kowa ya raina tsaiwar wata

89 5 0
                                    

Mamaki be kara kasheshi ba seda yaga, ta saki ledar shinkafar tushhh!!! Leda ta fashe shinkafa ta watse.

Kana ta cigaba da magana "yayin da mazaje ke kokarin farantawa iyalan su,shine kai don kuturun wulakanci. ka rasa abin da zaka kawomin se shinkafa 'yar Hausa, 'yar hausar ma me shegiyar tsimta jaka!!!"

Ta fada tana Huci kamar wacce tai dambe!.

Bata ko bari yayi magana ba tacigaba.

"Dan naman da zaka siyo,mudan sami chanji a tukunya ma ya gagara. shine kaje ka kwason kifi,kifin ma  banda! Sabida ga kura Ka ijiye ko? Hande miwadi!!!! Yau ina ganin abinda ya isheni kishiya tara rana daya.......🤔🤔🤔

Izuwa yanzu kuma kabiru ransa yafara baci l,da irin maganganun da zulfa'a ke saki na rainuwa darashin godiyar Allah.

Cikin fishi shima yace "kinsan de talaka ne ni kuma Allah yaga ni iya karfina kenan. Zulfa kinsan ni meson farincikin ki ne, babu yadda za'ai inhar inada halin siyo maki 'yar gwamnati kuma naki.

Kana ya sassauta murya cikin sigar lallaashi yace.
"In kika duba da aiba haka nake ba samunne yaja baya kasuwa tayi nauyi zulfa,inbanda abinki kuma kifin ma inawa lefi da babu aigara ba dadi. Kumama nasiyo miki kayan ciki ninayafe kici ke kadai keda yara.

Ya karashe maganar cikin murmushi.

Zulfa'u wadda tundayafara magana, take kyabe baki tana kallon sa a dage.

Tace "toh Al'alata shugaban matalauta, jagoran talakawa!!!
Har wani qafulli kake  nan kayo siyayyar kayan Abinci. niban yarda ma shinkafar nan siyota kaiba,nafi tunanin sharar kanfanin su Husaini me United kura ce nasan yaron akwai tausayi kila da sukai shara kai suka bamawa."

Tafada cikin izgili.
Ta cigaba,

" nikam banyi sa'ar miji ba,kaiko kishi ba zakai kayi koyi da mijin maman Unaisa ba. Bawan Allah nan yau inagani buhun shinkafa yadire mata yar gwamnati,da gallon din manjada mangyada ga kwalin spaghetti ♨ gishirima kwali sugar bahu guda, namako rago akayanka akasa afreezer kaji kam ba'a maganar su.
Abinde se wanda yagani,saboda wulaqanci dan  karamin buhun shinkafar ma da kake siya samfarin mayunwatar ma kadena, kadawo awu. Babun taka memakon tai sauqi abu se dada gaba yake cigaban me hakan rijiya. na tabbata wannan siyayyar cewa zakai mu cancana harcikin azumi."😡

Kabiru yai galala yana kallon matar,tasa kamar yaga manzon mutuwa.
Zuwa yanzu lamarin matar tasa,ya wuce acemamaki ya fara bashi tsoro.

Kamar ba Wannan zulfa'ar da yasani shekarun baya ba,mesonshi da kaunar sa me tattalinsa  da tausayinsa. Irin soyayyar da suka zuba zamanin samartakarsu har wani laqabi ake masu, #laylamajnun
Anma dubi cikin shekaru dabasu gaza hudu da 'yan doriya ba abar kaunar tasa ta chanza masa. Zuwa yanzu 'ya'ya biyu ubangiji ya azurtasu dasu kuma duk maza waleed da Hameed.

Chanjin zulfa'a yasamo asali,tun a haihuwar ta ta biyu.
Kowacce haihuwa da irin  Tagomashin da take zuwa wa mutum,toh haihuwar waleed abin se godiyar ubangiji.
Don Alokacin kasuwa tayi nauyi komi yatsaya cak, Dakyar ya ququta yasai wani dan magyazon Rago.

A ranar suna tunda tai tozali,da wannan  dan duqurqushin rago tadinga yarfa ruwan bala'i,wai ita dan ya rena ta zekawo mata wannan kafi zurun a natsayin Hakika! Se kawayenta sun renata.

Dakyar da makyarkyata wata goggonta,ta shawo kanta sannan tai shiru.
Tundaga wancen lokacin yau wata Ashirin kenan, matar tasa ta rikide takoma masa monster.

Sabili da kullum jiya iyau lamarin samun nasa se godiyar Ubangiji.

kowa Ya Raina Tsaiwar wata........Where stories live. Discover now