GARIN KALLON RUWA PAGE 1

261 15 3
                                    

💦 *GARIN KALLON*💦
            *RUWA*💧

          

                ✍️
        *AISHA GALADIMA*

_BISMILLAHI RAHAMANIRRAHIM_


 
_Masoya 'yan uwa da Abokan Arziki nagode da Addu'o'in ku na Alkahiri Allah ya bar zumunci_
*

   

*Page 1*


_____________________________
 

  FEDERAL COLLEGE OF EDUCATION (T) GUSAU

A yau garin na gusau wata irin Rana ake kwalla wa me zafin gaske ,Wanda mutane da dama duk suna cikin inuwa sun labe , a can gefen biology department Naga wasu 'yan Mata su ukku zaune , dayar naji Tana cewa Wai Billy me yasa wani lokacin kike da taurain Kai ,miye a ciki Dan kinje kinba lecturer Nan hakuri,tunda kin San ke ce da laifi da kika zo latti,bayan kinsan ka'idar sa na duk ya shiga class ba Wanda ya Isa ya sake shiga

Shiru wadda ake ma maganar ta yi, dayar ce ta ce kema Fatima kina da mun kanki da yawa ,kin San duk ba zuwa zata yi ba in dai Billy ce

Dago Kai Naga tayi ta kalle su tayi murmushi ,kafin tace "kuyi hakuri kun San fa ni walakanci ne bana so shiyasa ma bazan je ya disgani a banza ba ehhe

Fatima ce tace"to miye a ciki Dan ya disgaki din ,ba nema kike ba ,yanzu fa kusan so ukku kina rasa lecture din sa,Kuma kinsan attendance Yana da muhimmanci sosai a wurin sa

Karar wayar ta ne ya jawo hankalinsu duk akan wayar
Bestie Naga ansa ,daga wayar tayi ta Kara a kunnenta  "Assalamu Alaikum"
Tace ,daga dayan bangaren banji me aka ce Mata ba tace   "Ok mu Hadu love garden"

Ta sauke wayar ta na kallon kawayen nata tace" bestie ne ya kirani zanje ya koya min Abunda Akayi ba da Ni ba

Fatima tace "to se kin dawo ,Khadija handout ta ci gaba da dibawa

Ta shi tayi ta dauki side bag dinta ta  fara tafiya ,tafe take har ta wuce library se Naga ta iso wani fili da aka kawata da wasu kujerin zama ga bishiyoyi a wurin iri iri sun ma wurin lib Wanda yasa wurin ya zama me inuwa ,atakai ce dai wurin ya ci sunan sa love garden

Wayar ta Naga ta dauka ta lalubo number bestie ta sake Kira bayan wasu dakiku ya daga cewa tayi "gani a love garden din fa"

Ban san me yace Mata ba Naga ta juyo bayanta Tana kallon wani kyakyawan saurayi murmushi ta tako ta karaso in da yake tsaye  Tana zuwa zama kawai tayi ,shima zama yayi kasancewar kujerin wurin suna da Fadi

Kallonta yayi yace "bestie ya lectures ?"

Cewa tayi "Hmm Alhamdulillah Ammah yau ma ban samu lecture din ba fa"

Da mamaki yake kallonta ba ya ce "kamarya ,Baki zo da wuri ba ko ?"

"Eh Kuma kasan mugunnan ne fa muke da,ai baze barni na shiga ba"
Tace Masa

"Was kenan?"

"Aliyu Mana" ta kare maganar Tana turo Baki

Cewa yayi "habah bestie kema ki dinga kiyayewa Mana,ka'idar sa ke Nan shiyasa ,sannan ko mu da muke Degree haka ya ke muna,Kuma mutumin nada saukin Kai sosai fa"

Hade Rai tayi kafin tace "Kai ke ganin Yana da kirki Ammah a wurina ba yada wani mutunci ,Kullum cikin Shan toka kamar Wanda aka aikowa da sakon mutuwa,Ni wanna be dame Ni bama ,Ammah abunda na sani shine duk Wanda ya taka Ni ,Ni ma se na taka sa ,komai girman mutum ko"

