Kowa ya Raina tsaiwar wata

40 3 0
                                    

"Inake ina raina wannan garar da mijinki ya kawo maki, toh wallahi ahir dinki kishiga hankalinki. Kifarka  daga mafarkin dakike,inma kawayene suke zugaki tabbas zasu kaiki su baroki."

"Toh waini dakika kwaso kafa kikataho,uban mezamumaki? Koso kike mukirashi mumai fada akan bekawo miki kayan dadi kinciba? saboda ga 'yar sarkin Santanbul!!!🤔🤔🤔

"Kinfi kowa sanin halinda mukeciki agidannan ci uku tuni ya zama tarihi a cikingidannan.
Babanki bamai karfi bane,seyafita yake nemowa randa kuma yafita ba sa'a haka mukezama. Sanin kanki ne ina kokari wajen sana'a kowacce irice,anma jarin ba inda yake zuwa daga nafara zan durkushe,saboda ba a tsare maka cikinka ba. Ba'a sabo da wahala anma mukam munsaba."

"Shikansa wannan tuwon da kikaga inayi yau, dabadon Alhajinamadi ba da sede muci Nade da mai (Yunwa)"

Nanda nan zulfaa tafara zufa,

Ayyah tace "kike kiftamin ido yana kwarto,ai gaskia ce nake sake jaddada maki,saboda duk abinda nake fada din ba bako bane a gareki."

"Yanzu haka miyar cin tuwon tundazu na kada ta ba maggi,banida ko ficika babanki ko anini baya magani.
Allah de yasaka ma Alhajinamadi da alkairi bahu guda yaba babanku na nikakkar dawa da rabin buhun hatsi,da sukar kinga har azumi yakare bazamu shiga kakanakayi ba."

"Sede kuma anemi na cefane,kiyiwa kanki kiyamul laili kikoma gidanki sawunki a likkafa......."

Gyaran muryar da akayi ita ta katsewa ayya doguwar laccar datake,

Mal hamidu ne ke fitowa daga bayan gida,fuskar sa murtuk ba alamun wasa.
Ga dukkan alamu yaji komi da suka tattauna,

Ya karaso a hankali,kana cikin fada yace "Ashha kinbani kunya,kuma kinbani mamaki. Albasa sam batai halin ruwa ba bahaka mahaifiyarki takeba. Uwarki mutumce mai godiya anma kekam sam bansan ina kika samo wannan muguwar halayyar ba."

Ya Dora dafadin "kuma yaji bade a gidana ba, maza kikoma gidan mijinki tunkafin nasaba maki."

"Yamasan kin Taho?"
Ta girgiza kai dasauri

Haushi ya kara kama mallam hamidu,sannan ya zura hannu a aljihu ya danna lambar kabiru.

kowa Ya Raina Tsaiwar wata........Where stories live. Discover now