BAHAGON LAY BABI NA 17&18 DA 19&20

102 7 0
                                    

[8/7, 11:05] Hassana D'an Larabawa🥰: *TYPING*📲

🏘️ *BAHAGON LAYI* 🏘️

        (MAGANIN MALLAKA)

*TARE DA ALK'ALAMIN*✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR*👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

         *DA KUMA*👇

BAHAGON LAYI

*BABI NA SHA BAKWAI DA NA SHA TAKWAS*

*WATTPAD:Hassana3333*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*


_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/



*GODIYA MARA YANKE WA GAREKU MASOYANA,HAK'IK'A DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA,MUSAMMAN GROUPS D'IN*👇

AISHA BAGUDO FANS
TABITAL PULAKU
ZAUREN JIKAR NASHE
JIDDA REAL FANS
TASKAR FATI TEEJAY
Y'AR MUTAN DIKKAWA NOVELS
WAYE SILAR LALACEWATA FANS
BAHAGON LAYI FANS

DA SAURAN GROUPS D'IN DA BAN AMBATA BA DUK INA SONKU SOSAI,INA KUMA GODIYA GA MARUBUTAN DA SUKE BIBIYAR WANNAN LITTAFI DOMIN KARANTAWA,HAK'IK'A INA JIN DAD'I SOSAI,ALLAH YA BAR ZUMUNCIN MU 🤝🌹🥰😘😍💃


Sai yamma lik'is mijinta ya kusa dawowa sannan suka yi shirin komawa gidajen su,kafin su tafi sai da suka fad'awa Hauwa yanayin tsarin zamantakewar da suke yi a tsakanin su,karb'a karb'a ne tamkar mulkin farar hula,kowacce akwai randa za a yini a gidanta a bararraje ayi girki da hira,hatta da cefane da Kansu suke zuwa basu da almajirai,saboda almajiran yanzu tak'adirai ne a cewar Habiba.

      Nan Hauwa Amarya tace.

"Nima na bada goyan baya akan hakan,domin na kan samu kaina cikin kewa idan Hubby ya fita,bai wani d'au Hutu Dan tayani zama ba,gashi zuwan da akewa amare ni ba a yi min ba,sai naji Gidan yayi min ba dad'i,amma yau idan ya dawo zan masa bayanin abin da kuka ce min Dan ya zama ina fita da saninsa"

Har sunje bakin k'ofa Saratu ta waiwayo a zabure ta dubi Hauwa tace.

"Amma ke Y'ar fari ce a gidanku ko?"

Hauwa ta girgiza kai tace.

"Ah ah me kika gani,ina da yayye da yawa ma,ko yanzu tare da yayata akayi bikinmu"

Saratu ta tab'e baki tace.

"Ganinki nayi kamar wata gab'uwa sak'andama,yo in ba gab'unta ba ta ya ya za ki ce zaki sanar da mijinki wannan maganar?d'azu fa naji kince D'an tarangahuma ne yana da zafi,to akul kar ki masa maganar in ba so kike ya nane miki ido d'aya ba ,ki zama irin uwar Mijina Iya me ido d'aya"

Suka k'yalk'yale da dariya,Hauwa ji take kamar ta bisu domin ba ta gaji da jin shaftarsu ba,Shafa'tu ce ta fara gaba ta na cewa.

"Ni fa Saratu sai da kika ambaci Uwar mijinki na tuna yau k'annen Kamilu za su zo,gashi yamma tayi k'ila sun gaji da jira sun ware ma"

Amarya Hauwa da k'yar ta koma bayan ta rakasu soro,suka yi sallama da Zahra'u akan gobe zata kawo mata maganin har gida.
     Suna fita suka hango k'annen kamilu su biyu a k'ofar Gidan Shafa'atu,d'aya siririya d'ayar kuma k'atuwa,me k'ibar ce fuskarta a had'e tasha kunu saboda sunfi awa uku tsaye suna jiran Shafa amma shiru duk da ta san da zuwansu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 08, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAHAGON LAYIWhere stories live. Discover now