12

588 32 0
                                    

*NAYI DACE*

Maryam💕
Wattpad@mamsuhaimerh

*💫DA BAZAR MU WRITER'S ASS💫*

*We are here to make you happy, smile and to réalized that we are the best among all......DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO.*

12
        Gida na fara shiga na ajiye jakata sannan na fito, part din hajiya na nufa na samu har an fara aiki.

Kai tsaye sashin sultana na nufa, Hira sukeyi nayi sallama, ciki-ciki hajiya ta amsamin na dur'kusa na gaidata.

Amsa min tayi da " lafiya ".

" Hajiya kiyi ha'kuri da abinda ya faru, insha Allahu bazai sake faruwa ba wallahi ba da gan-gan nayi ba, Dan Allah kiyi ha'kuri ki dawo "

Banza hajiya tayi dani kaman ma ba magana nake ba, alamu nayi wa sultana da ta Sanya baki, gyara zama tayi tace.

"Hajiya tunda ta baki ha'kuri ki ha'kura mana, kinga ni gashi yanzu da vest nake zaune muna hira dake baki ce komai ba, to me zai hana itama ki d'an bata chance, tunda bakyaso tana zama hakan zata daina kiyi ha'kuri hajiya"

Ba tare da hajiya ta kalleni ba tace, " jeki naji, zan dawo "

Godiya nayi mata na koma na d'aura tuwon semo miyar kuka, Domin dumame nakeson ci da dare.

Har na gama nayi wankana na zauna ina hutawa hajiya Bata dawo ba shima d'an hajiya bai dawo ba, Ina zaune a gida ni kad'ai har magrib.

Saida akayi magrib tukun saleh ya dawo, sallamarsa naji na tashi cikin sauri na fita,saida na le'ka na tabbata hajiya Bata taho ba tukun na yi masa welcome, duk da haka ban sake ba ina rungume dashi ina duban 'kofa.

Kafad'ata ya ri'ke yace,

" Wai me kike waiwaye ne haka? "

'Daga gira nayi nace " hajiya mana,da 'kyar fa na shawo kanta da taimakon sultana tace zata dawo, bana so na sake wani abun da zai 'bata mata"

Hancina ya ja cikin wasa yace, " kefa akwai matsoraciya, to ai hajiya bazata hana mu soyayya ba ko?"

" Ni dai a'a " na fad'a tare da d'auke hannunsa daga kafad'ata, turo min baki yayi yace

"To zamu yi magana anjima".

Gaba yayi nabi bayansa, gani nayi yayi sama nayi zamana, da alamu ya d'an hau, to hajiyarnan dai gyatumarsa ce

Jallabiya ya Sanya ya fita masallaci sallar isha, yana fita hajiya na shigowa.

Tashi nayi cikin hanzari na dur'kusa na gaidata, zama tayi Kan kujera nace,

" Hajiya a kawo miki abinci?"

"Naci abinci " ta fad'a tare da gyara zamanta kan kujerar, remote na d'auka na mi'ka mata domin takai channel d'in da take so na nufi kitchen na d'aura d'umamen tuwona

Fitowa nayi da man shanu na da yajin daddawa, Ina ganin idon hajiya Kan tuwon a raina nace kin ma kanki

Ina fara cin tuwon hajiya ta tashi ta nufi d'aki, da alamu 'kamshin man shanu ya isheta.

Kafin na 'kare Saleh ya dawo, zama yayi muka ci tare muka sake 'karowa, saida mukayi fam tukun.

9:30 nayi ma hajiya sallama na wuce na kwanta,tashin asuba nayi na hau aiki da shirin breakfast, ina gama wa na d'aura na rana domin sai yamma zan dawo.

Har 10 hajiya bata fito ba, kwankwasa mata 'kofa nayi na sameta tana azkar, gaisheta nayi bata amsa ba na ajiye mata kwanon tuwonta nace

" Hajiya yau sai yamma zan dawo amma nayi girkin rana, idan ya dawo zai fito miki dashi "

NAYI DACE.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora