Kowa ya Raina Tsaiwar wata........Gajeren Labari

238 10 0
                                    

#KalubaleGareku #MatanAure!!!

Tin sa'in da yaji sanarwar data gabata a labaran 12 na gidan radion freedom.
Cewa gwamnati tabada umurnin lockdown a birnin kano da kewaye, ma'ana dokar taƙaita zirga-zirga  har na tsawon mako guda. Hankalin sa yake a tashe, kasancewar sa talaka me ƙaramin ƙarfi ba me wadata ba.

Gwamnati ikon Allah tunda tace ba shiga ba fitar nan fa zaman gida ya kama ƴan maza!.

Tun safe yake kwance a ɗaka yana ta fama da karanta wasiƙar Jaki sabili da ya duba aljihunsa yaga bashi da wasu wadatattun kuɗaɗe da ze iya yiwa iyali tanadi har na tsawon mako guda. 😫😫😫

"Dubu Goma sha shida" ya faɗa. Wannan shi ne karo na takwas da yake daɗa ƙara tisa kuɗin, kamar wanda akaiwa wahayi inya tisasu ba ƙaidi zasu karu.

Ganin dai ba shi da wata mafita su ɗinne dai ba ƙaruwa zasu yi ba, tasa  ya miƙe cikin sanyin jiki yayi waje.

A tsakar gida ya tadda Zulfa tana yiwa Walid wanka. Cikin sanyin murya yace "Zulfa na fita sai na dawo".

Ciki ciki ta  Amsa "Adawo lafiya."

"Allah yasa" ya amsa mata yana mai ficewa.

Cikin ƙanƙanin lokaci ya iso bakin kasuwar rimi,
Kasancewar gidan sa a KABARA yake.

Sai da ya fara siyan shinkafar sa me kyau ƴar Hausa kwano biyar, kana ya sai wake mudu ɗaya. Haɗi da garin masara kwano uku da taliya leda uku da macaroni leda uku da manja kwalba ɗaya, sai man gyaɗa kwalba biyu.

Ya gangara gurin masu saida kayan miya, yasai na dubu ɗaya da Ɗari biyar. Ya haɗa da kayan ƙamshi irin su Albasa da Citta da ƙanin fari da masoro da ganyen curry da tafarnuwa, da duk dai abinda mace zata nema a madafi.

Yana son siya masu Naman miya anma ganin kuɗin sunyi ƙasa sosai, kuma shi kansa naman yayi tsada yanzu na 1500 ganinsa za ayi kamar an roƙo, shi yasa ya yanke shawarar ya siya masu busasshen kifi. Nan yasai masu kifi banda banda na 2k.

Har zai fice daga kasuwar ya Hangi masu siyar kayan ciki, sun wankeshi tatas seya tuna zulfa nason kayan ciki, an ma gashi ba kuɗi, yana tsananin son matarshi sabili da haka duk wani abu da zai faranta mata shi yake so.

Ya ƙarasa cikin sanyin jiki ya miƙa 500 suka zuba masa a Leda ga mamakin sa, sai yaga sun kyauta masa.

Cikin farinciki ya karɓa, ya haɗe sayayyarsa rankatakab ya tafi gida.

Cikin karsashi yake tafiya Harya ƙaraso gidan
Ya rangaɗa sallama.

"Amin wa'alaikumussalam" zulfa ta amsa tana fitowa daga kicin. "Wash Allah nagaji" ya furta haɗi da zama kan tabarmar da ya gani a shimfiɗe a tsakar gidan.

"Aikin me kai da ka gaji" zulfa ta tanbayeshi.

"Daga kasuwa nake, siyayyar kayan Abinci na mana saboda Quarantine"

Fuskarta ta washe "masha Allah kace yau zamusha dabge!!! Dole kace kagaji Kaji nawa ake figo mana???"😁

Sai da ƙirjinsa ya ba da sauti Das!das!das! Jin abinda ta faɗa, Kana yace.

"Kewai baki duba yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziqi ba kudi a hannun mutane?"

Bata kulashi ba tana faman kicikici da buhun da aka  laftokayan siyayyar ciki, da budewar buhun tahau ɗaɗɗaga kayan tana yi masu kallon Wulaqanci idonta yai tozali da garin masara da Shinkafa 'yar hausa.

Cikin sauri ta ɗago tana Huci tamfar wata zakanya, #Kabiru!!! Ta kira sunanshi da wani irin sauti.

Cikin mamaki yake kallonta jin yau takira sunanshi gatsau, yauko Abban Walid ɗin babu.

kowa Ya Raina Tsaiwar wata........Where stories live. Discover now