kowa ya Raina tsaiwar wata

46 4 0
                                    

Kasancewar anshiga quarantine yasa,data fito waje titin kamar anyi shara.
"Kabara zuwa jakara bola! Dankari makari,abinfa basauqi" tafada yayinda take ratsa lunguna dan kaucewa 'yan sanda.

Abinka da anguwa irinta cikin badala,daidaiku take gamuwa da 'yansandan sede duk wanda tacikaro dashi, takan kantara masa karyar rasuwa akai mata hakan tasa suke rabuwa da ita.

Futufutu  ta isa jakara bola,lokonsu ma fetal kamar anshare mutane se daidaiku.

Faramfaram ta uka gidan hadi da rangada sallama,kannenta ne suka amsa mata. Suna ga aunty ga aunty bata bi takan marabar da  yaran ke mata ba tace "Ina Ayyah?."

Madafi murja ta gwada mata da hannu,can ta tsinkayi mahaifiyar tata ta dukufa tuka wani bakin tuwo. wanda base an tsaya maka tarjama ba tuwon bakar dawa ce,

Ta karasa da sassarfa,ta nemi kujera 'yar tsuguno ta zauna gamida kwanto waleed daga bayanta.

"Ina yini Ayyah" tace
Ayyah tadube ta da mamakin ganinta a dede wannan lokaci. kana tace "lafiya lau"
Tadora dafadin keko '' 'yar nan lafiya?" Dashike 'yar farice bata fadar sunanta.

Zulfa ta yamutsa fuska kana tace "lafiya ba lafiya ba nida kabiru ne."😏

Ayya tace toh "sarkin korafi me kumakabirun yaymaki? Kowacce mace fa dakika gani Hakuri take agidan mijinta, bakome zaa maki ki kwaso kafa ki taho gida faramfaram ba."

Zulfa tace "Anma Ayya kya tsaya kiji abinda yamin kamin kifara fada."

Ayya tace "toh inajinki"

Nan zulfaa ta kwashe komi, ta fadima Ayyah harda karin gishiri.

Ayya wadda tun da zulfaa tafara magana  ta sankare a zaune,Haushi mamaki takaici duk ya kasheta a zaune.

Cikin fishi da tsananin bacin rai, Ayyah Tace "bantaba sanin baki da Hankali kuma kedij gabuwa bace me raina baiwar da ubangiji ya huwace mata ba seyau."😡😡😡

"Nafahimci in dadi yaiwa mutum yawa,se yace Allah kashe ni."

"Aikafin aidakai kayi dakanka,kodashike duk kokunnenka yayi ya tabarma bazakaji radar daake maka ba.

Inba rashin hankali da rashin tunaniba  irin naki sekiduba daga wane irin gida kika fito!"

Tafada tana aikamata harara.

Ta dora dafadin inba samun wuri ba irin na diyar talaka

kowa Ya Raina Tsaiwar wata........Where stories live. Discover now