BAHAGON LAYI,BABI NA 1&2 DA 3&4

245 12 1
                                    

[7/23, 09:45] Hassana D'an Larabawa🥰: *TYPING*📲

🏘️ *BAHAGON LAYI* 🏘️

        (GIDAN KITSO)

*TARE DA ALK'ALAMIN* ✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR* 👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

      *DA KUMA* 👇

BAHAGON LAYI



*BABI NA D'AYA DA NA BIYU*


✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*


_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI,TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU K'ARA TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD (S A W)DA ALAYENSA DA SAHABBANSA*
        *MASOYA GANI NA DAWO DA WANI SABON LITTAFINA,DUK DA CEWAR GAJERE NE BA DOGO BA,AMMA INA FATAN SAK'ON YA KAI INDA NAKE SO HAR MA YA WUCE,KAR KU MANTA INA BUK'ATAR COMMENTS D'IN KU DOMIM YANA K'ARAMIN K'WARIN GWIWA*

   K'aramin Tsakar gidan   mata ne a zaune mabambanta,surutai da shewar su kawai ke tashi kamar su fasa gidan Dan hargowa,ga gyad'a marau marau da tub'us tub'us baje a gabansu sai b'arewa suke yi suna jefawa a bakunansu,Zagaye suke da Harira Me kitso wadda take kitse kan wata Yarinya da ba tafi shekara takwas zuwa tara ba.
Hirarsu ta katse a lokacin da suka ji yarinyar ta fasa kuka saboda azababben rank'washin da Harira ta zuba mata a tsakiyar kanta,duk suka maida hankalinsu kan Harirar da take kumfar baki tana yi wa yarinyar masifa tare da matse kanta a tsakanin cinyoyinta.

"Ke Dan Ubanki zaki tsaya na k'arasa miki kitson nan ko sai na k'ara zuba miki rank'washin da zaki ga k'wak'walwar kanki tana yarari?tunda kika zo nace miki ki bari nayi miki zane amma kika ce ke kwando(Doka) kike so,Dan haka tilas kisa kanki tsakanin cinyoyina in kina son kitsonki yayi kyau,ban da ni ma waye zai tab'a wannan kan da sunan kitso,aikin banza kai duk gunji da almajiran k'eya,billahillazi kika sake d'agowa ban gama ba idan na zuba miki dundu fes zan b'urma miki baya"
Ta k'ara matse kan yarinyar sosai tsakanin cinyoyinta tana ta bala'i da masifa,yayin da yarinyar ke kuka hawaye shab'e shab'e Dan azabar da take ji,ba kuma komai ke sata mutsu mutsu ba sai azabar wari da d'oyin da ya addabeta,da ta saka kanta kan cinyar harira sai wani masifaffen wari ya daki hancinta,ta rasa warin menene haka yake tasowa,ita dai ba zata ce warin tusa bane tunda ba taji k'ararta ba,haka nan ba zata ce warin kashi bane tunda Harirar babbace balle tace kashi tayi a zaune,gabad'aya warin ya dami hancinta har cikinta ya fara ciwo da kumburi saboda warin.

         Habiba ce ta hure gyad'ar da ta b'are a hannunta ta cilla bakinta ta taune,sannan ta kalli Harira tace.
"Gaskiya Harira ke azzaluma ce,haka kawai sai lodar yarinyar mutane kike yi Dan tazo kitso wajenki?kin matse mata fuska ta ya ya ba zata so d'agowa Dan ta shak'i iska ba?wallahi ina ganin k'ok'arin mutanen layin nan da unguwar nan da suke turo y'ay'ansu da sunan ki musu kitso,basu san azabar da kike ganawa y'ay'an bane,idan nice kika yiwa y'ay'ana haka ai kotu ce zata rabani dake,wannan rank'washin da kike mata idan tsautsayi ya gifta kika lotsa mata mad'iga fa?

BAHAGON LAYIWhere stories live. Discover now