BAHAGON LAYI BABI NA 5&6 DA 78

90 7 0
                                    

[7/25, 10:14] Hassana D'an Larabawa🥰: *TYPING*📲

🏘️ *BAHAGON LAYI* 🏘️

        (BABA DA DIDDIGA)

*TARE DA ALK'ALAMIN*✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR*👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

         *DA KUMA*👇

BAHAGON LAYI

*BABI NA BIYAR DA NA SHIDA*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*SADAUKARWA GA*👇

HUSSAINA D'AN LARABAWA😍,SISINA Y'AR UWA RABIN JIKINA🥰,BARI NA TUNO BAYA LOKACIN YARINTA😘(BABA DA DIDDIGA?)🤣😂😜


  Kamar yayi kuka saboda takaici,Sosai ya bugu har k'ugunsa sai da ya amsa,wai shi da gidansa shine me biyan kud'in haya amma bashi da katab'us,saboda tsabar bala'i da masifa matarsa ma bai isa ya sarrafata yadda yake so ba,ya rasa ina zai sa kansa da masifar Harira.

     Haka ya daddafa ya mik'e domin ya nemi gidan wanka ya gabatar da uzurinsa,Dan tabbas in yayi sake zai iya sakin kashin a wando saboda matsarsa da yayi,Wanda hakan abin kunya ne a gareshi.

Shi kam Salisu yana shiga gidansa yayi ta sakin tsaki yana harare harare,Saratu da ke zaune a tsakar gida da d'aurin k'irji ta juyo tana kallonsa,ganin yaja kujera Y'ar tsuguno ya zauna bai mata magana ba ita ma sai ta share shi,can taji sai sakin tsaki yake yi a jajjere,hakan yasa ta b'ata rai ta kalleshi tana danna masa Harara tace.

"Kayi a hankali dai Salisu,domin duk mutumin da ya cika tsaki to tsaka yake zama,haba! daga fitar ka sai ka dawo ka isheni da tsaki a gida,in wani abun ne ya b'ata maka rai ba sai kaji da lalurarka ba,haka kawai sai kazo ka tasani gaba ka addabeni da tsaki akan me?,Bari kaji na fito maka a mutum,Wallahi ni gabad'aya Salisu bana k'aunar zamanka a gida domin kana takuramin wallahi,kana Shiga rayuwata,kayi min wani shirim a gida ina son shan iska amma ka tare ko ina,wallahi daga fitarka ba kaji inda naga filin gurin ba,amma kana dawowa duk ka babbake ko ina,kai Allah ya rabamu da k'iba irin taka Salisu,Abu sai kace Sunduk'i"

Yayi wani irin murmushi na takaici, yayi mata banzan kallo sannan yace.

"Ai ke kin sani babu abin da zan fita na ci karo da shi ya b'atamin rai irin Akuyoyin k'awayenki,mata marasa kamun kai da nutsuwa,Lafiya k'alau na auroki a matsayinki na Y'ar gidan malamai Saratu,amma zuwanki layin nan kin had'u dasu kuna shashanci da tumasanci,kina Y'ar Malam amma kin k'i halin Malam,ga wata tsinanniyar d'abi'a da kika kwasa ta lek'e,Haka Shekaranjiya Najibu me shayi ya kawo min k'ararki,wai kullum in zai shige ta layin nan kina mak'ale jikin k'ofa da d'aurin k'irji kina lek'e,duk Wanda zai shige sai ya kalleki kin kalleshi,wallahi Saratu ina nan ina addu'a Allah yabi min hakkina na zubar min da mutunci da kike,ina son d'aukar mataki a kanki amma kunyar malam ta hanani yin hakan,amma ki tabbatar idan baki sauya hali ba ina dab da zartar da hukunci mummuna a gareki,maganar k'iba da kike yi to ai ni nagodewa Allah,tunda k'ibata ba ta sa na jibge har bana iya tafiya ba,wasu suna nan a jab'e ko yunk'urawa za su yi sai an d'aga su,sann...

BAHAGON LAYIWhere stories live. Discover now