*NAYI DACE*
Maryam💕
Wattpad@mamsuhaimerh*25*
*Alhamdulillah I am back, nayi missing dinku sosai fa, alhamdulillah na gama exams saura fatan sakamako mai kyau, Kar dai ku manta, Ina bu'katar addu'o'inku masu albarka.**Kafin naci gaba Zan danyi recap na abinda ya faru a baya saboda wad'anda suka manta, though it breaks my heart ace kun fara manta labarinnan😣😣😣😣😣😣*
RECAP
*Bilkisu yarinya ce da ta taso a gidan yayar mahaifiyarta, mahaifinta ya rasu tun kafin haihuwarta mahaifiyarta kuma ta rasu bayan ta haifeta, hakan bai sanya Bilkisu ta taso a maraici ba, hasalima ta taso cikin gata kasancewar yayar mahaifiyarta d'anta d'aya Namiji a duniya, jabir.*
*Kamar yanda al'adar gidan su jabir take kowacce mace ana aurar da ita ne ta hanyar auren zumunci, lokacin da auren bilkisu ya taso baba, wato maiahifin jabir ya za'ba ma Bilkisu d'an abokinsa da ya kammala karatunsa a 'kasar Russia, saidai d'abi'ar sa da halayensa sunsha ban-ban da yanda Bilkisu take so.*
*Hakan ya sanyata shiga damuwa sosai, abokin yayanta SALEH shine yake rarrashinta da kalamai masu sanyaya zuciya, hakan ya sanya ta fad'a soyayyarsa ba tareda ta shirya ba, bayan wasu al'amari da suka faru Bilkisu ta bayyanarwa iyayenta Saleh takeso, babu jayayya aka aura mata shi.*
*Tun ranar da Bilkisu ta Sanya 'kafarta a gidansu Saleh tasan cewa she's not welcomed, Mahaifiyar Saleh ta tsara Masa l auren 'yar 'kanwarta SULTANA, inda Saleh ya bijirewa umarnin hajiya saboda BILKISU, hajiya da sauran Yan uwan Saleh sun d'auki tsana sun d'aurawa bilkisu, haka alamura suka yita faruwa marasa dad'i har SULTANA ta samu ciki ta haihu ta sake samun wani, takura da natsawa sun yiwa bilkisu Yaya yayinta dangin mijinta ke zargin planning tayi domin karta haihu tana karatu.*
*Bilkisu tayi gwajin fertility anan ta samu most shocking news of her life, cewa bazata iya samun ciki ba saidai a Mata IVF, bayan wannan abun ya faru SULTANA ta d'auki yarta da ta Haifa ta baiwa Bilkisu ba tareda sanin kowa ba sai mijinta , duk yanda dangin Saleh sukaso ya sake aure ko ya saki bilkisu ya'ki amincewa, karshe suka had'ata da shaid'anu sannan sukayi kokarin k'wace Huda daga gareta, a wannan lokaci ne aka sanar musu Huda nada matsalar zuciya takurawa zata it sanyawa a rasata, Kan Dole dangin Saleh suka barwa Bilkisu Huda domin tafi amincewa da ita Kan uwarta, Saleh ya sanarwa bilkisu cewa saura kad'an ya kammala had'a kud'in aikinta suje a artificial insemination...........anan labarinmu ya tsaya*
Masu nema daga farko na rage masu aiki😅😅😅😅😅
*************
"Oh come on...... komai sai kice Huda, to Huda kwakwalwarta wani ri'kon abu zatayi? Infact ba fa wani abu nace ba kawai I just want to kiss you kafin na fita".
Kallonsa nayi tareda kashe ido d'aya, yayimin matu'kar kyau yanda ya turo bakinsa Yana buga 'kafarsa kamar yaro, ni kaina zanso ace yau ranar kawai tamu ce mu wuni muna ririta juna, amma dole ya fita aiki, sannan bazai yiwu na barshi ya lasamin Zuma sannan ya tafi ba, Sarai nasan mijina is a good teaser.
Kwanciya nayi kan love seat dita na tan'kwashe 'kafafuna tareda d'aura 'kafa d'aya kan d'aya, cije le'bena nayi jin ya saki wani sauti tareda matsowa inda nake kwance, kallon bayansa nayi naga Huda tabi motar wasanta bayan kujera.
Sunkuyowa yayi numfashinmu na gaurayuwa, bud'e bakina nayi zanyi magana naji ya hade lips d'insa da nawa, lumshe ido nayi tareda mantawa da duniyar da nake, banajin komai sai hannunsa dake zagaye 'kuguna, muryar Huda naji tana kirana a hankali na tureshi tareda tashi, wani murmushin mugunta yake yi na harareshi cikin wasa tareda bin muryar Huda, ko ya akai take guest room oho.
A bakin gado na ganta tana 'ko'karin shigewa 'kasan gado, d'aukota nayi da motarta da ta shige 'kasan gadon na fito da ita, har yanzu sauke numfashi nakeyi, a tsaye na sami Saleh da jakarsa a hannu yace, "sai na dawo boo-boo na, me zan taho miki dashi?"