Karaf a kunnen malam Aliyu da ya zo ze wuce ta cikin love garden din

Da sauri Bestie din nata ya juyo Yana kallon ta Yana zaro ido ,Yana Kuma Kara juyawa Yana kallon malam Aliyu da ya wuce

Juyowa yayi yace "Allah yasa malam Aliyu be ji me Kika ce ba"

"Ai so Nike ma yaji wallahi ,mutum kulum cikin mugunta "

Shiru yayi kafin yace "Kinga mu bar wannan maganar ,dauko littafin naki mu gani"

Jakarta ta jawo ta bude  ta fito da wani jotting book dinta da Kuma littafin fatimada ta ara,Nan ya shiga koyar da ita cikin kwarewa ,Tana ko ta fahimtar abunda yake koya Mata kasancewar Billy Akwai kokari

Malam Aliyu kuwa yaji maganar ta, ta karshe da take cewa "duk Wanda ya taka ta se ta taka shi"

Yana tafe yana mamakin Jin Kai irin na yarinyar, ya kula kamar Tana Jin kanta da yawa ,sannan wannan wanene da Kullum se ya gansu tare,oho wata zuciyar ta ce masa

Tsaki yayi ma ,ganin  Yana tunanin abunda be kama ce sa ba gaba daya

"Yawwa affan nagode sosai,kaga kuwa ka koya min yadda maths dinnan yake,nagode sosai fa ,tun farkon haduwa ta da Kai Affan na San Alkhairi ne,da ace Babu Kai a Fcet ban San ya Zan yi ba" ta kare maganar ta na murmushi

Tunda ta fara magana yake kallonta ,a cikin zuciyar sa kuwa ba karamin dadi yake ji ba,kafin yace " ai ke kawata ce Billy ,aboki kuwa ze iya ma Abokin sa koma menene"

"Duk da haka samun mutumin kirki irin ka ze yi wuya fa"
Tace Tana dariya

"Ki bar fasa min Kai da yawa fa"
Ya fada shima Yana murmushi

"Ai ya fashe ma In Dan yabonka ne yanzu na fara "
Billy tace

"Ok muje na rakaki"

Mikewa tayi ta dauki littafanta ta mayar a jaka suka jero suna tafe suna firar su har ya kawo ta wurin su Fatima

Gaisawa yayi da su Fatima ,sannan ya musu sallama ya tafi

Fatima ce ta tashi tace"to ki wuce muje kun San muna da lecture yanzu fa ,mikewa khadija tayi dama ita Billy a tsaye take ,cewa tayi

"A'ina za muyi GSE din?"

"Science theater"

Khadija tace

Jerawa sukayi gwanin sha'awa suka nufi hall din da zasu yi lecture din

Sun kusa Awa daya,sannan suka fito ,hostel suka nufa saboda duk a gajiye suke

_______________________________

Dattijai ne maza guda biyu akan wata tabarmar kaba ,se dai daya yafi daya tsufa ,Wanda yafi tsufan ne naji yana cewa "sambo Wai yaushe zaka aurar da 'yarka ne ,ko har yanzu bata gama karatun bokon bane?"

Cikin girmamawa dayan mutumin yace"Baba An kusa Mata insha'Allah da ta gama makarantar da take za'ayi"

" Ba se ta gama ba sambo da ta samu miji ka aurar da ita Mana, da a kauyen Nan take ai da yanzu harda 'ya'yanta ma ga su huraira Nan warinta har da 'ya 'ya ukku ,kar ka biye wata boko da ta samu miji a aurar da ita kana jina ko
Cewar tsohon

"insha'Allah baba duk yadda kace haka za'ayi

"To yayi Allah ya maka Albarka,yanzu  ka tashi kar dare ya ma ka kama hanyar
Gusau"

Sallama ya ma dattijon ya tashi Naga ya nufi wata mota ya shiga.........✍️

Aysha galadima ce

GARIN KALLON RUWAWhere stories live. Discover now