Kowa ya Raina tsaiwar wata

79 5 1
                                    

#ƙalubaleGarekuMatanAure

Wattpad@Qeenajanah
Write Queenjanahstar

Tabbas zuwa yanzu,zulfa'a tayi Nadamar duk wani kutsu data aikata ta. Saboda duk wanda ya santa a kwanakin baya inhar ya ganta a yanzu dole ya jefeta da tanbayar ko tayi jinya ne???

Babu ciwo babu komi illah tsabar yunwa da wahala,ga azumi gashi yayin da kakai azumi bawani abun maƙwalashe dazakaci ko wasu ƴaƴan itatuwa sede ka jibgi tuwo, tuwon ma na dawa baƙi ƙirin da kunun tsamiya su zulfa'a bana anyi bautar Ubangiji. Duk Ta rame tayi baƙi ta jejjeme ta ƙwarjale,jikin da take taƙama dashi duk ya bushe. Nikaina saida ta bani tausayi.

yauma de kamar kullum tana zaune a tsakar gida tana aikin nata na tunani da ta saba, Wanda zuwa yanzu ya zamar  mata jiki.

Duk da ba tun yau ba ,ta daɗe da gundura da cimakar gidan nasu. Anma yau lamarin yafi kullum hayaƙa. Jitake yau in aka sha ruwa taci tuwon nan zata iya samun matsala😭.
Lokaci daya wani tunani ya ɗarsu a ranta.

Batasan sanda ta saki wani busasshen murmushi ba. Ahankali tace *Iklima gwagwuɗa*

Cikin karsashi ta miƙa hannu taɗau wayar ta,hadi da lalubo sunan *Gwaguɗa* ta latsa kira... Dake ba ko ƙarfanfana a sim ɗinnata ringing biyu tai ta latse kiran dama plashing ne tasan dole zata kira inde har tagani, cikin abinda befi daƙiƙa Arba'in ba wayar ta takama neman agaji. Da hanzarin ta ta ɗauka gami da furta "Assalamu alaiki shegiyar gari,dama talaka na Ganin ku?" Daga ɗaya ɓangaren iklima tai murmushi sannan tace "Uhm talakan inya tuna damu ze gan mu mana kinsan bama nacewa a inda ba'a damu damu ba" ta karshe maganar da gugar zana.

Zulfa'a ta katse ta "ke ni banason baƙar magana,yakike yagariyajindadi kwana biyu,ai naɗauka ma bakya ƙasar. Kawai de gwada kira nai sena ci sa'a kuma kina nan ashe."

Iklima taja dogon tsaki "mtssw!!!" Kana tace "Kede bari ƙawas corona ko jaraba!!! Ai tunda cutar nan ta ɓulla a turai Darling ya kansile duk wasu harkokin sa dake ƙasashen ƙetare. Badon wannan cutar ba da yanzu haka muna Faransa sede Maganar dawowa Saboda Sallah kinsan ɗan gargajiya ne baya iya idi a wata kasa inba Lanjeriya ba."🤣🤣🤣
Ta karashe maganar tana dariyar shaƙiyanci.

Zulfa'a tai murmushi tace "Hmmm Allah ya shiryeki ƙawata.kana tace ke bakisan meyafaru daniba ko??? Wlh ina gida yau kwanana Ashirin da huɗu daga kawo ƙara kabiru yace in zauna in huta"
nande ta labar ta mata komai yadda lamarin ya kasance.

Daga ɗaya barin *Iklima gwagwuɗa* tasau wani boyayyen murmushi haɗi da girgiza kaman ta taka rawa don daɗi,
Anma dake ƴar bariki ce se ta lanƙwashe murya cikin sigar tausayawa tace "A gaskiya lamarin bemin daɗi ba ƙawata yanzu shi kabiru duk irin Haƙuri dakike dashi na halin babu da fatarar nan tashi,da wannan zai sakamaki???"
Sedatayiwa wayar gwalo sannan tacigaba, "gaskiya ba'a kyauta maki ba yaci amanar soyayya! In banda abinshi shida yatsinci dami akala, kyawawa irinki aibaa masu wulaƙanci ko ya manta irin gwagwarmayar dayai  kafin yakai ga Mallakar ki??? Irin ku ai waina ne rububinku ake bakwa kwantai!!!"

Zulfa'a tai shiru tana sauraren  jawabin ƙawar ta mai kama da zuga,ta wani fannin tanaso ta gasgata maganar ta na cewa ita me kyau ce tabbas tasan ba ƙarya tanada kyau. Anma kuma tana da sanin cewa a wannan gaɓar itace babbar mai laifi. Kabiru bayada laifi kona sisin kwabo, don haka itade yanzu duk bawannan zugar ce agabanta ba mafitar ɗa'ami take nema watau *Abinci*

Cikin sanyin murya zulfa'a tace "Nifa ƙawata duk bawannan ya damen ba kamar halin, ƙaƙanikayi dana shiga agidannan ba cimar arziki se baƙin tuwo Abinda kika jima da sani ne base na zauna maki dogon zance ba sister na tagayyara da azumin nan,mafita nake nema!"

"Anzo wajen" *Gwaguɗa* ta furta a zucciyarta,
Anma a fili se tace.

"Kina nufin haka kika taho gidan tiikk,tsiren Kabo bamai bs ba yaji???" 🤔🤔
Zulfa'a tace"Wallahi haka nadira bako asi"  "yanzu yakenan za'ai?" Iklima tafaɗa tana jiran taji abinda zulfa'a zata faɗa.

Cikin sanyin murya zulfa'a tace "Abin da kika saba shi zakiyi,don wlh inbaki taimakan ba yau kam Rayuwa ta na kwalekwale!"

*Gwaguɗa* ta saki murmushi me sauti kana tace "ki jirani ina zuwa"

Tsakanin jakara da Brigade,tafiya ce ba ƙarama ba,kuma gashi gari a garƙame ba shiga da fita  lockdown.
Anma duk da haka batai mamakin jin cewa ƙawarta ta tace gatanan zuwa ba saboda ta kwana da sanin ba da ƙana nan mutane take mu'amala ba, duk wanda ma yai gigin Tare ta koyai  mata gar~gar ze iya yin ta aikin sa.

Cikin Abinda befi minti Arba'in ba, taji sallamar iklima a tsakar gida suna gaisawa da Ayya.

Lokacin da Gwaguɗa tai tozali da ƙawartata seda ta murza idonta sabili da a tunanin ta bai gani da kyau seda ta muttsike shi Sannan ta yarda ba gizo yake mata ba wannan yamutsorar matar dake tsaye gabanta itace ƴar gayun ƙawarta zulfa'a a Wani shuɗaɗɗen zamani daya wuce.

Cikeda Al'ajabi take duban ta,seda suka samu wuri suka zauna kana  ta

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 25, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

kowa Ya Raina Tsaiwar wata........Where stories live. Discover now