1

1K 12 0
                                    

💕 *TAWA KADDARARCE HAKA*💕




*Na darlinh_princess*💕


*free page 1*





Garin katsina garine mai girma,garine wanda yatara mutane kala² acikinsa,garine na yan boko da masu kudi,akwai wata anguwa wadda ake kira kwado,wanda duk mazaunin katsina yasan dazaman wannan anguwa,wata matashiyar yarinyace naga tafito daga gida sanye da hijab da nikaf tanata sauri ga dukkan alamu taso tamakara a islamiya,tasha kwana kenan taji ana kwadamata kira, "Zuwairiya,Zuwairiyya"
Wannan matashiya da akakira zuwairiya tatsaya tare da waiwayawa domin ganin mai kiran nata,kawartace tagani cikin kwalliya takaraso gurinta.
"Zuwairiyya badai makaranta zakiba"
Kallonta zuwairiyya tayi tace,"makaranta zani sadiya ya'akayine ke bazakibane?"
"Aah ni bazani makarantaba yau akwai inda zani"
"Sady yakamata kima kanki karatun tanatsu,wallahi wannan yawon duk banakibane,kinga rayuwa yanzu batada tabbas dan Allah"
"Ya isa"sady tadagamata hannu"haba zuwairiyya ni bansan har yaushane zaki wayeba,gakide afuska kamar wadda tawaye amma azuciya bahakaba,kumama dakike maganar wani miyecan,rayuwatacefa,sai yadda naso nayi da ita,kema nafadamaki kizo kibi wannan hanyar danabi wallahi zakisamu kudi,koba komi zakidinga kashema kanki bukatunki na yau da kullum,amma kullum idan kinason abu sai kinje kincema baba ko mama tabaki,wataran sai sungaji dake,amma idan kina kama naki wallahi babu mai maki wulakanci,ke nafadamaki saima lallabaki daza'a dingayi"
"Humm sady kenan,bazan taba shiga irin wannan rayuwar dakikemin sha'awar nashigaba,kema inamaki addu'ar Allah yashiryaki"

"Amin to,ni yanzu zanwuce idan Allah yakaimu gobe zanzo gida ai"

"To sai Allah yakaimu"sady tayi gaba tashiga motar da aka Parker nan zuwairiyya kuwa tagyada kai kawai tatafiyarta.

Bayan suntaso daga makaranta zuwairiyya ta isa gida,lokacin mamarta tana kitchen tana dafamasu abincin dare,zuwairiyya naganin mamarta a kitchen tayi saurin cire hijab dinta dama doguwar rigace ajikinta,don juwairiya tatsani tasaka kayan daza'a dinga ganin gabanta,bataso shiyasa mafi yawan kayanta duk dogayen rigunane,tashiga kitchen din tanafadin,"mama kawi naci gaba tunda nadawo ke jeki kihuta abinki"
Mama:"aah zuwairiyya kibari nakarasa ai nakusa gamawa daga dawowarki yanzu,ai kyabari kihuta ko"
"Aah mama nide kikawo ainadawo miye amfanina,kawai kije kizamanki"
Bayadda mama ta iya haka tabarnata sanwar ta karasa lokacin har anfara kiran sallahr magriba taje tayi alwala tashige dakinta domin gabatar da sallah.

Zuwairiyya ba itace tafitoba sai bayan sallahr isha'i lokacin babanta yashigo mamarta har tabashi abincin darensa yanaci saigata tafito,tsugunnawa tayi kusa da baban nata tace"baba inawuni,dafatan kadawo lafiya"
BABA:"lafiyalo zuwairiyya Allah yamaki albarka kinjiko"
"Amin baba nagode"
"Baba nifa bakacemin Allah yamin albarkaba"inji yayan zuwairiyya".
"To Allah yamaku albarka baki dayanku"suka amsa da amin.

Nan suka zauna suna fira sunacin abincinsu har lokacin bacci yayi kowa yatashi yashiga muhallinsa domin kwanciya.

Washe gari tunda safe zuwairiyya tatshi tagyara gidan tadauramasu kalaci sana tashirya cikin uniform dinta na wtc na Senior dayake ss3 take,sadda tagama duk mutanan gidan nabacci haka tadibi kayan karin kumallonta taci,tana kallon agogo taga 7:15,aiko tasabi skul bag nata, sana tayi hanyar dakin mamanta tana knocking,jimkadan mamanta tabude,tana ganinta tasaki murmushi tace"mama ina kwana"
Mama:"lafiyalo zuwairiyya badai zaki wuceba"
"Eh mama zantafi nakusa makara"
"To kije kicema babanku zaki tafi yabaki kudin makaranta ko"
"Aah mama ainakwai sauran naira dari biyu awurina kawai nayi amfami da ita kyakesa yaita baccinsa,banso natadasa kema dan kada nabar gidan shiru shiayasa nace bari natadake"
"To shikenan zuwairiyya sai kindawo"takara gaba.
Tana fita kamar ance tadaga ido tahango sady natahowa hanyar gidansu itama sanye da uniform,tsayawa zuwairiyya tayi domin takaraso.
Sady nakarasowa tace"ai nadauka baki tashiba"
"Rufan asiri ai kinsan bana wasa da karatu"cewar zuwairiyya"
Haka suka kama tafiya izuwa titi domin suhau napep.
Suna tafiya suna hira.
Sadyce tace"baki tambayeni jiya karfe nawa nadawoba"
"Toni sady inaruwana dako karfe nawa kika dawo,tunda abinda kika daukarma rayuwarki ai saikije kitayi,amma waima natanbayeki mana"
"Inajinki"
"Baki gudun gida aganemaki,dannide nasan gida ba'asan kina wannan yawoce²n ba"

Sady:"ai abinda nakeso nafadamaki kenan,jiyafa karya nayi zani gidan anty nafisa,shine saurayina yazo yadaukeni,bai maidoniba sai bayan isha'i,inashiga gida natarar mama tadaga waya zata kira anty nafisa wai nataho hakanan,ke bakiji yadda gabana yafadiba".
"Hmm sady kenan,duk wani boye²nki wataran dole aganoki,bakiji masu magana nacewaba,rana dubu tabaro dayace takk tamai kayaba"

"Kafin lokacinma nayi aure"hannu sady tasa ajikka tafiddo kudu yan dubu² tanunama zuwairiyya,"kingani kudin danasamu jiya kawai"

Zaro ido zuwairiyya tayi tana mamakin uban kudin datagani kawar tata tafiddo.

TAWA KADDARARCE HAKAWhere stories live. Discover now