rai, meyasa Hajiya zata ce masa yarinyar ta gama FCE alhali secondary kawai ta gama, sannan kud'in da take fad'a shi bai ganshi ba dukda wannan ba damuwarsa bane, amma meyasa bazata nema masa yarinya me hankali ba?

Tambayoyi yaci gaba da mata tana amsa masa, shekarunta kamar yanda ya canka 17, saura 5 months tayi 18, su bakwai ne a gidansu itace auta, aurensu kuma ita bata ma san mene so ba balle tace tana sonshi ko bata sonshi, lallai Hajiya ta had'a masa aiki, yaushe zai gama rainon yarinyarnan balle har yayi tunanin had'a ta da Bilkisu? Haka dai ya kare mata kallo ya tattara ya koma.

Part d'in Hajiya ya nufa bayan sun gaisa yace "Hajiya naje na ganta amma 'karamar yarinya ce fa".

"Eh to amma ai ta isa aure, tunda iyayenta sun baka ita ai shikenan ko? Nasan zaka iya ri'keta shiyasa na nema maka aurenta Kuma su iyayensu a haka suke aurar dasu 'kanana abunsu".

Shiru yayi domin yasan bashida wani choice, har ya fita ta.kirashi tace "karka mata, saurin.yin aurennan shine saurin dawowar matarka".

Shiru yayi mata ya fita domin a yanzu kam baisan ma direction d'in da rayuwarsa take bi ba.

Bai fasa zuwa wajen Bilkisu ba ita kuma Bata fasa wula'kantashi ba, a haka har lokacin aurensa yayi, yayi komai kamar ango saboda al'kawarin da Hajiya ta d'auka na ta janye sai Hadiyya ta samu ciki, matu'kar ya kuka da ita kamar matarsa cikin so da kulawa to a wata uku zata barshi ya dawo da Bilkisu sannan tsyi al'kawarin bazata sake shiga harkar Bilkisu ba idan yaga dama ma ya nema mata gida a waje ta zauna, amma kar yayi tunanin zata so Bilkisu, hakan ya amince saboda yanda soyayyar Bilkisu ke dawowa sabuwa fil a kowacce rana, yayi missing d'inta sosai har abin ya fara affecting rayuwarsa.

An kawo amarya amma ko kallon inda take baiyi ba, kwanciya yayi yana kallon ceiling tareda tunanin Bilkisu a first night nasu, da second da duk sauran rayuwar da sukayi takaici da nadama sunyi masa yawa, Hawaye ne suka zubo masa meyasa ya saki Bilkisu? Meyasa ya aikata babban kuskure a rayuwarsa wanda bai ta'ba aikata irinsa ba kuma yasan zai dad'e yana nadama, idan ma Bilkisu bata dawo gareshi ba to zai 'kare rayuwarsa yana nadama akan hakan.

Kuka yaji a gefensa ya juya cikin mamaki, baiyi tunanin har yanzu batayi bacci ba, zama yayi itama ta tashi ta zauna kafin ya bud'e baki tace " saboda baka sona shine zaka kwanta kana kuka? Ai ba haka aka cemin anayi ba idan bazaka min abinda miji yakewa matarsa ba kawai ni ka sakeni na koma gidanmu".

Dafe kansa yayi, matsalar auren yara kenan ita a karatun auren abu d'aya aka sanar mata?, Sauke numfashi yayi tareda goge fuskarsa yace "ki kwanta kiyi bacci banajin dad'i kema kuma nasan a gajiye kike".

hard'e hannayenta tayi a 'kirji tareda turo baki batada niyyar kwanciya, wata harara take wurga masa, dafe kansa yayi domin ta fara Sanya masa ciwon kai yace "Hajiya kuma da wata matsalar ta had'a ni?"

"Da matsalar mata mana, au nice ma matsalar bayan na taimaka na aureka? Hajiyarnan taka fa zuwa tayi ta dinga ro'kon umma akan a baka aurena banda haka ai kai ba sa'an aurena bane ko? Inaga ma bakada lafiya shiyasa babarka ta had'a aurena dakai gashinan kazo ka zubamin ido kamar ba namiji ba".

NAYI DACE.Where stories live. Discover now