BAHAGON LAYI BABI NA 9&10 DA 11&12

84 7 0
                                    

[7/27, 16:08] Hassana D'an Larabawa🥰: *TYPING*📲

🏘️ *BAHAGON LAYI* 🏘️

        (MACE ME LEK'E )

*TARE DA ALK'ALAMIN*✍️

HASSANA D'AN LARABAWA

*MARUBUCIYAR*👇

SANADIN HOTO
HASSANA DA HUSSAINA
CIN AMANAR RUHI

         *DA KUMA*👇
.
BAHAGON LAYI

*BABI NA TARA DA NA GOMA*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

🖊 *PEN WRITERS ASSOCIATION*🖊️

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*

_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

*K'ila daga yau ba zaku sake ganin posting ba sai bayan sallah fan's*🥰🥰🥰



Kamar Dodo haka fuskar Malam Arabi ta koma saboda k'ullun kunu da yayi masa kwalliya faca faca,yana ganin yayi wurgi da Habiba ya daddafa ya mik'e a razane ya d'iba da mugun gudu yayi tsakar gida, ya yarda bulalar a nan,jin gudunsa yasa shima Babalalo ya d'iba a guje suka yi k'ofar gida suna rige rigen fita,a zaton Babalalo ko Habiba biyo Malam Arabi tayi,a sukwane suka fito k'ofar gida suna sauke bahagon numfashi da ajiyar zuciya,sannan suka tsaya suka yi cirko cirko suna kallon juna.

Babalalo ya kalli fuskan Malam Arabi a ragowar farin watan da ya haske sararin samaniya,yaga yadda k'ullu ya b'ata masa fuska tamkar Wanda watan Ramadan ya shigo yayi shirin tafiya tashe,k'iris ya rage ya kwashe da dariya sai dai yayi ta maza ya waske da tambayar Malam Arabi cikin haki.

"Wai Malam biyo ka tayi ne naga ka fito da gudu?

Malam Arabi yaji kamar ya shak'e Babalalo Dan k'ufula,ya kuwa dank'ara masa muguwar Harara ya zarce da bashi amsa a fusace.

" Ban sani ba,nace maka ban sani ba,banda wulak'anci daman ka san matarka mahaukaciyace kuma Y'ar iska ce ka kawo ni da sunan cire mata aljanu,yanzu ba Dan Allah ya kiyaye nayi ta maza ba Cibiyata fa taso cire min,kai wannan mata anyi tsinanniya,billahil azimu na zata kaca aka watsa min a Cibiyar,wai Ashe hak'oran ta ta kafta min,in banda Y'ar iska ce tana matar aure amma ta cafki Cibiyar k'aton mutum irina?Haka kawai da gemuna na sunnah ta keta min haddi?a yanzu ji nake Cibiyar na rawa tamkar zata fad'o k'asa,Allah dai ya tsareni kar in je ta zuba min virus da dafin bakinta"

Babalalo Abu biyu ya had'e masa,ga takaici ga shi yana son yayi dariya,tilas ya k'unshe dariyar ya dinga bawa Malam Arabi hak'uri,har da cewa.

"Malam mu koma cikin gidan na baka kaya ka sauya,kaga na jikinka duk sun b'aci da mark'aden gero, kar kaje gida a ganka haka babu dad'i"

    Kallon da Malam Arabi yayi masa ko bai tanka ba ya isheshi amsa,amma Duk da hakan saida ya tanka cikin fusata da b'acin rai.

"Babalalo ka san tsirara?to gara na tafi tsirara akan na sake shiga gidanka domin annobar da take ciki,matarka kuwa kada Allah ya k'ara had'a fuskata da tata ko a hanya,domin naga bala'i da masifa a tare da ita yau,haka kurum daga zuwa taimako ta had'ani da jinyar Cibiya,Wallahi Allah ya isa ban yafe ba,Y'ar banza me hak'ora irin na karya"

Yana gama magana ya saita hanya yayi gaba zugudun zugudun kamar zai kifa,da yaga malum malum d'insa na hard'eshi ma tsayawa yayi ya cire ya soketa a hammatarsa,sannan yayi gaba yana ta masifa yana Jan Allah ya isa,Dan ji yaket yi kamar Cibiyarsa ta tashi daga aiki.

BAHAGON LAYIWhere stories live. Discover now